Ruwa: wani tataccen sinadari ne wanda yake da matukar muhimmanci ga halittun Duniya baki daya.
Kama daga kwari, tsuntsaye, halittun ruwa da na doron kasa. A turance ana kiransa da water, Hakika Ruwa ya kasance shine ginshikin rayuwar halittun duniya baki daya, ruwa shine tubalin ginin kwayar duk wata halitta dake doron duniya.
Ruwa | |
---|---|
oxide (en) da dihydrogen chalcogenide (en) | |
Kayan haɗi | iskar shaƙa da hydrogen (en) |
Said to be the same as (en) | water (en) |
Ruwa ya Kuma kasance yana tabbatuwa ko saukowa zuwa doron duniya a bisa kudirar Allah mahalicci. Da farko dai asalin samuwar ruwa daga cikin giza-gizai yake taruwa, sannu a hankali har giza-gizan su cika da tekun ruwa wadda daga nan iska zata rika tura girgijen zuwa inda ruwan zai sauka, shi yasa duk lokacinda hadari ya taso zakaji iska tana kadawa da karfi cikin kankanin lokaci sai kaji an goce da ruwa.
Bayan ruwa ya sauka nan take kasa zata tsose shi, wasu kuma su kwarara zuwa teku daga nan kuma sai kasa ta kumbura, saboda haka duk wata kwayar tsiro itama sai ta kumbura ta rube sakamakon ruwan da ta tsotsa cikin ikon Allah sai kaga an wayi gari tsirrai iri-iri sun cika ko'ina a sararin duniya abin gwanin ban sha'awa. Hakika ruwa shine ginshikin duk wata halitta mai rai a doron kasa kowacce halitta tana bukatar ruwa, musamman Dan'adam yana amfanuwa da ruwa ta hanyoyi da dama wanda bazai yiwu a iya kididdige amfanin da ruwa keyiwa dan'adam ba, tsarki ya tabbata ga Allah mahaliccin ruwa domin amfanin bayinsa.
This article uses material from the Wikipedia Hausa / هَوُسَ article Ruwa, which is released under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 3.0 license ("CC BY-SA 3.0"); additional terms may apply (view authors). An samar da dukkan muƙaloli a ƙarƙashin lasisin Creative Commons Attribution/Share-Alike; tana yiwuwa wasu ƙa'idoji su yi tasiri. Ku duba Ka'idojin Amfani na Gidauniyar Wiki domin ƙarin bayani. Images, videos and audio are available under their respective licenses.
®Wikipedia is a registered trademark of the Wiki Foundation, Inc. Wiki Hausa / هَوُسَ (DUHOCTRUNGQUOC.VN) is an independent company and has no affiliation with Wiki Foundation.