Nahiya

Nahiya na nufin manya-manyan da'irar shimfiɗaɗɗun ƙasashe da ake da su a duniya.

Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.

Akan ƙididdige su ne dangane da yarjejeniya ba wai don wasu ƙa'idoji na musamman ba, akawai yankuna na ƙasa guda bakwai wanda ake ɗauka a matsayin nahiyoyin duniya. Wanda aka jera su daga mafi girmansu zuwa mafi ƙanƙantsu, waɗannan nahiyoyi bakwai sune: Asiya, Afirka, Amurka ta Arewa, Amurka ta Kudu, Antatika, Turai, Ostiraliya. Wasu 'yan bambance-bambance na iya haɗe wadannan nahiyoyi misali, Amurka, Eurasia, ko kuma Afro-Eurasia akan dauke su a wasu lokutan a matsayin nahiya ɗaya wadanda ka iya rage yawan nahiyoyin zuwa guda huɗu.

Nahiyanahiya
Nahiya
Bayanai
Ƙaramin ɓangare na landmass (en) Fassara da natural geographic object (en) Fassara
Bangare na Earth's crust (en) Fassara da Duniya
Ƙasantuwa a yanayin ƙasa continental crust (en) Fassara
Shafin yanar gizo whosonfirst.org…
Hannun riga da ocean (en) Fassara

Amma abin da aka fi haƙƙaƙewa akai shi ne, waɗannan nahiyoyi guda Bakwai ne. Kuma sun haɗar da Afirka da Antarctica da Asiya da Austaraliya da Turai da kudancin Amirka da kuma Arewacin Amirka. Wannan a yadda aka karantar da ɗalibai kenan a yankin nahiyar Amirka baki ɗaya. Ana daukan Zealandia, wani katafaren yanki na duniya a matsayin nahiya mai zaman kanta.

Amma kuma a yankin nahiyar Turai da kuma sauran sassan duniya, mafi yawan ɗaliban yankunan ana karantar da su cewar, nahiyoyi Shida rak ake da su a duniyar nan. Ma'ana a waɗannan yankuna ana duban Kudancin Amirka da kuma Arewacin Amirka a matsayin nahiya guda ɗaya ta Amirka. Anan lissafin nahiyoyi shidan kenan ya haɗar da Afirka da Amirka da Antarctica da Asiya da Australiya da kuma Turai.

To sai dai a halin da ake ciki kuma, mafiya yawan masana ta fuskar kimiyya na duban waɗannan nahiyoyi Shida da cewar nahiyar Turai da ta Asiya a dunƙule suke wuri ɗaya a matsayin nahiya guda, don haka ne ma suke kiran nahiyar da suna Eurasiya, sai kuma Afirka da Antarctica da Austaraliya da Kudancin Amirka da kuma Arewacin Amirka.

Masana ilimin taswirar duniya, su kuma a halin yanzu sun kasafta duniyar nan zuwa yankuna takwas domin samun sauƙin fahimta. Yanki na farko dai shi ne na Asiya, wanda ya ƙunshi Gabas ta Tsakiya da Arewacin Afirka. Sai kuma Turai da Arewacin Amirka. Akwai kuma Tsakiyar Amirka da yankin Carribbean, kana kuma Kudancin Amirka da Afirka da Austaraliya da kuma Yankin Teku, wato Oceania kenan.

Yawan jama'a

Continents of the world
Nahiya Faɗin ƙasa Jumullar Mutane
km² mi²
Asiya 44,579,000 17,212,000 4,298,723,000
Afrika 30,221,532 11,668,599 1,110,635,000
Amurka ta Arewa 24,709,000 9,540,000 565,265,000
Amurka ta Kudu 17,840,000 6,890,000 406,740,000
Antatika 14,000,000 5,400,000 4,490 (Estimated)
Turai 10,180,000 3,930,000 742,452,000
Osheniya 8,525,989 3,291,903 38,304,000
Duniya Around 7.7 billion

(As of 2019)

Nahiya mafi yawan mutane itace Asiya, sai Afrika mai biye mata baya. Ta uku itace Turai. Ta huɗu itace Amurka ta Arewa sai ta biyar kuma [[Amurka ta Kudu]].

Manazarta

Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.

Tags:

AfirkaAfro-EurasiaAmurkaAmurka ta ArewaAmurka ta KuduAntatikaAsiyaOstiraliya (nahiya)Turai

🔥 Trending searches on Wiki Hausa / هَوُسَ:

Waƙoƙi CossackTsuntsuLisa-Marié kwariUnilever Nigeria PlcAl'adar bikin cika-cikiIspaniyaƊan wasaJega, NigeriaMaleshiyaGoroKaabaZainab AbdullahiJyoti ChettyMusulunci a NajeriyaLynette BurgerHauwa WarakaMikiyaSurahSarkin OmanJodanAjingiSallolin NafilaIbrahimAbdullahi Umar GandujeYanar gizoTumfafiyaSadiya Umar FarouqKhalid Al AmeriAbubakar Adam IbrahimGadar kogin NigerMuhammad AliJerin SahabbaiAshiru NagomaYahudanciJahar TarabaSadiq Sani SadiqAmurkaKisan ƙare dangi na RwandanRimiCiwon nonoBernette BeyersJerin yawan habakar mutane a jahohin NajeriyaGafiyaFati NijarJerin Sunayen Gwanonin Jihar kebbiJerin sunayen Allah a MusulunciIbrahim NiassFarisMaymunah bint al-HarithAlhaji Ahmad AliyuSani AbachaTanya AguiñigaUsman Dan FodiyoZumunciCiwon Kwayoyin HalittaRFI HausaAdabin HausaAbinciShah Rukh KhanAfirka ta KuduFilmAlhassan Saeed Adam JosHungariyaTarihin HausawaRimin GadoElvira WoodDaular RumawaBornoTarihin Ƙasar IndiyaFuruciCristiano RonaldoMa'anar AureJerin Ƙauyuka a Jihar KatsinaUkraniya🡆 More