Ka'aba (Larabci ٱلْـكَـعْـبَـة Ka'abah) ana kuma kiran ta da al-Kaʿbah al-Musharrafah (Larabci ٱلْـكَـعْـبَـة الْـمُـشَـرًّفَـة Daki mai tsarki), wani ginannen daki ne a birnin Makka na kasar Saudiyya mai matukar tsarki a tsakanin Musulmai.
(ٱلْـمَـسْـجِـد الْـحَـرَام Al-Masjid Al-Ḥarām, Masallacin Harami), Har ila yau kuma Musulmai kan kira shi da (بَـيْـت ٱلله Dakin Allah). Duk inda suke a duniya Musulmai ana bukatar su da su fuskanci bangaren wannan dakin lokacin gabatar da Sallah (صَـلَاة Ṣalât, Bautar Allah a Musulunce). Dakin kuma shine ake kira da (قِـبْـلَـة qiblah, mafuskanta) wato dai mafuskantar ta musulmai domin gabatar da Sallah.
Kaaba | |
---|---|
ٱلْكَعْبَة ٱلْكَعْبَة ٱلْمُشَرَّفَة | |
Wuri | |
Ƴantacciyar ƙasa | Saudi Arebiya |
Province of Saudi Arabia (en) | yankin Makka |
Tourist attraction (en) | Makkah |
Coordinates | 21°25′21″N 39°49′34″E / 21.4225°N 39.82617°E |
History and use | |
Ɗawafi | |
| |
Aikin Hajji | |
| |
Umrah | |
Karatun Gine-gine | |
Tsawo | 12.95 m |
Tsawo | 11.68 meters |
Yawan fili | 119 m² |
|
Daya daga cikin shika shikan Musulunci biyar shine aikin Hajji حَـجّ, a dakin na Ka'aba ne matattarar mahajjatan,duniya kuma kowanne Musulmi yana da fatan zuwa dakin koda sau daya ne a rayuwar sa domin dawafi (طَـوَاف tawaf, kewaya dakin sau bakwai da niyyar bauta ma Allah). Hakanan ma bayan aikin Hajji haka dai musulman na yin dawafin a fakin yayin zuwansu Umara (عُـمْـرَة Umrah). Miliyoyin mutane ne ke ziyartar dakin domin tsarkake Allah, mutane daga wajen kasar Saudiyya 1,379,531 ne suka halarci dakin yayin aikin hajji na 2013, a shekarar 2014 ma Saudiyya ta sanar da adadin mahajjata daga wajen kasar ta 1,389,053 wadan da suka halarci hajjin shekarar yayin da yan kasar ta kuma kimanin mutane 63,375 ne suka samu halar ta.
Asalin kalma da canzawarta
Mahanga ta addinin musulunci
Dawafi
matsayin alkibla
This article uses material from the Wikipedia Hausa / هَوُسَ article Kaaba, which is released under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 3.0 license ("CC BY-SA 3.0"); additional terms may apply (view authors). An samar da dukkan muƙaloli a ƙarƙashin lasisin Creative Commons Attribution/Share-Alike; tana yiwuwa wasu ƙa'idoji su yi tasiri. Ku duba Ka'idojin Amfani na Gidauniyar Wiki domin ƙarin bayani. Images, videos and audio are available under their respective licenses.
®Wikipedia is a registered trademark of the Wiki Foundation, Inc. Wiki Hausa / هَوُسَ (DUHOCTRUNGQUOC.VN) is an independent company and has no affiliation with Wiki Foundation.