Abdullahi Umar Ganduje: Ɗan Siyasa a Nigeria

Abdullahi Umar Ganduje An haifeshi a ƙauyen Ganduje da ke ƙaramar hukumar Dawakin Tofa jihar Kano Najeriya, a shekarar alif ɗari tara da arba'in da tara(1949).

Abdullahi Umar Ganduje: Farkon rayuwa da ilimi, Siyasa, Badakalar cin hanci Abdullahi Umar Ganduje
Abdullahi Umar Ganduje: Farkon rayuwa da ilimi, Siyasa, Badakalar cin hanci
gwamnan jihar Kano

Mayu 2015 - 29 Mayu 2023
Rabiu Kwankwaso
Rayuwa
Cikakken suna Abdullahi Umar Ganduje
Haihuwa Dawakin Tofa, 25 Disamba 1949 (74 shekaru)
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Hausa
Ƴan uwa
Abokiyar zama Hafsat Ganduje
Karatu
Makaranta Jami'ar Ahmadu Bello
Government College, Birnin Kudu
Jami'ar Ibadan
Jami'ar Bayero
Dawakin Tofa
Harsuna Turanci
Hausa
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa Jam'iyyar National Party of Nigeria

Farkon rayuwa da ilimi

An haifeshi a ƙauyen Ganduje a shekara ta alif ɗari tara da arba'in da tara (1949) miladiyya Isa dan Maraya.

Ya fara karatun Qur'ani da Islamiyya a ƙauyensa inda ya samu ilimin addini. Daga nan kuma ya shiga makarantar firamare ta Dawakin Tofa daga shekarar 1956 zuwa shekarar 1963. Ganduje ya fara makarantar sakandaren Birnin Kudu daga shekarar alif ɗari tara da sittin da huɗu, 1964, kuma ya kammala a shekarar alif ɗari tara da sittin da takwas, 1968. Bayan nan Ganduje ya shiga makarantar horar da malamai da ke Kano, tsakanin shekara ta 1969 zuwa shekarar 1972 inda ya shiga Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a jahar Kaduna Ya kammala karatun jami'a a fannin ilimi cikin shekarar ta 1975. A shekarar 1979 ne kuma ya kammala digirinsa na biyu a Jami'ar Bayero dake Kano. Sannan ya ƙara komawa Jami'ar Ahmadu Bello Zariya daga shekarar 1984 zuwa shekara ta 1985 domin karantar ilimin tafiyar da gwamnati. A shekarar 1993 ne ya samu digirin digir-gir daga Jami'ar Ibadan.

Siyasa

Ganduje ya shiga jam'iyyar NPN a jamhuriyya ta biyu sannan ya zama mataimakin sakatare na jihar Kano daga shekara ta 1979 zuwa shekarar 1980. Ya tsaya takarar wakiltar Kano a zauren majalisar wakilai a shekarar 1979 a jam'iyyar NPN amma bai yi nasara a zaben ba. A shekarar 1998 ya kuma shiga jam'iyyar People Democratic Party (PDP) inda ya nemi jam'iyyar ta tsayar da shi takarar gwamna, amma bai yi nasara ba bayan da PDP ta tsayar da Rabi'u Musa Kwankwaso.

Mataimakin Gwamna

An zaɓi Ganduje a matsayin mataimakin Gwamna Rabi'u Musa Kwankwaso tsakanin shekarar 1999 zuwa 2003. Baya ga haka, an naɗa shi a matsayin kwamishinan ƙananan hukumomi. Daga shekarar 2003 zuwa 2007, ya riƙe mukamin mai bai wa ministan tsaro shawara na Najeriya, wato Rabi'u Kwankwaso, An zaɓi Ganduje a matsayin shugaban kwalejin fasaha a Ado Ekiti a 2008 daga nan kuma aka naɗa shi a matsayin babban sakataren Hukumar Kula da Tafkin Chadi da ke Ndjamena. Ya kuma kasance daga cikin waɗanda suka halarci taron yi wa tsarin siyasa a Najeriya garambawul a shekarar 2006. Kwankwaso da Ganduje sun kuma yi rashin nasara a zaɓen da suka nemi ta-zarce inda Malam Ibrahim Shekarau ya samu nasara.

An sake zabar Kwankwaso da Ganduje ranar 27 ga watan Afrilun 2011 inda aka rantsar da su ranar 29 ga Mayun shekarar 2011 domin ƙarasa zangon mulkinsu na biyu.

Gwamnan Jihar Kano

A shekarar 2014, an zaɓe shi a matsayin ɗan takarar gwamnan jihar Kano na jam’iyyar All Progressives Congress (APC). Ya ci gaba da kayar da ɗan takarar jam’iyyar PDP Malam Salihu Takai da ƙuri’u 1,546,434 yayin da Takai ya samu ƙuri’u 509,726 a zaɓen gwamna na 2015. A ranar 29 ga watan Mayun 2015 ne aka rantsar da shi a matsayin gwamnan jihar Kano, inda ya maye gurbin mai ba shi shawara ta fuskar siyasa Rabiu Musa Kwankwaso. A wa’adinsa na farko, Ganduje ya yi kaca-kaca da Kwankwaso, wanda ya zarge shi da ubangida . Haka kuma wa’adinsa ya kasance da taho-mu-gama da Sarki Muhammadu Sanusi II, wanda ya yi bincike kan rashin kudi. A shekarar 2019, ya sake lashe zaɓe karo na biyu, inda ya kayar da surukin Kwankwaso, Abba Kabir Yusuf, a zaɓen da aka yi mai cike da kura-kurai a zaɓen.

A shekarar 2019, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya sanya hannu kan dokar kafa sabbin masarautu huɗu. Wannan mataki da ba'a taɓa ganin irinsa ba ya sa an rage masarautun gargajiya na Sarki Muhammadu Sanusi II a matsayin sarki. A bisa doka, sarkin Kano zai jagoranci kananan hukumomi 10 ne kawai daga cikin 44 da ake da su a jihar, yayin da a baya masarautar ta kasance dukkanin kananan hukumomin jihar Kano 44. A watan Maris din shekarar 2020 ne dai majalisar dokokin jihar ta ƙaddamar da wani sabon bincike a kan Sanusi bisa saɓa al’adar gargajiya, wanda hakan ya biyo bayan hukuncin da wata babbar kotu ta yanke na hana binciken cin hanci da rashawa da ake yi wa Sanusi. A ranar 9 ga Maris, 2020, Ganduje ya tsige Sarki Sanusi, ya kuma kore shi daga kan mulki, bisa zarginsa da rashin bin doka da oda daga ofishin gwamna.

Badakalar cin hanci

Ganduje na fuskantar tuhuma daga al'umma daban-daban a kan wani bidiyo da wani ɗan jaridar yanar gizo, wato Jafar Jafar ya wallafa da hadin gwiwar gidan jaridar sa ta 'Daily Nigerian' ta fitar, inda aka ga Gandujen na karɓar daloli daga hannun wani ɗan kwangila yana tura su aljihun babban rigarsa, ɗan kwangilan na faɗi masa cewar kaga haka yafi rufin asiri. Amma gwamnati ta yi mirsisi ba tare da tace komai ba akan hakan, sai majalisar jahar ta nemi shugaban jaridar Ja'afar Ja'afar da ya gurfana a gabanta dan tabbatar da sahihancin bidiyon daya fitar, daga nan sukai watsi da batun, kuma da akwai wani lauya Mai zaman kansa wato Audu Bulama Bukarti wanda a lokacin da abun ya faru Yana ƙasar Ingila wanda ya faɗa cewa ya tambayi mukaddashin hukumar EFCC wato Ibrahim Magu Kuma ya tabbatar mai da wannan bidiyon na gaskiya ne.

Manazarta

Tags:

Abdullahi Umar Ganduje Farkon rayuwa da ilimiAbdullahi Umar Ganduje SiyasaAbdullahi Umar Ganduje Badakalar cin hanciAbdullahi Umar Ganduje ManazartaAbdullahi Umar GandujeDawakin TofaJihar KanoNajeriya

🔥 Trending searches on Wiki Hausa / هَوُسَ:

Iganmode Grammar SchoolNasir Ahmad el-RufaiZakiEnisa NikajKalmar TheGumelMulkin Farar HulaWikidataTarihin AmurkaYarukan AfrikaKubra DakoBilkisuBornoYusuf Maitama SuleRimin GadoAbu HurairahLafiyaBorisShanonoGobirMa'anar AureBasirAl-BakaraSaudi ArebiyaSankaran NonoKachiyaIstiharaRahama SadauSallar NafilaTumfafiyaJimaRabi'u RikadawaNaziru M AhmadMohammed Badaru AbubakarSiyasaAnnabi IsahNijarTanzaniyaAdamShams al-Ma'arifSam DarwishMaruruBuba GaladimaCiwon Daji na Kai da WuyaZuciyaHaƙƙin Mata Saddam Hussein's IraqUmar Ibn Al-KhattabIvory CoastSani Musa DanjaJerusalemJerin SahabbaiBello TurjiGuguwaJirgin RuwaFuruciMarsJerin ƙauyuka a jihar YobeKanyaFati WashaBoni HarunaMalam InuwaGoroHadiza MuhammadBudurciSadarwaSudanHarsunan NajeriyaMadinahƘarama antaGidaDawakin TofaAhmad Ali nuhu🡆 More