Abba Kabir Yusuf: Ɗan siyasar Najeriya kuma zaɓaɓɓen gwamnan jihar Kano

Abba Kabir Yusuf wanda aka fi sani da (Abba gida-gida) ɗan siyasa ne, kuma gwamnan Jihar kano karkashin jam'iyar New Nigeria People's Party (NNPP).

Abba Kabir Yusuf: Haihuwa da Nasaba, Karatun sa, Siyasa Abba Kabir Yusuf
Abba Kabir Yusuf: Haihuwa da Nasaba, Karatun sa, Siyasa
gwamnan jihar Kano

Rayuwa
Haihuwa Gaya, 5 ga Janairu, 1963 (61 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Harsuna Turanci
Hausa
Larabci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Addini Musulunci

Haihuwa da Nasaba

An haife shi a Jihar Kano, Abba dan Muhammadu Kabir dan dan makwayon Kano Yusuf dan Muhammad Bashir dan Galadiman Kano Yusuf ɗan Sarkin Kano Abdullahi Maje Karofi, dan Sarkin Kano Ibrahim Dabo dan kabilar Sullubawa ne na kabilar Genawa ta Fulani, a ɓangaren uwa kuma yana da alaƙa da Walin Zazzau Sheikh Umarul Wali dan Galadiman Zazzau Malam Ahmadu, kakarsa Zainab diyar Malam Saidu Limamin Huggalawa daga gidan Limamin Huggalawa ne a garin Bichi, kakarsa Khadijat Naja'atu tana da alaqa da Gwani Mukhtar wanda shi ne jagoran Jihadin Fulani a Kanem- Daular Borno.

Karatun sa

Abba Kabir yayi karatun Primary a Makarantar Sumaila Primary School, ya kammala a Shekara ta 1969-1975. sannan kuma Yayi karatun Sakandire a makarantar Lautai Secondary School Gumel GCE 0/level- a shekara ta 1975-1980. bayan nan ya halarci Federal Polytechnic Yola Jihar Adamawa inda ya sami National diploma ta ƙasa a ɓangaren kimiya da fasaha a fanin injiniya wato(Engineering) A shekara ta 1982-1985, a Kaduna Polytechnic, yayi HND a fannin injiniya a shekara ta 1987-1989 sai kuma ya halarci Jami'ar BUK Kano, PGDM a shekara ta 1994-1995. har wayau ya samu shaidar Masters a bangaren karatun harkokin kasuwanci (MBA) a shekara ta 1997-1999 a Bayero University Kano.

Siyasa

Ya riƙe muƙamin Kwamishinan aiyuka a zamanin mulkin tsohon gwamnan jahar kano Engr.Dr. Rabiu Musa Kwankwaso, daga shekara ta 2011 Zuwa shekara ta 2015 sannan yayi takarar gwamnan kano a karkashin jam'iyyar PDP a shekara ta 2019. Sannan Kuma ya sake yin takarar Gwamna a jam'iyyar NNPP a jihar Kano a shekara ta 2023. Abba yayi nasarar zama Gwamnan jihar Kano a zaɓen gwamnan Kano na shekara ta 2023 inda kuma yayi nasara a kan babban abokin hamayyar sa na Jam'iyyar APC Nasiru Yusuf Gawuna. An rantsar da Abba kabir yusif a matsayin gomnan jihar kano a ranar Litinin ashirin da tara 29 ga watan Mayu na shekara ta dubu biyu da ashirin da uku 2023.

Manazarta

Tags:

Abba Kabir Yusuf Haihuwa da NasabaAbba Kabir Yusuf Karatun saAbba Kabir Yusuf SiyasaAbba Kabir Yusuf ManazartaAbba Kabir YusufKanoNew Nigeria People's Party

🔥 Trending searches on Wiki Hausa / هَوُسَ:

Abdullahi AmdazAmina GarbaKarin maganaTsarin DarasiLokaciJanabaMurtala MohammedBabban Birnin Tarayya, NajeriyaAliyu Ibn Abi ɗalibAbubakar Tafawa BalewaAbincin HausawaMuhammad gibrimaSallar Matafiyi (Qasaru)Guidan SoriMohammed Umar BagoTuranciCarles PuigdemontHassan Sarkin DogaraiTarihin Kasar SinƘarama antaShuwa ArabUsman Ibn AffanTunisiyaArewacin NajeriyaAbdu BodaAyabaLandanRagoMusaJerin Sarakunan KanoJerin gwamnonin jihohin NijeriyaKankanaAlgajabbaDuniyar MusulunciNijar (ƙasa)Eniola AjaoKhalid Al AmeriKaruwanci a NajeriyaMusulunci a NajeriyaLarry SangerAccraƊan AdamSallolin NafilaArewa (Najeriya)OmanAnnabi IbrahimTunaniTuraiMasarautar DauraKadangareFarida JalalMasallacin ƘudusJerin shugabannin ƙasar NijarSalatul FatihAisha Sani MaikudiZazzauJennifer VelDokar NajeriyaAminu Waziri TambuwalShehu Hassan KanoIbn TaymiyyahƳancin mallakar hannun jariZainab AbdullahiMasarautar KatsinaMikiyaMike Flynn (kwallon kwando)Ibrahim ZakzakyJerin ƙasashen Afirka🡆 More