Hafsat Ganduje

Hajiya Hafsat Abdullahi Ganduje (wadda aka fi sani da Gwaggo) 'yar Najeriya ce, farfesa, Masaniyar Harkar Siyasa a Najeriya kuma matar gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ce, sannan kuma memba ce a jam'iyyar All Progressive Congress.

Hafsat Ganduje Hafsat Ganduje
Rayuwa
Haihuwa jihar Kano, 28 Disamba 1960 (63 shekaru)
ƙasa Najeriya
Ƴan uwa
Abokiyar zama Abdullahi Umar Ganduje
Karatu
Harsuna Turanci
Hausa
Sana'a
Sana'a Malami

Tarihin Rayuwa da Karatu

An haifi Hafsat Ganduje a jihar Kano.Ta halarci makarantar firamare ta Malam Madori, da makarantar firamare ta kwana a jihar Kano, da Kwalejin Mata ta garin Kano. Hafsat Ganduje ta samu digiri na farko na fannin Kimiyyan Ilimi, acikin shekara ta dubu daya da Dari Tara da tamanin da daya (1981), ta zama Jagoran Ilimin halin ɗan Adam, a shekara ta alif ɗari tara da chasain da biyu (1992), ta zama Jagora na Kasuwanci, a shekara ta dubu biyu da hudu (2004), ta zama Doctor na fannin Falsafa a cikin Gudanarwa da Tsare-tsare, a shekara ta dubu biyu da Sha biyar(2015) duk daga Jami'ar Bayero, Kano.

Ayyuka

Ganduje ta fara aiki ne a matsayin malama a aji sannan bayan ta zama shugabar makaranta, daga baya ta zama malama a Kwalejin Ilimi ta Jami'ar Bayero, Kano, Najeriya. Jami'ar Maryniam Abacha ta Nijar ce ta ɗaga darajar ta zuwa matsayin Farfesa a shekara ta (2019).

Ita abokiyar zama memba ce a Cibiyar Gudanarwa ta ƙasar Nijeriya kuma ta samu lambobin yabo da yawa.

Aure da Iyali

Hafsat, ta auri Alhaji Abdullahi Umar Ganduje wanda a yanzu haka shi ne gwamnan Jihar Kano, sannan Allah ya albarkace su da ‘ya’ya.

Fes Ledi

Duk da cewa Hafsat ba ta da ofis ɗin amatsayin matar gwamna da ake kira ‘First Lady’, amma ta himmatu a ƙashin kanta wajen fito da shirye-shirye da tsare-tsaren da suke samar wa mata ayyukan dogaro da kai, gangamin samar da tallafin kayan karatu, kekunan ɗinki, tallafin kuɗaɗe domin mata su fara gudanar da ‘yan kananan sana’o’in dogaro da kai agarin Kano, dubban ɗaruruwan mata ne suka amfana da ƙoƙarinta da azamarta wacce suke ƙiran hakan a matsayin jinƙai a gare su.

Farfaganda

An yi ta yaɗa jita-jitan cewa Hafsat tana kaka-gida cikin sha’anin mulkin mijinta wanda ake cewa tana bayyana ra’ayinta ko lamunce ma waɗanda take son a basu kwangila ko naɗin mukamai, amma jami’an gwamnatin jihar sun sha karta wannan batun da cewa ba ta katsalandan wa gwamnan a sha’anin tafiyar da mulkin jihar Kano.

Manazarta

 

Tags:

Hafsat Ganduje Tarihin Rayuwa da KaratuHafsat Ganduje AyyukaHafsat Ganduje Aure da IyaliHafsat Ganduje Fes LediHafsat Ganduje FarfagandaHafsat Ganduje ManazartaHafsat GandujeAbdullahi Umar GandujeAll Progressives CongressKano (jiha)NajeriyaƊan Nijeriya

🔥 Trending searches on Wiki Hausa / هَوُسَ:

Nasarawa (Kano)Isaiah Oghenevwegba OgedegbeJamhuriyar Dimokuraɗiyyar KwangoYolaTsibirin BamudaSani Mu'azuAnnabawa a MusulunciWikipediaHausa–FulaniTanya AguiñigaAisha NajamuAnnabi SulaimanKabaraKungiyar Kwadago ta NajeriyaGombe (jiha)Abu HurairahSaudi ArebiyaArewacin NajeriyaJerin Gwamnonin Jihar ZamfaraRuwandaTarihin DauraPhilippa JohnsonAl'adar bikin cika-cikiZazzabin RawayaKajal AggarwalAlqur'ani mai girmaAmina GarbaZogaleYouTubeYaƙiWhatsAppfordKimiyyaISa AyagiShah Rukh KhanNasiru Ado BayeroHusufin rana na Afrilu 8, 2024Maryam Abubakar (Jan kunne)SiyasaMisraManchester City F.C.Hajara UsmanMaɗigoHarshen Karai-KaraiMaliHacktivist Vanguard (Indian Hacker)Yaƙin Duniya na IJerin manyan makarantun jihar TarabaJohannesburgShahoShugaban GwamnatiKalabaYahudawaGumelJalingoRingimNolu NdzundzuLokaciBiyafaraMasarautar Sarkin Musulmi, SokotoBuhariyyaRukunnan MusulunciZakkaAmal UmarKufaGandun DajiSomaliyaSahabban AnnabiAngelina JolieDauraDalar ZimbabweKogon da As'habKamaruMuhammadu Bello🡆 More