Rukunnan Musulunci

Rukunnan Musulunci Biyar (arkān al-Islām, larabci أركان الإسلام; ko arkān al-dīn, larabci أركان الدين, Rukunnan addini, Shika-shikan addini) abubuwa ne ko ayyuka waɗanda ginshikai ne, guda biyar a Musulunci, wadanda wajibai ne akan kowane mai imani, kuma sune farkon ginshikin rayuwar Musulmi.

Suna nan tattare a shahararren hadisin nan na mala'ika Jibril.

Rukunnan MusulunciRukunnan Musulunci
obligation (en) Fassara
Rukunnan Musulunci
Bayanai
Ƙaramin ɓangare na Taklif (en) Fassara
Bangare na Ahkam (en) Fassara
Farawa 631
Amfani aqidah (en) Fassara da Ibadah (en) Fassara
Facet of (en) Fassara Usūl al-Dīn (en) Fassara da Foundations of the Islamic religion (en) Fassara
Sunan asali أَرْكَانُ الْإِسْلَامِ
Addini Musulunci
Suna saboda Submission (en) Fassara
Al'ada Arab world (en) Fassara da Duniyar Musulunci
Part of the series (en) Fassara Shari'a
Muhimmin darasi Fiƙihu
Mabiyi Hidayah (en) Fassara
Ta biyo baya iman (en) Fassara
Nau'in spiritual practice (en) Fassara da religious activity (en) Fassara
Mawallafi God in Islam (en) Fassara
Ƙasa da aka fara Hijaz
Harshen aiki ko suna Larabci
Mai kwatanta Jibril (en) Fassara da Muhammad
Commemorates (en) Fassara Muhammad prophecy (en) Fassara
Ma'aikaci Musulmi da Mukallaf (en) Fassara
Location of creation (en) Fassara Makkah da Madinah
Hashtag (en) Fassara Five Pillars of Islam
Copyright status (en) Fassara public domain (en) Fassara
Kiyaye ta WikiProject Islam (en) Fassara

Shia, da Ahmadiyya, da Sunni dukkanin su sun yarda da muhimman bayani da ayyukan wadannan abubuwan, amma Shi'a basa kiran su da irin wannan sunan (see Ancillaries of the Faith, na Twelvers, da kuma Seven pillars of Ismailism). Sune suka hada rayuwar musulmi, sallarsa, taimakawa gajiyayyu, tsarkake kai daga zunubbai, da aikin hajji, ga wanda yake da ikon zuwa.

Shahada: (Imani)

Shahada ita ce miƙa wuya da tabbatar da Imani da bada gaskiya dake yarda da cewar babu wani abun bauta idan ba (Allah) ba, kuma Annabi Muhammad Manzon Sa ne, Kalman shahada dai rukuni ne na farko daga cikin Rukannan Musulunci guda biyar, wanda wajibi ne sosai mutum ya kiyaye ta , tana shigar da mutum cikin Musulunci in har ya furta , kuma ya kudur ce a zuciyar shi ,kuma yayi aiki da ma`anan abinda ya firta, kuma tana fitar da Mutum daga Musulunci idan ya saɓa ma`anar kalman ta hanyan yin saɓo ko shirka ko ya aikata wani aiki dake fitar da mutum daga Musulunci

Kalmar da kuma Ma`anarta

Kalma itace kamar haka:- Na shaida babu abinda bautawa da gaskiya sai Allah kuma Annabi Muhammad Manzo n Allah ne.

 Ma`anarta shine ka yarda akan karan kanka ba tilasta ka akayi ba cewa Allah shi kaɗai zaka bautamawa , shine ka tsayar da Tauhidi guda uku Rububiyya da Uluhiyya da Asma`i wassifat , kuma  baza ka haɗa shi da kowa ba a gurin bauta , wato baza kayi Shirka ba ko Tsafi ko wani nauyin na hakan, kuma kaji ka yarda cewa Annabi Muhammad manzan Allah. Ma`ana ɗan aike ne daga Allah. Ma`ana duk abinda Annabi Muhammad yace zaka yarda kuma ka gasgata ,abinda yayi umurni dashi kuma ko yayi hani, zaka aika ta sau da kafa.   

. Jawabi ne da yake a tsare, kuma ana furta shi ne da Larabci: lā ʾilāha ʾillā-llāhu muḥammadun rasūlu-llāh, (لَا إِلٰهَ إِلَّا الله مُحَمَّدٌ رَسُولُ الله) "Babu abun bautawa da gaskiya sai Allah (kuma) Annabi Muhammad Manzon Allah ne. Furta wannan jawabin nada muhimmanci sosai, Kafin mutum yazama Musulmi, ko ya dawo musulunci.

Salah: (Sallah)

Sallah (ṣalāh) itace bautar musulmai, Sallah ta kunshi yin salloli biyar kamar yadda Sunnah tazo dasu; sunayensu akan lokutan Amfani: Fajr (Subhi), Dhuhr (rana), ʿAṣr (Yamma), Maghrib (Almuru), da kuma ʿIshāʾ (dare). Sallar Fajr ana gudanar da ita ne kafin fitowar(tasowar) rana, Dhuhr kuma ana yinta ne a tsakiyar rana, bayan rana yayi zawali, Asr kuma da yammaci ake yinta kafin faduwar rana, Maghrib da almuru bayan rana ya fadi, sannan sai sallar Isha'i da akeyinta acikin dare. Duk wadannan salloli anayinsu ne ta hanyar kallon Kaaba a Mecca daya samar da muhimmin ginshiki a cikin alumman Musulmi. Musulmi sai sun wake jiki kafin yin Sallah; wannan wankin ake kira da wudu

Zakāh: (Zakkah)

Zakkāh Zakka rukuni ne daga cikin Rukannan Musulunci guda biyar ana bayar da wani sashi ne na dukiyar mutum idan dukiyar ta kai nisabi.

Sawm: Azumi

Azumi rukuni ne daga cikin Rukannan Musulunci guda biyar , ana kin cin abinci ne da kuma kin shan abun sha tin daga fitowar alfijir har zuwa faduwar rana , haka za`a tayi har sai anyi wata daya na watan Ramadan tukunnan aka sauke nauyin farillan. ref>Al Kur'ani 2:196 .

Hajj: Aikin Hajji

Hajj itace ziyarar ibada dake faruwa a kowace watan musulunci na Dhu al-Hijjah zuwa Makkah. Kowani musulmi baligi dake da iko ya zama wajibi yayi aikin hajji a rayuwarsa koda sau ɗaya ne, Hajji rukuni ne daga cikin Rukannan Musulunci guda biyar ga wanda Allah ya bashi ikon zuwa ,ana yin aikin hajji ne kaɗai a makkah, kuma ba`a son mutum ya tafi aikin hajji alhali akwai bashi akan shi ko iyalansa na cikin wani hali ,ko kuma zasu shiga idan har ya tafi. .

Manazarta


[[Category:Kalma shahada]

Tags:

Rukunnan Musulunci Shahada: (Imani)Rukunnan Musulunci Kalmar da kuma Ma`anartaRukunnan Musulunci ManazartaRukunnan MusulunciAddiniMusulmiMusulunciWajibi

🔥 Trending searches on Wiki Hausa / هَوُسَ:

Jerin Sarakunan KanoDana AirJerin jihohi a NijeriyaRukunnan MusulunciRamsey NouahPatrice LumumbaRockmond DunbarJerin kasashenIlimiBarau I JibrinWhatsAppAbdullahi Bala LauHankakaAbubakar Bashir MaishaddaJerin shugabannin jihohin NajeriyaAlaskaMutuwaTurkmenistanGidan zooBasirKabir SaniPortugalKasuwanciMusulunci a AfrikaHujra Shah MuqeemTekun AtalantaƘofofin ƙasar HausaKa'idojin rubutun hausaDahiru Usman BauchiCutar hanta AKanadaNejaRotimi AmaechiSoyayyaBello TurjiHauwa'uTarihin HabashaSaidu DansadauNuhu PolomaImam Malik Ibn AnasHaɗejiyaAl'aurar NamijiAsabe MadakiAli NuhuAnnabi SulaimanAmedework WalelegnYemenMisraRuwaSahabban AnnabiAndré MacangaBagdazaKebbiJuyin Juya HaliLaylah Ali OthmanTarihin AmurkaMabiya SunnahKoriya ta ArewaShehu Musa Yar'AduaHafsat IdrisTahir I TahirSadiya Umar FarouqBirnin KuduHausawaJoe BidenWaziri ZayyanaKano (birni)AnguluAure🡆 More