Jiha Gombe: Jiha a Najeriya

Gombe jiha ce dake Arewa maso Gabashin Najeriya.

Tayi iyaka daga Arewa da Arewa maso gabas da jihohin Borno da Yobe, daga Kudu kuwa da Jihar Taraba, daga Kudu maso yamma kuwa da Jihar Adamawa sannan daga Yamma da Jihar Bauchi. Ta samo asalin sunanta daga babban birninta kuma yanki mafi girma a jihar wato Babban Birnin Gombe - kuma an ƙirƙireta ne daga sashin Jihar Bauchi a ranar 1 ga watan Oktoban shekara ta alif ɗari tara da cassain da shida 1996. Jihar na daga cikin jihohin da ke ɗauke da ƙabilu iri-iri a Najeriya. Acikin jihohi 36 da Abuja na Najeriya, Jihar Gombe itace Jiha ta 21 a girma, kuma ta 32 a yawan jama'a, da mutane aƙalla miliyan 3.25 dangane da ƙiyasin shekarar 2016.

Jiha Gombe: Bayani, Ƙananan Hukumomi, AlummaGombe
Jiha Gombe: Bayani, Ƙananan Hukumomi, Alumma
Jiha Gombe: Bayani, Ƙananan Hukumomi, Alumma

Suna saboda Gombe
Wuri
Jiha Gombe: Bayani, Ƙananan Hukumomi, Alumma
 10°15′N 11°10′E / 10.25°N 11.17°E / 10.25; 11.17
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya

Babban birni Gombe
Yawan mutane
Faɗi 3,256,962 (2016)
• Yawan mutane 173.54 mazaunan/km²
Harshen gwamnati Turanci
Labarin ƙasa
Yawan fili 18,768 km²
Sun raba iyaka da
Bayanan tarihi
Mabiyi Jihar Bauchi
Ƙirƙira 1 Oktoba 1996
Tsarin Siyasa
Majalisar zartarwa executive council of Gombe State (en) Fassara
Gangar majalisa Gombe State House of Assembly (en) Fassara
Bayanan Tuntuɓa
Kasancewa a yanki na lokaci
Lamba ta ISO 3166-2 NG-GO
Wasu abun

Yanar gizo mof.gm.gov.ng
Jiha Gombe: Bayani, Ƙananan Hukumomi, Alumma
Jiha Gombe: Bayani, Ƙananan Hukumomi, Alumma
Jihar gombe
Jiha Gombe: Bayani, Ƙananan Hukumomi, Alumma
Sarkin gombe
Jiha Gombe: Bayani, Ƙananan Hukumomi, Alumma
gombe post ofis

Ta fuskar yanayin ƙasa, Jihar tana da ƙasa nau'in Tropical West Sudanian Savanna. Muhimman wurare a jihar sun haɗa Kogin Gongola, wanda ke kwarara ta arewaci da Gabashin Gombe zuwa cikin tafkin Dadin Kowa Dam zuwa gaɓar Tsaunukan Muri da ke can yankin kudancin jihar. Daga cikin dabbobi asali na jihar akwai nau'in macizai irin su: carpet viper, puff adder, da kuma Egyptian cobra da kuma dabbobi irin su dorinar ruwa, Senegal parrot, da kuma grey-headed kingfisher.

Jihar Gombe na ɗauke da ƙabilu da dama, yayinda Ƙabilar Fulani suka mamaye yankin arewaci da tsakiyar jihar tare da Bolewa, Kanuri, da kuma Hausawa. A yayin ƙabilu irin su Cham, Dadiya, Jaranci da Kamo, Pero, Tangale, Tera, da kuma mutanen Waja da suka mamaye yankunan gabashi da kudancin jihar.

Kafin zuwan Turawa, yankin Jihar Gombe ta yau tana ɗauke da ƙasashe da dama masu zaman kansu, har zuwa farkon karni na 1800, lokacin da Fulani suka ƙwace yankuna da dama na yankin kuma suka haɗeta a matsayin Masarautar Gombe a ƙarƙashin Daular Sokoto. A cikin karni na 1900, Turawan mulkin mallaka sun mamaye masarautar da yankunan gefen ta kuma sun haɗeta acikin Yankin Mulkin Mallaka na Arewacin Najeriya, inda daga baya ta zamo Colonial Nigeria, kafin daga bisani ta samu 'yanci a1960 kuma ta zamo ƙasa Najeriya. Bayan samun 'yancin kai kuwa, Jihar Gombe ta yau ta faɗa ƙarƙashin Arewacin Najeriya har zuwa 1967 lokacin da aka raba yankin kuma jihar ta faɗa ƙarƙashin Jihar Arewa ta Gabas. Bayan an raba Jihar Arewa maso Gabas, an ƙirƙiri Jihar Bauchi a shekarar 1976 tare da Sauran jihohi guda goma. Shekaru ashirin bayan haka (1996) an cire wasu gungun ƙananan hukumomi daga yammacin Jihar Bauchi don samar da Jihar Gombe.

Dangane da fannin tattalin arziƙi, Jihar Gombe ta dogara ne akan noma da kiwo, da man fetur, inda ake shuka gero, masara, gyaɗa, dawa da tumatir tare da kiwon dabbobi kamarsu raƙumma, shanu, akuyoyi da kuma tumaki. Sauran muhimman masana'antu sun haɗa da hidindimu na zamani da ake gudanarwa musamman a birnin Gombe. Jihar Gombe itace jiha ta huɗu a jerin ƙarancin Cigaban al'ummaa.

Tana da yawan fili kimanin kilomita murabba’i 18,768 da yawan jama’a miliyan biyu da dubu uku da hamsin da uku (ƙidayar yawan jama'a shekara ta 2006). Babban birnin tarayyar jahar ita ce Gombe. Muhammadx Inuwa Yahaya shi ne gwamnan jihar tun zaben shekara ta 2015 har zuwa yau. Mataimakin gwamnan shi ne Dr Manasa Daniel Jatau. Dattijan jihar su ne: Sarakunan gargajiya, Malaman addini da kuma jigogin siyasa.

Bayani

Jihar na da faɗin fili na kimanin 20,265 km2 da kuma mutane kimanin mutum 2,365,000 a shekara ta 2006. An ƙirkire ta ne a cikin watan Oktoban 1996, daga yankin tsohuwar Jihar Bauchi a lokacin mulkin Shugaba Sani Abacha. Jihar na nan a yankin ƙasar Najeriya mai nau'in tsirrai irin na Guinea savannah da Sudan savannah. Akwai tuddai masu ɗan bisa, duwatsun ƙasa da kuma duwatsu na daga witar volcano a yankunan tsaunukan garin. Zaman jihar a yankin savanna na arewa maso gabashin Najeriya yasa jihar ta haɗa iyaka da jihohi kaman Borno, Yobe, Taraba, Adamawa da Bauchi.

Jihar Gombe ta na yanayi guda biyu: yanayin rani (daga watan Nuwamba zuwa March) da kuma damuna (daga watan Aprelu zuwa Oktoba) tare da matsakaicin ruwam sama na kimanin 850mm.

Gwamnan jihar, Muhammad Inuwa ke javorancin jihar tare da taimakon muƙarrabai 24 daga majalisar dokoki na jihar. Jihar Gombe na da ƙananan hukumomi 11 da kuma masarautu na gargajiya guda 14. Tana da sanatoci guda 3 da kuma 'yan Mjalisar Tarayyar Najeriya guda shida.

Ƙananan Hukumomi

Jihar Gombe nada Kananan hukumomi guda goma sha ɗaya (11). Sune kamar haka:

Karamar Hukuma Fadin kasa (km2) Adadin 2006
Mutane
Cibiyar Karamar Hukuma Lambar aika
sako
Akko 2,627 337,853 Kumo 771
Balanga 1,626 212,549 Tallase 761
Billiri 737 202,144 Billiri 771
Dukku 3,815 207,190 Dukku 760
Funakaye 1,415 236,087 Bajoga 762
Gombe 52 268,000 Gombe (city) 760
Kaltungo 881 149,805 Kaltungo 770
Kwami 1,787 195,298 Mallam Sidi 760
Nafada 1,586 138,185 Nafada 762
Shongom 922 151,520 Boh 770
Yamaltu/Deba 1,981 255,248 Deba Habe 761

Al'umma

Jihar Gombe na ɗauke da al'ummomi iri-iri, yayinda Fulani suka mamaye mafiya yawancin yankin arewacin jihar. Fulani sun mamaye Kusan ƙananan hukumomi guda 6 na Jihar Gombe. Waɗannan ƙananan hukumomi sun haɗa da Dukku, Kwami, Funakaye, Nafada, Akko, kuma ƙaramar hukumar Gombe. Bayan Fulani akwai kuma Tangale, da ke rayuwa a yankin Billiri da Kaltungo. Sauran ƙabilu sun haɗa da the Hausawa Tula, Tera (Yamaltu-Deba), Waja, Bolewa, da kuma Kanuri.

Harsuna

An zayyano harsunan Jihar Gombe dangane da ƙananan hukumominsu a teburi da ke ƙasa:

LGA Area (km2) Census 2006
population
Administrative capital Postal
code
Akko 2,627 337,853 Kumo 771
Balanga 1,626 212,549 Tallase 761
Billiri 737 202,144 Billiri 771
Dukku 3,815 207,190 Dukku 760
Funakaye 1,415 236,087 Bajoga 762
Gombe 52 268,000 Gombe (city) 760
Kaltungo 881 149,805 Kaltungo 770
Kwami 1,787 195,298 Mallam Sidi 760
Nafada 1,586 138,185 Nafada 762
Shongom 922 151,520 Boh 770
Yamaltu/Deba 1,981 255,248 Deba 761

Ilimi

Jami'o'i a jihar Gombe

Manyan jami'oi na Jihar Gombe sun haɗa da:

Makarantun Sakandare

  • Matrix International Academy
  • Gombe High School
  • Pen Resource Academy
  • Demonstration Secondary School
  • Government Day Science Secondary School
  • Ilimi International School
  • Gombe international School
  • JIBIWIS Arawa Secondary School
  • All-saint Secondary School
  • Darul Arqam Academy
  • Government Day Hassan Central
  • Yahya Ahmad Model School
  • Government Senior Secondary School Herwagana, Gombe
  • Government Senior Secondary School Gandu
  • Ubaidah Academy
  • Government Day Secondary School Gandu

Kiwon Lafiya

Jihar Gombe nada cibiyoyin kiwon lafiya masu yawa, dukkanin su i sun samu ne ta karkashin gudanarwa sashi guda uku, gwamnatin jiha, Gwamnatin tarayya da kuma cibiyoyi mallakin dai-daikun mutane. Wadannan cibiyoyi sun hada da :

Cibiyoyi Karkashin Gwanatin Tarayya

  • Federal Teaching Hospital Gombe (FTHG)

Cibiyoyi Karkashin Gwamnatin Jiha

  • Billiri General Hospital
  • Gombe State Specialist Hospital
  • Arawa Primary Healthcare
  • Gabukka Primary Healthcare
  • Doma Primary Healthcare
  • Pantami Primary Healthcare
  • Zainab Bulkachuwa Women and Children Hospital
  • Town Maternity (Gidan Magani).

Cibiyoyin da ba na Gwamnati ba

  • Miyetti Hospital
  • Musaba Hospital
  • Sabana Hospita
  • AHAJAS Memorial Hospital

Cibiyoyin Magun-guna

  • Kumbi chemist
  • Sauki phamarcy
  • A.A. Aliyu Mega Store
  • Jam Bandu Pharmacy

Ma'adanai

Jihar Gombe na daya daga cikin jahohi masu tarin albarkatun kasa a Nigeria wanda ke samar da kayan tasarrufi da ma'aikatu ke amfani dashi, yan kasuwa ke kasuwance su, wasun kuma ake amfani dasu a matsayin abinci, wadannan ma'adanai sun hada da :

Ma'adanai da Ake Hakowa

  • Laka
  • Dayen Mai

Ma'adanai da Ke Tsira

Gwamnoni

A ƙasa an jero sunayen gwamnoni da jagorori na Jihar Gombe.

Name Take Lokacin hawa mulki Lokacin sauka daga mulki Jam'iyya
Group Captain Joseph Orji Administrator 7 Oct 1996 Aug 1998 Military
Abubakar Habu Hashidu Governor 29 May 1999 29 May 2003 APP
Mohammed Danjuma Goje Governor 29 May 2003 May 2011 PDP
Ibrahim Hassan Dankwambo Governor May 2011 29 May 2019 PDP
Muhammad Inuwa Yahaya Governor May 2019 Incumbent APC

Sanannun Mutane

Wuraren ziyara a Gombe

Wuraren buɗe idana a jihar sun haɗa da:

  • Tomb of Sultan Attahiru
  • Bubayero's Tomb
  • Shahararren Bima Hill
  • Tula Plateau
  • Bulok Warm Spring
  • Kalam Hill


  • Cham Valley
  • Tsaffi burbushin Binga
  • Maƙabartar Major Mash
  • Maƙabartar LT Phillips
  • Bace Hills
  • Tula Hideout Caves
  • Kanawa Forest

Manazarta


Jihohin Najeriya
Babban birnin tarayyar (Abuja) | Abiya | Adamawa | Akwa Ibom | Anambra | Bauchi | Bayelsa | Benue | Borno | Cross River | Delta | Ebonyi | Edo | Ekiti | Enugu | Gombe | Imo | Jigawa

Kaduna | Kano | Katsina | Kebbi | Kogi | Kwara | Lagos | Nasarawa | Neja | Ogun | Ondo | Osun | Oyo | Plateau | Rivers | Sokoto | Taraba | Yobe | Zamfara

Tags:

Jiha Gombe BayaniJiha Gombe Ƙananan HukumomiJiha Gombe AlummaJiha Gombe HarsunaJiha Gombe IlimiJiha Gombe Kiwon LafiyaJiha Gombe MaadanaiJiha Gombe GwamnoniJiha Gombe Sanannun MutaneJiha Gombe Wuraren ziyara a Gombe[31]Jiha Gombe ManazartaJiha GombeAbujaAdamawaArewa (Najeriya)Bauchi (jiha)BornoGombe (birni)Jahar TarabaJerin Jihohin Najeriya dangane da faɗin ƙasaJerin yawan habakar mutane a jahohin NajeriyaNajeriyaYobe

🔥 Trending searches on Wiki Hausa / هَوُسَ:

Daniel Dikeji MiyerijesuWidad BertalPakistanHassan Usman KatsinaZinareHalima Kyari JodaSiyasaZamfaraZanzibarAfirka ta YammaAbubakar RimiMaganin gargajiyaNicki MinajAdamawaJerin Gwamnonin Jahar SokotoƊan wasaBan dariyaMaleshiyaUlul-azmiTarihin Kasar SinAdamu a MusulunciRuwan BagajaAuren HausawaJerin ƙauyuka a jihar BauchiBaburaUmmi KaramaMuhammad Ibn Musa AlkhwarizmiBebejiAminu Ibrahim DaurawaMatan AnnabiSadi Sidi SharifaiKogin LogoneMalamiRijiyar ZamzamBernadette CostonSiriyaKannywoodShukaGabonGabas ta TsakiyaYaƙin BadarSarakunan Gargajiya na NajeriyaRiyadhJerin gidajen rediyo a NajeriyaTuraiYahudanciTarihiJanabaWaƙaHausawaIlimin lissafi a duniyar Islama ta tsakiyaMasarautar DauraJerin ƙauyuka a jihar JigawaSurahZamanin Zinare na MusulunciSani Musa DanjaAntatikaDoualaKelechi IheanachoHarshan cornishMansura IsahKunkuruSanda KuraHarshen HausaMuhammadu BuhariDara (Chess)NajeriyaOncologyCoca-colaTauraNuhu PolomaUmar Ibn Al-KhattabIfẹNaziru M AhmadGidan Tarihi na ƙasa na Habasha🡆 More