Jalingo ita ce babbar birnin jihar Taraba (a da tana ƙarƙashin Jihar Gongola ne), kuma ita ce cibiyar gwamnatin jihar.
Mafiya yawan al'umman dake zaune a garin Jalingo Fulani ne. Amma akwai Kuteb, Hausawa da wasu yararrukan dake zaune a garin suna gudanar da harkokinsu, an kiyasta adadin al'umman birnin sunkai dubu dari da goma sha takwas (118,000). Garin Jalingo yana a tsakiyar duwatsu ne. Jalingo tana da masarauta da sarakunan yanki. Masarautar ta samo asali ne daga Musarautar Muri.
Jalingo | |||||
---|---|---|---|---|---|
| |||||
| |||||
Wuri | |||||
| |||||
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya | ||||
Jiha | Taraba state | ||||
Babban birnin | |||||
Yawan mutane | |||||
Faɗi | 660,213 (2016) | ||||
• Yawan mutane | 3,456.61 mazaunan/km² | ||||
Labarin ƙasa | |||||
Yawan fili | 191 km² | ||||
Altitude (en) | 351 m | ||||
Bayanan Tuntuɓa | |||||
Lambar aika saƙo | 660213 | ||||
Kasancewa a yanki na lokaci |
A cikin garin Jalingo, akwai makarantun daban-daban masu tarin yawa kama daga firamari, sakandari har ma da Jami'o'i na Ilimi da Likitanci; wanda wasu na gwamnati (government) ne wasu kuma mallakan Anguwa ne (community) wasu kuma mallakan mutane ne (private).
Daga cikin makarantun firamari mallakan gwamnati akwai irin:
Haka zalika, ga wasu daga cikin makarantun firamari na mallakan mutane:
Bugu da kari, ga jerin makarantun Sakandari na gwamnati, anguwa da kuma na mutane:
Har ila yau, akwai makarantu na kwallejin Ilimi da kimiya kamar haka:
Bugu da kari, akwai Jami'a guda daya a cikin garin: Taraba State University Jalingo, wacce ake kira da TSU.
Karamar hukumar Jalingo a kasancewar ta fadar Jiha, tana da kasuwanni a cikin ta masu tarin albarka, wanda ake saye da sayarwa. Daga cikin wadannan kasuwanni akwai:
This article uses material from the Wikipedia Hausa / هَوُسَ article Jalingo, which is released under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 3.0 license ("CC BY-SA 3.0"); additional terms may apply (view authors). An samar da dukkan muƙaloli a ƙarƙashin lasisin Creative Commons Attribution/Share-Alike; tana yiwuwa wasu ƙa'idoji su yi tasiri. Ku duba Ka'idojin Amfani na Gidauniyar Wiki domin ƙarin bayani. Images, videos and audio are available under their respective licenses.
®Wikipedia is a registered trademark of the Wiki Foundation, Inc. Wiki Hausa / هَوُسَ (DUHOCTRUNGQUOC.VN) is an independent company and has no affiliation with Wiki Foundation.