Sani Musa Danja: Dan wasan kwaikwayo na hausa sannan kuma mawaki

Sani Musa Danja: Aiki, Fina-finai, Iyali Sani Musa Danja
Sani Musa Danja: Aiki, Fina-finai, Iyali
Rayuwa
Cikakken suna Sani Musa Abdullahi
Haihuwa Fagge, 20 ga Afirilu, 1973 (50 shekaru)
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Hausa
Karatu
Harsuna Turanci
Hausa
Pidgin na Najeriya
Yarbanci
Sana'a
Sana'a Jarumi
Imani
Addini Musulunci

Sani Musa Abdullahi, wanda aka fi sani da Sani Danja ko kuma Danja {An haife shi a ranar 20 ga watan Afrilu shekaralif ɗari tara da saba'in da Uku1973} Miladiyya. jarumin fim ne a Nijeriya, furodusa, darekta, mawaƙi kuma mai rawa. Yana fitowa a finanin masana'antar Kannywood da kuma na kudancin Najeriya Nollywood.. A watan Afrilun shekara ta dubu biyu da Sha takwas 2018 Etsu Nupe, Yahaya Abubaka ya nada shi a matsayin Zakin Arewa. Ya kasance ɗaya daga cikin shahararrun yan wasan kwaikwayo a Kannywood

Aiki

Ya shiga harkar finafinan Hausa a shekarar 1999 a amatsayin dalibi. Danja ya fito a fina-finai da dama irin su, Manakisa, warya tabi Kwarya, Jaheed, Nagari, Wasiyya, Harsashi, Gidauniya, Daham, Jarida, Matashiya, da sauransu. A shekarar 2012 ya fara haskawa a Nollywood'Yar Kogin.

Fina-finai

Sani Musa Danja ya yi, ya shirya kuma ya ba da umarni a fina-finan Kannywood da Nollywood . Daga cikinsu akwai:

Sunan Fim Shekara
Yar agadez 2011
A Cuci Maza 2013
Albashi (Albashi) 2002
Bani Adam 2012
Budurwa 2010
Da Kai zan Gana 2013
Daga Allah ne '' (Daga Allah ne) 2015
Daham 2005
Dan Magori 2014
Duniyar nan 2014
Fitattu 2013
Gani Gaka 2012
Gwanaye 2003
Hanyar Kano 2014
Kukan Zaki (Kukan zaki) 2010
Daya bangaren 2016
Buri uku a duniya (Buri guda uku a duniya) 2016

Iyali

Sani danja ya auri Mansura Isah Allah ya azurta su da ƴaƴa huɗu.

Manazarta

🔥 Trending searches on Wiki Hausa / هَوُسَ:

TarihiWahabiyanciFilmAdele na PlooyWhatsAppMajalisar Dattijai ta NajeriyaPakistanAfirkaJerin ƙauyuka a jihar BauchiKasashen tsakiyar Asiya lTufafiJerin sunayen Allah a MusulunciAuta MG BoyAduduAmen Edore OyakhireDuniyar MusulunciBalagaKebbiKaduna (jiha)Bola TinubuAishwarya RaiJerin AddinaiMuhammadu BelloMoroccoAliyu Magatakarda WamakkoAddiniMaruruTanya SeymourMarc-André ter StegenAbu HurairahKabiru Mai KabaJerin Sunayen Gwamnonin Jihar JigawaAisha NajamuRundunar ƴan Sandan NajeriyaSaudiyyaJapanAyar Al'arshiTuraiAisha TsamiyaNamenjGonda BetrixRubutuLandanHannatu Bashir2008Zulu AdigweMansura IsahMuhammadBolibiyaGine-BisauAnnabiSautiAzareYusuf Maitama SuleHassana MuhammadAkwa IbomMisraJimaAllu ArjunA'Darius PeguesHamza al-MustaphaFuruciNasir Ahmad el-RufaiƘananan hukumomin NijeriyaIsaiah Oghenevwegba OgedegbeKaabaAnnabi YusufLibyaMasarautar KatsinaPhoenixDuniyoyiKhalid ibn al-WalidAsalin jinsi🡆 More