Jiha Kaduna: Jiha a Najeriya

Jihar Kaduna wace Ake mata kirari da (Cibiyar Ilimi), ta samu wannan sunan ne a Allah ya azurta ta da makarantu na Ilimi, Kaduna jiha ce dake a Arewacin Najeriya.

Babbar cibiyar birnin Jihar na da suna Kaduna, wanda ta kasance birni ta 8 mafi girma daga cikin biranen ƙasar Najeriya. Kamar yadda yake dangane a ƙiyasin shekara ta 2006. An ƙirƙiri Jihar Kaduna shekara 7 bayan samun ƴancin kai, an ƙirƙire ta a shekarar 1967, da sunan Jihar Tsakiyar Arewa, wadda kuma ta haɗa da Jihar Katsina ta yanzu, Kaduna ta samu iyakar ta ne a shekarar 1987. Kaduna Ita ce jiha ta uku mafi girman ƙasa kuma ta haɗa da yawan mutane daga cikin sauran Jihohin Najeria, ana kuma ma Jihar Kaduna laƙabi ko kirari da Cibiyan koyon Ilimi (Centre of Learning,) saboda ta kasance tana da manyan makarantu na gaba da sakandare masu muhimmanci, kamar su Jami'ar Ahmadu Bello, Jami'ar Tsaro ta Najeriya da dai sauran su.

Jiha Kaduna: Asalin suna, Tarihi, Kananan HukumomiKaduna
Kaduna State (en)
Jiha Kaduna: Asalin suna, Tarihi, Kananan Hukumomi

Suna saboda Kaduna
Wuri
Jiha Kaduna: Asalin suna, Tarihi, Kananan Hukumomi
 10°20′N 7°45′E / 10.33°N 7.75°E / 10.33; 7.75
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya

Babban birni Kaduna
Yawan mutane
Faɗi 8,252,366 (2016)
• Yawan mutane 179.19 mazaunan/km²
Harshen gwamnati Turanci
Labarin ƙasa
Yawan fili 46,053 km²
Sun raba iyaka da
Bayanan tarihi
Mabiyi Jihar Arewa ta Tsakiya
Ƙirƙira 1976
Tsarin Siyasa
Majalisar zartarwa Majalisar zartaswa ta jihar Kaduna
Gangar majalisa Kaduna State House of Assembly (en) Fassara
Bayanan Tuntuɓa
Lambar aika saƙo 720001
Kasancewa a yanki na lokaci
Lamba ta ISO 3166-2 NG-KD
Wasu abun

Yanar gizo kdsg.gov.ng
Jiha Kaduna: Asalin suna, Tarihi, Kananan Hukumomi
Lugard Hall, Kaduna.parliamentary house of Assembly capital north region
Jiha Kaduna: Asalin suna, Tarihi, Kananan Hukumomi
kaduna state polytechnic.03.jpg
Jiha Kaduna: Asalin suna, Tarihi, Kananan Hukumomi
Kaduna capital plaza

Asalin suna

Jiha Kaduna: Asalin suna, Tarihi, Kananan Hukumomi 
Lambar mota ta jahar kaduna
Jiha Kaduna: Asalin suna, Tarihi, Kananan Hukumomi 

Jihar Kaduna ta samo sunan ta Kaduna ne daga kalmar kada, jam'in kalmar Kadduna, sai aka cire harafin ''D" sai ya koma "Kaduna". A wani ƙaulin kuma, an ce kalmar ta Kaduna ta samo asali ne daga yaran Gwari, sun kasance Odna suna nufin "Kogi" kasancewar kaduna a zagaye take da rafuka. Tambarin Jihar Kaduna dai shi ne hoton Kada.

Tarihi

Jiha Kaduna: Asalin suna, Tarihi, Kananan Hukumomi 
Gadar masallacin sultan bello a Kaduna
Jiha Kaduna: Asalin suna, Tarihi, Kananan Hukumomi 
Sarauniya amina lokacin da take mulki
Jiha Kaduna: Asalin suna, Tarihi, Kananan Hukumomi 
Crocodile

A zance mafi inganci ba a san lokacin da mutane suka fara rayuwa ba a yankin Kaduna, amma akan iya tina garin a wasu ma'aunai na tarihi da suka shuɗe, kuma hakan ya faru ne kasancewar yawan ƙabilun da ke zaune a cikin garin, Haƙiƙa birnin ya kafu ne tun kafin zamanin Usman ɗan Fodiyo wato tun tale-tale can a shekarun baya, birnin Kaduna ya kasance cibiyar jamhuriyyar Arewa tun daga shekarar 1917, har zuwa shekarar 1967, tarihi ya nuna cewa an mallake kaduna ne ga masu mulkin mallaka na turawan ƙasar Birtaniya, babban kwamandan yaƙin mulkin mallaka Frederick Lugard ya kwace Kaduna a shekarar 1897, da shi da sauran yan koransa. Daga baya kuma suka yi hadin gwuiwa tsakanin Kudancin Najeriya da kuma arewacin Najeriya a shekarar 1914. Wasu daga cikin tsofaffin garuruwan Kaduna sun haɗa da Zariya, Kafanchan da kuma Nok, wanda waɗannan garuruwan tarihi ya kasa riskan farkon garuruwan da tarihinsu tun asali. Garin Zaria shi ne tsohon gari a duk faɗin yankin Kaduna, wanda ake tunanin an kafa garin ne a shekarar 1536, wanda a wannan lokacin garin baya da suna, amma daga bisani ana kiran garin da sunan wata shahararriyar sarauniya wato Amina (Sarauniya Amina).

Sannan Kaduna ta kasance cibiyar addinin musulunci a yankin arewa, kuma daga ciki ne aka baiwa Katsina jiha. Kaduna birni ne na Hausawa ko dayake daga baya Kaduna ta kasance tana ɗaya daga cikin manyan biranen da sukafi tara kabilu daban-daban, a kalla akwai kabilu a cikin Kaduna da suka kusan 57. Jihar Kaduna a da ta hada manyan jahohi a cikinta irin su Katsina, kafin daga bisani aka cire su aka mayar da su Jihohi masu zaman kansu, a da Jihar Kaduna ita ce babban birnin tarayyar yankin arewacin najeriya a zamanin mulkin mallaka na turawa, kafin a bata babban birnin, da Zungeru a1903 zuwa1923) dake Lokoja a (1897 zuwa 1903) su ne manyan biranan. A shekarar 1923 zuwa 1966 aka bama Kaduna babban birnin tarayyar yankin arewacin najeriya. Jahar Kaduna ita ce ta huɗu 4 a jadawalin jihohin da suka fi fadin kasa a Najeriya, kuma sannan ita ce ta 3 a jihohin da suka fi kowane yawan mutane a Najeriya. Babban birnin Jihar Kaduna Shi ne Kaduna

Jiha Kaduna: Asalin suna, Tarihi, Kananan Hukumomi 
Babban Kogin Jahar Kaduna kenan wanda ake tinanin jahar ta samo suna daga gare shi



Kananan Hukumomi

Jihar Kaduna tana da matuƙar faɗin gaske, wanda faɗin ƙasar ta ya kai kimanin kilomita 46,053 km2, Kaduna ita ce jiha ta Huɗu da ta fi kowacce jiha girman ƙasa, kuma tana da ƙananan hukumomi guda 23, kowacce ƙaramar hukuma ta na da shugaba da ƙananan garuruwa, ƙananan hukomomi su ne kamar haka:

Jiha Kaduna: Asalin suna, Tarihi, Kananan Hukumomi 
wannan sashin jihar kaduna kenan daga cikin taswirar Nijeriya.
Adadi Karamar Hukama Fadin Kasa Shuwagabanni
1 Birnin Gwari
2 Chikun
3 hukumar Giwa
4 Igabi
5 Ikara
6 Jaba
7 Jama'a
8 Kachia
9 Kaduna ta arewa
10 Kaduna ta kudu
11 Kagarko
12 Kajuru
13 Kaura
14 Kauru
15 Kubau
16 Kudan
17 Lere
18 Makarfi
19 Sabon-Gari
20 Sanga
21 Soba
22 Zangon-Kataf
23 Zariya

Mulki

Jiha Kaduna: Asalin suna, Tarihi, Kananan Hukumomi 
Nasir el Rufa'i da gwamna Lalong na jahar plateau

A jihar Kaduna, akwai masu mulki daban-daban da suka haɗa da sarakuna, zaɓaɓɓun shuwagabanni na mulkin dimukuradiya, a jihar ta Kaduna akwai Gwamna, Ƴan Majalisa, ƴan majalisar Dattijai, da kuma Sarakuna masu mulkin gargajiya. Shuwagabanni a ɓangaren dimukuradiya ana zaɓen su ne duk bayan shekaru Huɗu, su kuma sarakunan gargajiya suna gada ne a wajen iyaye da kakanni, kuma zasu iya yin mulki iya tsawon rayuwar su, amma gwamna yana da cikakken ikon da zai iya cire/nada kowane sarki a jihar sa.

Dimukuradiya

A jihar Kaduna, akwai gwamna da mataimakin gwamna, kuma wadannan su ne masu cikakken mulki a cikin jihar ta Kaduna, kuma zaben su ake yi a duk bayan shekaru hudu, wanda yanzu haka Mallam Uba sani shi ne gwamnan jihar Kaduna da kuma Hadiza Sabuwa Balarabe a matsayin mataimakiyar gwamnan jihar ta Kaduna. A tsarin mulkin dimokuraɗiyya akwai ƴan majalisun jiha masu kula da dokokin jihar da kuma tsarinta, sannan akwai sanatoci uku masu kula da yanki uku na Jihar Kaduna su ne; Suleiman Abdu Kwari, Danjuma Laah da kuma Uba Sani.

Mulkin Gargajiya

Jiha Kaduna: Asalin suna, Tarihi, Kananan Hukumomi 
gadar masallacin sarkin musulmai bello kaduna
Jiha Kaduna: Asalin suna, Tarihi, Kananan Hukumomi 
Shehu Idris Sarkin Zazzau

Akwai sarakuna da hakimai a kowanne karamar hukuma da kuma gunduma, amman da manyan sarakunan gargajiya su ne kamar haka; Sarkin Zazzau Shehu Idris, sarkin Birnin gwari, sarkin Nok da kuma sarkin Kafanchan, wadannan sarakunan suna da ka'idojin salan mulki ga iya mutanan su kadai, sannan gwamnan jahar yana da cikakken ikon da zai sauke su ya daura wanda yake so.

Jiha Kaduna: Asalin suna, Tarihi, Kananan Hukumomi 
Wannan tambarin kasar Hausa kenan. Kaduna tana daya daga cikin jahohin Hausa.

Kabilu

Jahar Kaduna jaha ce mai tarin al’adu da ire-iren abinci daban-daban Kamar haka:

  1. Hausawa
  2. Fulani
  3. Gwarawa
  4. Katafawa
  5. Birom da dai sauran
  • .Ire iren abinci:

Tuwon masara da na dawa,da na gero da ɗan wake da dambu da fate da doya da dankalin Hausa da rogo da koko da dai sauran su.

Addinai

Addinai biyu sune manyan addinan jahar Kaduna, wato addinin Musulunci da kuma addinin kiristanci, kasancewar addinai ne manya akwai alaka mai tsami a tsakaninsu musamman a shekara ta 2000 zuwa ta 2001 an samu rikicin addini a jahar kaduna a bisa dalilin sharia'ar Musulunci da musulmai sukai kokarin assasawa amma sai aka samu rashin jituwa da kiristoci wai suna tsammanin in har shari'ar musulunci ta kafu, to suma zai shafesu shi yasa suka ki amincewa a dalilin haka rikici ya balle inda aka samu asarar rayuka da dimbin dukiya mai tarin yawa, bayan haka akasa Mutane 1000 suka rasa rayukansu. Bayan haka an kara samun rikicin addini a shekarar 2002 amma a halin yanzu akwai zamantakewa mai karfi tsakanin addinan guda biyu.

Musulunci

File: sultan bello mosque by Anasskoko 03.jpg\masallacin da yamma

Ilimi

Ilimin Zamani

A fagen Ilmi kaduna ce cibiyar ilimi a arewacin Najeriya kaduna ce cibiyar makarantar horar da jami'an tsaro ta kasa wato Nigeria Defence Academy an kafaTa ne tun a shekarar 1964. Sai kuma babbar makarantar kimiyya da fasaha dake kaduna, wato Kaduna Polytechnic an kafa ta ne a shekarar 1968, sai kuma jami'ar Ahmadu Bello dake Zariya ita kuma ta kafu a shekarar 1962.Bayan haka akwai Jami'ar jahar Kaduna (kasu) da Nuhu bamalli polytechnic Zaria da college of education gidan waya da dai sauran manyan cibiyoyin ilimi. Lallai kaduna duniya ce ta ilmi wannan dalilin ne yasa kaduna tayi fice a jahohin Nigeria ta ko'ina ana barkowa daga sassa daban-daban na Najeriya ana wajajeu n neman ilimi a jahar ta kaduna domin ita jahar kaduna ta bambanta da sauran jahohin Arewacin Najeriya.

Jadawalin manyan makarantu

  • Jami'ar Jihar Kaduna
  • Kwalejin Horar da Manyan Jami'an Soja Nigerian Defence Academy' (NDA), Kaduna
  • Jami'ar Greenfield University Kaduna
  • Kwalejin share fagen shiga jami'a wato National Open University of Nigeria. Kaduna.
  • Air Force Institute of Technology, Kaduna
  • Kwalejin horar da malamai National Teachers Institute (NTI), Kaduna
  • Kwalejin unguwar-zoma School of Midwifery Kaduna
  • Kaduna Polytechnic (1968), Kaduna
  • Hukumar kula da ilimin addinin Musulunci da harshen Larabci
  • Kaduna Business School.

Ilimin Addini

A cikin jahar kaduna ana karantar da ilimin addini matuka, cibiyar addini na bangaren Izala, shi'a, Ɗariƙar Tijjaniya da salafiyya duka suna cikin garin jahar kaduna

Jiha Kaduna: Asalin suna, Tarihi, Kananan Hukumomi 
Wani masallacin juma'a na ginin al'ada a zaria kaduna
Jiha Kaduna: Asalin suna, Tarihi, Kananan Hukumomi 
ginin zamani na hedikwatar Jama'atul nasril Islam kaduna
Jiha Kaduna: Asalin suna, Tarihi, Kananan Hukumomi 
wani ginin hotal na zamani a kaduna

Wasanni

Akwai dandalin Murtala Mohammed Square inda ake wasanni da kuma motsa jiki, a ciki akwai Kaduna Polo Club da kuma Kaduna Golf Club kuma akwai sitadiyam mai suna Ahmadu Bello Stadiyam da Ranchers Bees Stadiyam

Sadarwa

Kafofin yada labarai (Talabijin)

  • Nigerian Television Authority Kaduna (NTA)
  • Kaduna State Media Corporation TV (KSTV)
  • Desmims Independent Television (DITV)
  • Liberty TV

Kafofin yada labarai (Gidan Rediyo)

A.M masu nisan zango sun hada da:

  • 639 MW – Kada 1 (KSMC)
  • 747 MW – Nagarta Radio
  • 594 MW – FRCN (Hausa), Kaduna
  • 1107 MW – FRCN (English), Kaduna

F.M masu matsakaicin zango sun hada da:

  • Brila FM
  • Kada 2 FM, Kaduna (KSMC)
  • Capital Sounds FM, Kaduna (KSMC)
  • Liberty Radio (English) Kaduna
  • Karama FM, Kaduna (FRCN)
  • Freedom Radio FM, Kaduna
  • Supreme FM, Kaduna (FRCN)
  • Alheri Radio FM, Kaduna
  • Invicta FM, Kaduna
  • Liberty Radio (Hausa) Kaduna
  • Ray Power FM Kaduna
  • Vision FM

Tattalin arziki

Kaduna cibiya ce ta masana'antun arewa, kamar masana'antar karafa, masaka,matatar man fetur ta ƙasa, ginin tukwane, Kaduna garine wanda ake kasuwanci kasancewar yawan mutane da kuma cunkosa, akwai kasuwanni dayawa a cikin garin kaduna,galibi ma kusan kowanne anguwa a cikin babban birnin kaduna tana da kasuwan ta.

Masana'antu

A cikin kaduna akwai babban kampanin matatan mai, me suna kaduna Refining and Petrochemical Company (KRPC),wanda daya ne daga cikin manyan kampanonin matatan mai da'ake dasu a Najeriya

Kasuwanni

Jahar tana da manyan kasuwanni kaman su kusuwan kasuwar sheikh Abubakar gumi,fanteka,kasuwar chechenia, kasuwan magani,kasuwar kawo, kasuwar bacci,kasuwan tudun wadan zaria.

Sufuri

Babbar hanyar data ratsa ta cikin gari ana kiranta Ahmadu Bello way. Kaduna tanada babbar kasuwa wadda aka gina tun a shekarun 1990s bayan ta fuskanci mahaukaciyar gobara. Acikin garin kaduna akwai hanyoyin jiragen kasa wadda ake sufuri daga kaduna zuwa wasu sassan Najeriya.

Jiragen kasa

Akwai hanyoyin layin dogo na jiragen kasa wadanda aka gina tun a watan satumba shekarar alif 2009 mai nisan tazarar kilomita 1,435 mm (4ft 81/2) zuwa babban birnin tarayya Abuja.

Jiragen sama

Jiha Kaduna: Asalin suna, Tarihi, Kananan Hukumomi 
Chanchangi Airlines na jihar kaduna

bayan haka akwai filayen jiragen sama guda biyu wato Filin Jirgin Saman Jihar kaduna da kuma filin jirgin sama na chanchangi wato Chanchangi Airlines wadda ake sufuri daga jahar zuwa jaha ko daga Nigeria zuwa kasashen ketare.

Sufurin motoci

Jahar kaduna tana da hukumar dake kula da tafiye-tafiye a fannoni sifirin motoci, wacce ak kira da KSTA.

.

Wuraren bude ido

  • Lugard Hall
  • Government Monument Bridge
  • General Hassan park
  • Man-made kaduna
  • Nok Terra Cotta
  • Nok Village
  • Cultural kaduna
  • National museum
  • Jakaranda pottery
  • kaduna souvenir

Hotuna

Sanannun mutane mazauna kaduna

  • Jiha Kaduna: Asalin suna, Tarihi, Kananan Hukumomi 
    Arc Muhammad Namadi Sambo. Tsohon Gwamnan jihar kaduna
    Mohammed Namadi Sambo
  • Shehu Sani tsohon sanata
  • Ahmed Mohammed Makarfi
  • Uba Sani sanata
  • Abubakar Gumi Malamin Addinin musulunci
  • Umar Farouk Abdulmutallab.
  • Tijani Babangida
  • Celestine Babayaro
  • Michael Eneramo
  • Fiona Fullerton
  • Dahiru Sadi, Dan wasan kwallo
  • Adam A Zango, jarumi a fina finan Hausa
  • General Mohammed Wushishi
  • sherhk Usman bauchi malamin addini
  • Col Sani Bello
  • Mal Muntaqa Usman Bilbis, malamin addinin musulunci
  • Hon Yusuf Hamisu Abubakar, mai rago

Manazarta


Jihohin Najeriya
Babban birnin tarayyar (Abuja) | Abiya | Adamawa | Akwa Ibom | Anambra | Bauchi | Bayelsa | Benue | Borno | Cross River | Delta | Ebonyi | Edo | Ekiti | Enugu | Gombe | Imo | Jigawa

Kaduna | Kano | Katsina | Kebbi | Kogi | Kwara | Lagos | Nasarawa | Neja | Ogun | Ondo | Osun | Oyo | Plateau | Rivers | Sokoto | Taraba | Yobe | Zamfara

Tags:

Jiha Kaduna Asalin sunaJiha Kaduna TarihiJiha Kaduna Kananan HukumomiJiha Kaduna MulkiJiha Kaduna KabiluJiha Kaduna AddinaiJiha Kaduna IlimiJiha Kaduna WasanniJiha Kaduna SadarwaJiha Kaduna Tattalin arzikiJiha Kaduna SufuriJiha Kaduna Wuraren bude idoJiha Kaduna HotunaJiha Kaduna Sanannun mutane mazauna kadunaJiha Kaduna ManazartaJiha KadunaArewacin NajeriyaJihar Katsina

🔥 Trending searches on Wiki Hausa / هَوُسَ:

Jerin Sarakunan KanoBet9jaGandun DajiTana AdelanaSani Umar Rijiyar LemoMouhamadou GningYaƙin gwalaloAhmadu BelloMuhammadAhmed MusaFezbukYakin HunaynKenyaYusuf (surah)KadaSaddam HusseinUmar Abdul'aziz fadar begeAnnabawaDagmawit Girmay BerhaneMr442Sadiya GyaleAuyoHussaini DankoNuhuAlioune Ndour (footballer)Saudi ArebiyaGashuaZinderMansur Ibrahim SokotoPharaohMalmoJinin HaidaIsaJabir Sani Mai-hulaTsarin DarasiMomee GombeSokotoPrincess Aisha MufeedahIdrissa MandiangAbdullah ɗan UmarSule LamidoFariKalmaIbrahim NiassTsakiyar AsiyaBayajiddaNasarawaJerin ƙasashen AfirkaBushiyaMaryam BabangidaUmar M ShareefAmal UmarImam Malik Ibn AnasDawaMasarautar KagaraIyabo OkoLeyti N'DiayeBBC HausaMikiyaAikin HajjiMarinette YetnaAppleTarayyar TuraiDaular SokotoHawan jiniDikko Umaru RaddaFika EmirateSana'oin mataShehu ShagariKatsina (birni)Muhammad AhmadJerin Ƙauyuka a Jihar KatsinaLarabawaBankin JaizHawainiyaMurja Ibrahim🡆 More