Abdulbaqi Aliyu Jari: ɗan jarida

Abdulbaqi Aliyu Jari (An haife shi a ranar 18 ga watan Agustan, shekara ta alif ɗari tara da casa'in da ɗaya 1991).

Akan rubuta shi da Abdulbaki Aliyu Jari kuma akan kira shi da Bahaushe, dan Najeriya ne, dan jarida, marubuci, mai fafutuka ne a kafar sada zumunta. Shi ne wanda ya kafa Ranar Hausa, ranar da aka ware domin bikin yaren Hausa. Shi ne kuma wanda ya kirkiro IHAME sabuwar alama ta rubuta harshen Hausa. Shi ne tsohon shugaban sashen Hausa na Naija News Media kuma tsohon mataimakin editan gidan talabijin na Nishadi.

Abdulbaqi Aliyu Jari: Farkon rayuwa da aiki, Ayyuka, Abubuwan sasantawa gwagwarmayar zamantakewa Abdulbaqi Aliyu Jari
Rayuwa
Haihuwa 18 ga Augusta, 1991 (32 shekaru)
Sana'a
Sana'a ɗan jarida da maiwaƙe
Abdulbaqi Aliyu Jari: Farkon rayuwa da aiki, Ayyuka, Abubuwan sasantawa gwagwarmayar zamantakewa
Abdulbaqi a ranar Hausa ta duniya
Abdulbaqi Aliyu Jari: Farkon rayuwa da aiki, Ayyuka, Abubuwan sasantawa gwagwarmayar zamantakewa
abdulbaqi maaikacin BBC
Abdulbaqi Aliyu Jari: Farkon rayuwa da aiki, Ayyuka, Abubuwan sasantawa gwagwarmayar zamantakewa
hoton abdulbaqi aliyu jari

Farkon rayuwa da aiki

Abdulbaqi an haife shi kuma ya girma a jihar Katsina, ya samu digiri na farko daga jami'ar Usman Danfodio Sakkwato a Biochemistry. Ya kuma sami difloma a Kimiyyar Computer da kuma Shari'a. Bayan kammala karatunsa daga Jami’ar Usman Danfodio, Abdulbaki ya fara aikinsa na dan Jarida mai zaman kansa, ya rubuta labarai sama da guda 1,000 wanda jaridu sama da guda 100 suka buga wadanda suka hada da Daily Trust, BBC Hausa, Legit.ng. Shi ne tsohon Shugaban sashen Hausa na Naij News kuma daga baya ya zama Mataimakin edita a gidan talabijin na Nishaɗi. Abdulbaqi a halin yanzu mai gabatar da bidiyo ne tare da BBC. Ya gudanar da bincike tare da African Eye na BBC inda ya kasance daga cikin wanda suka yi bincike a cikin shirin Tabay Torture Technique da Fake News.

Ayyuka

A shekarar 2011, Abdulbaqi ya kirkiri alamomin rubutun Hausa wadda ake kira Ihame. Ihame ya kunshi haruffan Hausa, adadi da kuma hanyar rubutu, ya yi shekara 3 yana bincike sannan ya kammala aikinsa. Tare da taimakon Farfesa Salisu Ahmad Yakasai, an buga Ihame a cikin mujallu 3. Yanzu haka ana inganta Ihame ga mutanen Hausa. A cikin 26 ga watan Agusta shekara ta 2015, Jari ya kafa Ranar Hausa ta duniya, ya fara gabatar da bikin farko a kafafen sada zumunta musamman ta shafin twitter da niyyar hada L1 da L2 na masu magana da harshen Hausa. Yayin bikin shekara 5, mutane fiye da 400,000 suka halarci duka ta yanar gizo kuma an gudanar da bikin a Faransa, Amurka, Kamaru, Ghana, Nijar, da Najeriya Saboda gudummawar da ya bayar ga Hausawa, marigayi Sarkin Rano ya ba shi Abdulbaqi lakabi na gargajiya na Sarkin Yakin Hausa. (Chief Publicist of Hausa) daga wajen sarkin Kano Emir of Rano.

Abubuwan sasantawa gwagwarmayar zamantakewa

A shekara ta 2014, Jari ya la'anci matakin da gwamnatin jahar Legas ta ɗauka na hana 'yan matan musulmai sanya Hijabi a makaranta. Jari yana cikin wadanda suka matsa lamba ga gwamnan jahar Katsina a cikin Shekara ta 2014 don sakin wani ɗalibi da aka tsare saboda wani shafin Facebook.

Wasu labarai da aka zaba da kuma binciken Abdulbaki Jari

  • Kisan Kenya da kuma aikin watsa labarai na duniya
  • Shugaba Janatan ya “yi tambayoyi”
  • Shugaban arewa ya dauki alhakin matsalolinmu
  • Dalilin da ya sa aure tsakanin mutanen Hausawa yakan gaza
  • Xenophobia da hadin kan Afirka
  • Ina tauraron mu guda hudu.

Manazarta

Hanyoyin haɗin waje

Tags:

Abdulbaqi Aliyu Jari Farkon rayuwa da aikiAbdulbaqi Aliyu Jari AyyukaAbdulbaqi Aliyu Jari Abubuwan sasantawa gwagwarmayar zamantakewaAbdulbaqi Aliyu Jari Wasu labarai da aka zaba da kuma binciken Abdulbaki JariAbdulbaqi Aliyu Jari ManazartaAbdulbaqi Aliyu Jari Hanyoyin haɗin wajeAbdulbaqi Aliyu JariHarshen HausaRanar HausaƊan NijeriyaƊan jarida

🔥 Trending searches on Wiki Hausa / هَوُسَ:

Yaƙin Larabawa-Isra'ila 1948IranTaken NajeriyaHafsat GandujeAl'adaƘur'aniyyaAfghanistanJerin ƙauyuka a Jihar GombeTuranciTauraron dan adamHannatu MusawaAlgajabbaMohammed Umar BagoLibyaBBC HausaYadda Ake Turaren Wuta Na MusammanMuhammad gibrimaUmar Ibn Al-KhattabCiwon Daji Na BakaAsiyaAbba el mustaphaKiristanciDahiru MohammedIbrahim ShemaCadiJerin shugabannin ƙasar NijarSam DarwishIbrahim Saminu TurakiSani AhmadKasar YarbawaBiyafaraBindigaJegoKate MolaleYakin Falasdinu na 1948FassaraBatsariThe emily man fimTY ShabanBornoKashiTek-x katsinaKannywoodGélita HoarauAbubakar RimiAduwaaGoribaZubayr ibn al-AwamKhalid ibn al-WalidTarihin IranShi'aKabir Garba MarafaHaruna Talle MaifataBayelsaArewa (Najeriya)Mutanen TangaleBauchi (birni)MikiyaAbdullahi AmdazAfirka ta YammaHarsunan NajeriyaAman Anand SinghKadangareDikko Umaru RaddaIbrahim DaboSoja🡆 More