Abdul Samad Isyaku Rabiu CFR CON (an haife shi a ranar 4 ga watan Agusta na shekara ta alif dari tara sittin 1960 a Kano, Nijeriya) dan kasuwa ne dan Nijeriya kuma mai taimakon al'umma.
Mahaifinsa shine marigayi Khalifah Sheikh Isyaka Rabi'u, yana daya daga cikin fitattun 'yan kasuwa a Najeriya a shekara ta alif dari tara da saba'in 1970 da 1980. Abdul Samad shi ne wanda ya kafa kuma yake shugabantar kamfanin BUA Group, wani kamfani na hadin gwiwa a Najeriya wanda ke mai da hankali kan masana'antu, kayayyakin more rayuwa da noma da samar da kudaden shiga da ya kai sama da dala biliyan 2.5, Kuma shi ne shugaban bankin masana’antu na Najeriya (BOI). A watan Janairun 2023, Abdul Samad Rabiu ya zama attajiri na 4 a Afirka.[1].
Abdul Samad Rabiu | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Kano, 4 ga Augusta, 1960 (63 shekaru) |
ƙasa | Najeriya |
Ƙabila | Hausawa |
Harshen uwa | Hausa |
Karatu | |
Makaranta | Capital University (en) |
Harsuna | Turanci Hausa Pidgin na Najeriya |
Sana'a | |
Sana'a | ɗan kasuwa |
Mahalarcin |
This article uses material from the Wikipedia Hausa / هَوُسَ article Abdul Samad Rabiu, which is released under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 3.0 license ("CC BY-SA 3.0"); additional terms may apply (view authors). An samar da dukkan muƙaloli a ƙarƙashin lasisin Creative Commons Attribution/Share-Alike; tana yiwuwa wasu ƙa'idoji su yi tasiri. Ku duba Ka'idojin Amfani na Gidauniyar Wiki domin ƙarin bayani. Images, videos and audio are available under their respective licenses.
®Wikipedia is a registered trademark of the Wiki Foundation, Inc. Wiki Hausa / هَوُسَ (DUHOCTRUNGQUOC.VN) is an independent company and has no affiliation with Wiki Foundation.