Ƙwayoyin Cuta Na Ebola

Ƙwayoyin cutar na Ebola (EVD) ko Cutar zazzaɓin jini ta Ebola (EHF) cuta ce ta ɗan adam wadda kwayoyin cuta na Ebola ke haifarwa.

Alamomin cutar kan fara bayyana daga kwanaki biyu zuwa mako uku daga kamuwa da ƙwayoyin cutar, wanda kan fara da zazzaɓi, zafin maƙogwaro, ciwon nama, da ciwon kai. Musamman tashin zuciya, amai, da gudawa kan biyo baya, tare da raguwar aikin hanta da ƙoda. A wannan matakin, wasu mutanen kan fuskanci matsalar zubar da jini.

Ƙwayoyin cuta na Ebola
Ƙwayoyin Cuta Na Ebola
Description (en) Fassara
Iri viral hemorrhagic fever (en) Fassara, Filoviridae infectious disease (en) Fassara, viral infectious disease (en) Fassara, hospital-acquired infection (en) Fassara
cuta
Specialty (en) Fassara infectious diseases (en) Fassara
Sanadi Orthoebolavirus (en) Fassara
Orthoebolavirus zairense (en) Fassara
Symptoms and signs (en) Fassara nausea (en) Fassara, amai, ciwon kai, gudawa, zazzaɓi, rash (en) Fassara, dyspnea (en) Fassara, arthralgia (en) Fassara, Conjunctivitis, bleeding (en) Fassara, Habo, internal bleeding (en) Fassara, myalgia (en) Fassara, Ciwon ciki
poisoning (en) Fassara
Effect (en) Fassara Western African Ebola virus epidemic (en) Fassara
Disease transmission process (en) Fassara contact transmission (en) Fassara
haemocontact transmission of pathogen (en) Fassara
Physical examination (en) Fassara physical examination (en) Fassara, complete blood count (en) Fassara, ELISEA (en) Fassara, viral culture (en) Fassara, polymerase chain reaction (en) Fassara, electron microscope (en) Fassara
immunofluorescence microscopy (en) Fassara
Suna saboda Kogin Ebola
Identifier (en) Fassara
ICD-10-CM A98.4
ICD-10 A98.4
ICD-9 065.8
DiseasesDB 18043
MedlinePlus 001339
eMedicine 001339
MeSH D019142
Disease Ontology ID DOID:4325
Ebola virus disease
Ebola virus disease
Ebola virus disease
Rabe-rabe da ma'adanai da waje
ICD/CIM-10A98.4 A98.4
ICD/CIM-9065.8 065.8
DiseasesDB18043
MedlinePlus001339
Ƙwayoyin Cuta Na Ebola
yadda kwayoyin cutar Ebola take

A kan sami cutar idan an haɗu da jini ko ruwan jiki na dabbar da ke ɗauke da cutar (musamman birrai ko jemagu). Babu wani rahoto da ya tabbatar da yaɗuwar cutar ta hanyar iska a wuraren zaman jama’a. An yi imani cewa jemagu kan ɗauki ƙwayar cutar kuma su yaɗata ba tare da su sun kamu ba. Da zarar ɗan adam ya kamu, to sauran jama’a na iya kamuwa. Maza waɗanda su ka warke daga cutar na iya yaɗata ta hanyar maniyyi har tsawon kusan wata biyu. Domin bayar da magani, a kan ware wasu cututtuka masu yanayi guda kamar zazzaɓi, kwalara da sauran cututtukan zazzaɓi da suka shafi jini. Domin tabbatar da maganin, ana gwada jini domin tabbatar da ƙwayoyin garkuwar jiki, RNA, ko ƙwayar cutar kanta.

Matakan kariya sun haɗa da hana yaɗuwar cutar daga birrai da aladai pigs da suka kamu da cutar zuwa ‘yan adam. Za’a iya haka ne ta duba dabbobin domin gano waɗanda suka kamu da kuma kashesu da binnesu idan an gano cutar. Dafa nama sosai da kuma saka kayayyakin kariya lokacin da ake sarrafa nama zai taimaka, kamar dai yadda saka kayan kariya da wanke hannu za su taimaka lokacin da aka kusanci mai ɗauke da cutar. Lallai a yi kaffa-kaffa wajen ta’ammali da ruwa ko yau da majina da suka fita daga masu ɗauke da cutar.

Babu wani magani na musamman ga cutar; amma za’a iya taimakawa mai ɗauke da cutar ta hanyar ɗura masa ruwan gishiri da sukari (ruwa mai gishiri-gishiri da sukari-sukari domin sha) ko ta hanyar ƙarin ruwa a jijiyar jini. Cutar na da saurin hallakarwa: wasu lokutan ta kan kashe tsakanin mutum 50% da 90% na waɗanda suka kamu da ƙwayoyin cutar. An fara gano ƙwayar cutar EVD a Sudan da Jamhuriyar Damukuraɗiyyar Kwango. An fi samun ɓarkewar cutar a yankuna masu zafi na kusa da Hamadar Afirka. Daga shekarar 1976 (lokacin da aka fara gano cutar) zuwa shekara ta 2013, ƙasa da mutane 1,000 ne suka kamu. Ɓarkewa mafi girma har zuwa yau ita ce wadda aka samu a halin yanzu Ɓarkewar Ebola a Yammacin Afirka na shakara ta 2014, wanda ya shafi Guinea, Sierra Leone, Laberiya da wata kila Najeriya. Har zuwa watan Agusta shekara ta 2014 an sami mutane 1600 waɗanda suka kamu. Ana nan ana ƙoƙarin gano allurar riga-kafin cutar; amma, yar yanzu babu..

.

.

Manazarta

Tags:

Ciwon kaiGudawaZazzaɓi

🔥 Trending searches on Wiki Hausa / هَوُسَ:

Hadarin Jirgin sama na KanoTijjani AsaseJerin kasashenAureAnnabawa a MusulunciCiwon daji na mahaifaZulu AdigweSahabbai MataMiyaFiqhun Gadon MusulunciMuharramBashir Aliyu UmarYaƙin Duniya na IITuranciTarihin Ƙasar IndiyaHadaddiyar Daular LarabawaUlul-azmiCiwon hantaBeljikCiwon daji na fataSiriyaKurciyaIbrahim MandawariIbn TaymiyyahMaganin gargajiyaMai Mala BuniMajalisar Ɗinkin DuniyaLalleƊan siyasaAhmad S NuhuShin ko ka san IlimiAl'aurar NamijiMasallacin AnnabiAttahiru BafarawaJerin ƙauyuka a jihar BauchiRomawa na DaSokotoJa'afar Mahmud AdamZainab BoothSallar Idi BabbaShehuAbdul Samad RabiuIbrahim ShekarauSallar NafilaDamisaCententennialSadiq Sani SadiqAlmaraFuntuaAdamAhmadu BelloAbubakar ImamSao Tome da PrinsipeUmar Abdul'aziz fadar begeYankin MaradiUmaru Musa Yar'aduaKasuwar DawanauKashiDubai (birni)Rakiya MusaAljeriyaKebbiKhulafa'hur-RashidunJamusShah Rukh KhanNigerian brailleBande, NijarArewacin NajeriyaSarauniya DauramaTattalin arziki🡆 More