Lalle

Lalle ko Lalli wanda aka fi sani a kasarmu ta Hausa da wata bishiya wadda mata suka fi yawan amfani da kuma ganyenta musamman don yin kwalliya a lokutan bukukuwan aure, sallah, suna, ko kuma haka nan.

A nan ba muna nufin lallen da ake yin zanen jiki na siffa ba ko dayin (dye), ina nufin lallen da muka sani na gargajiya da aka daina yin sa musamman a wannan lokacin ba. Ita dai bishiyar lalle tana da ganye launin kore da fure da kuma sayu, wadanda dukkanin su ana amfani da su a sarrafa a yi magani da su. Ana kuma yin shi lokacin sha'ani kamar biki, ko suna, musamman a kasar Hausa.

LalleLalle
material (en) Fassara
Lalle
Bayanai
Ƙaramin ɓangare na vegetable dye (en) Fassara
Amfani mehndi (en) Fassara
Time period (en) Fassara al-Andalus (en) Fassara
Natural product of taxon (en) Fassara Lawsonia inermis (en) Fassara
Lalle
lallen wata ƙasar
Lalle
ana Saida garin lalle
Lalle
Baqin lalle na Zane

Ado

Ganin yanda wasu suka ɗauki lalle tamkar kayan ado na mata kawai waɗanda ko su a yanzu sun daina yin lallen nan na gargajiya da na ke magana a kai, inda suka rungumi amfani da wannan da ake sayarwa a shaguna wato "dying" a harshen Turanci wanda wannan lallen haɗe-haɗe ne kawai na wasu sinadarai da har illatarwa suke yi. Kusan abin da ake kallon maccen da take yin lallen gargajiya tamkar Bakauyiya ce.

Amfani

Na farko dai darajar mata masu yin lalle ba ta daya da wadda ba ta yi ko a farin jinin su da tagomashin su ba zai zamo daya ba. Lalle kariya ce daga aljannu dalili a nan shi ne, akwai miyagun aljanun da suka tsani ganyen lalle. Lalle na karya sihiri a jikin mace, don haka, sai a nemi ciyawar aniya makomiya a daka shi tare da ganyen lalle a dingi shafawa. Lalle kariya ce daga cututtuka masu dama musamman na fata. Yin lalle a kafa na zuke cutar da ke a kafa, sannan yana tabbatarwa mace da irin ni’imar da ke gare ta. Maccen da take fama da "infection" kamar na kaikayin gaba ko makamantansu, sai ta tafasa lalle ta dunga zama a ruwan na tsawon sati biyu. In sha Allahu za ta rabu da shi. Sannan kuma GA macen data Bude dayawa itama zata kwaba lalle Da Dan kauri tayi matsi dashi Bayan munti talatin ta wanke Da ruwan Dimi Yana matse mace Kuma Yana Kara ni'ima.Ana iya shan ruwan ganyen lalle cokali daya da safe domin wankin dattin ciki amma mace mai juna biyu kada ta sha. Don gyaran fata, lalle ne a kan gaba wajen gyaran fata da matukar tasiri domin yana dauke da ‘natural toner’ wanda ba bilicin yake yi ba, amma yana da sinadiran da ke canza launin fatar ta zamo abin sha’awa kuma yana goge dattin fata. A bangaren gyaran fuska, lalle ya zarce sauran kayan kolliya domin duk yanda kike amfani da foda a fuskarki, to ba za ta kai lalle tasiri ba domin shi lalle har sha’awa yake karawa mace, haka kuma yana janyo hankalin namiji yaji yana sha’awar matarsa muddin tana yawan yin lalle. Ga macce mai warin kashi sai ta nemi lalle ta kwaba da turaren da tafi bukata sai dai a kula wani tirare ya kan janyo iska a jiki musamman idan aka gauraya shi da lalle, kamar zakyash da zafran, dan haka a san irin tiraren da za'a gauraya da lalle.

Yin lalli

To, a zuba isasshen ruwa a bokiti, sai ki sa garin lalle a ciki, sai ya jika ya yi ja jir, sai ki tsiyaye ruwan, ki diga turaren ki mai kamshi a ciki, bayan kin yi wanka da sabulunki, sai ki dauraye jikinki da shi, idan kin nace da haka to ba ke ba warin kashi ba, insha Allah. Haka kuma mazan da ke fama da matsala irin wannan su ma za su jarraba. Ta bangaren magani kuma, lalle ya kasance mai maganin cututtuka kamar haka: Lalle yana maganin ciwon yatsa da muke kira dan kankare. Lalle na maganin cututtukan da ke lailayi a baki kamar zubar jini a sanda ake kurkurar baki ko kuraje ga harshe ko a cikin baki na ba gaira ba dalili. Sai a tafasa ganyen lalle a dunga kurkure baki da ruwan a kalla sau uku a wuni. Ganyen lalle na maganin ciwon huhu kamar tarin asma, tarin t.b da tarin lamoniya da wasu cututtukan huhu na daban. Sai a tafasa ganyen a tarfa zuma gangariya a sha. Lalle na maganin cin ruwa na yatsu idan aka kwaba garin da ruwan kal aka dinga shafawa. Lalle na maganin hauhawar jini da bugun zuciya. Sai a tafasa a tarfa zam-zam da zuma a dunga sha. Macen da take da ni’ima ma’ana wadda Allah ya san ya wa yawan sha’awa a jiki da kuma damshin jiki da gamsarwa, idan tana yin lalle to sha’awar da ni’imarta ba za su gushe ba har sai sanda tsufa ya kai wani mataki.

Managarta

Tags:

Lalle AmfaniLalle Yin lalliLalle ManagartaLalle

🔥 Trending searches on Wiki Hausa / هَوُسَ:

Umar Abdul'aziz fadar begeTarihin HausawaEros YanzuSahabbai MataPortugalWasan ShaɗiFilin jirgin saman DubaiHauwa MainaTufafiRashaUlul-azmiAnne-Marie PayetDubai (birni)Tarihin Gabas Ta TsakiyaItofiyaMasallacin AnnabiBauchi (birni)Hannatu BashirIbn TaymiyyahAhmad S NuhuGani FawehinmiQatarSana'o'in Hausawa na gargajiyaRonaldo (Brazil)Yunss AkinochoBobriskyBabba da jakaMuhammadu DikkoPharaohTsarin DarasiDawaBilkisuAbdullahi AmdazFarida JalalGabonHauwa'uFezbukKoriya ta ArewaKhalid BukichouSadi Sidi SharifaiRabi'u Musa KwankwasoTarihin NajeriyaShams al-Ma'arifIlimiISa AyagiJalingoNitish GulyaniAll Progressives CongressBashir Aliyu UmarMansura IsaGanuwaZubayr ibn al-AwamDuniyaAl'ummar WikipediaJihar RiversSanusi Ado BayeroRagoGoroYakubu GowonTarayyar AmurkaMaryam Abdullahi BalaWikimaniaMudasir ZafarMa'anar Aure🡆 More