Jihar Neja Jaha ce dake Arewa ta tsakiyar Najeriya.
Tana da yawan fili kimanin kilomita dubu saba'in da shida da ɗari uku da sittin da uku (76,363 ), da yawan jama’a kimanin miliyan uku da dubu ɗari tara da hamsin da huɗu da ɗari bakwai da saba'in da biyu, ƙidayar yawan jama'a na shekara ta (2006).Babban birnin jahar shine Minna.
Neja | |||||
---|---|---|---|---|---|
Niger (en) | |||||
| |||||
| |||||
Suna saboda | Nijar | ||||
Wuri | |||||
| |||||
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya | ||||
Babban birni | Minna | ||||
Yawan mutane | |||||
Faɗi | 5,556,247 (2016) | ||||
• Yawan mutane | 72.76 mazaunan/km² | ||||
Harshen gwamnati | Turanci | ||||
Labarin ƙasa | |||||
Yawan fili | 76,363 km² | ||||
Sun raba iyaka da | |||||
Bayanan tarihi | |||||
Mabiyi | Arewa maso yammacin jiha | ||||
Ƙirƙira | 3 ga Faburairu, 1976 | ||||
Tsarin Siyasa | |||||
Majalisar zartarwa | executive council of Niger State (en) | ||||
Gangar majalisa | Niger State House of Assembly (en) | ||||
Bayanan Tuntuɓa | |||||
Kasancewa a yanki na lokaci | |||||
Lamba ta ISO 3166-2 | NG-NI | ||||
Wasu abun | |||||
| |||||
Yanar gizo | nigerstate.gov.ng |
Jihar Neja na cikin jihohi 36 na Najeriya Takenta shi ne '"Power State"' saboda tana da madatsun ruwa guda uku (3) da ke samar da kusan kashi 70% na wutar lantarkin Najeriya.
An kafa jihar Neja ne a ranar 3 ga watan Fabrairun 1976 daga rusasshiyar jihar Arewa maso Yamma a zamanin mulkin Janar Murtala Mohammed.
Jihar tana a shiyyar arewa ta tsakiya mai yanki mafi girma wanda ya kai kusan 80000km2, tare da kusan kashi 70% na gonaki da noma. Jihar Neja tana iyaka da Jihar Zamfara ta ɓangaren Arewa, Yamma da Jihar Kebbi, Kudu da Jihar Kogi, Kudu maso Yamma da Jihar Kwara, Arewa maso Gabas da Jihar Kaduna da kuma Kudu maso Gabas da Abuja. Haka kuma jihar tana da iyaka ta ƙasa da ƙasa da jamhuriyar Benin tare da ƙananan hukumomin Agwara da Borgu zuwa Arewa maso Yamma.
Jahar ta Neja tana da manyan mutane da dama waɗanda suka riƙe manyan muƙamai a ƙasar Najeriya sannan jiha ce wacce ta ke da tsofaffin shugabannin ƙasa na Najeriya har guda biyu a lokacin mulkin soja, wato Ibrahim Badamasi Babangida (IBB) mai ritaya da kuma Abdusalami Abubakar mai ritaya dukkaninsu mutanan Jahar ta Neja ne.
Manyan ƙananan hukumomin Jahar su ne kamar haka: Chanchaga, Bosso da kuma ƙananan hukumomin Bidda, Suleja da kuma Kontagora.
Manyan yarukan jihar sun haɗa ne da Nufanchi, Hausa, Gbagi da kuma turanci inda yankunan Bidda da Agaie da kuma Lapai, Mokwa suka fi yawan masu amfani da yaren Nufanci, Yankin Kontagora, Kagara, Mariga, Mashegu Rijau, Suleja suke da mafi rinjayen masu amfani da yarukan Hausa. Paikoro, Chanchaga, Bosso, Edati da dai sauransu suna amfani da saura yarukan a matsayin masu rinjaye.
Akwai wuraren tarihi sosai a jahar ta Neja musamman a garin Zungeru inda kuma a nan ne turawan Yamma suka saka hannu domin haɗewan Najeriya ƙasa ɗaya daga sauran yankuna sannan a wannan garin ne gwamnan farko na Najeriya ya yada zango a matsayin hedikwata gareshi.
Alhaji Umar Farouk Bahago shi ne sarkin Minna.
Jihar Neja tana da iyaka da misalin jahohi shida, sune: Babban birnin tarayya, Kwara, Kogi, Kaduna(jiha)|Kaduna]], Kebbi kuma da Zamfara.
Jerin sunayen Gwamnonin jihar Neja. https://en.m.wikipedia.org/wiki/List_of_governors_of_Niger_State
Jihar Neja tana da Ƙananan Hukumomi guda ashirin da biyar (25). Sune:
Jihar Neja na da manyan jami'oi na ilimi waɗanda suka haɗa da:
An jero yarukan jihar Neja dangane da ƙananan hukumomin da ake amfani da su;
LGA | Languages |
---|---|
Agaie | Nupe, Dibo; Kakanda; |
Agwara | Cishingini |
Bida | Nupe, BassaNge, Gbari |
Borgu | Busa, Bisã; Boko; Cishingini; Laru; Reshe |
Chanchaga | Basa-Gumna; Bassa-Gurmana; Gbagyi; Gbari; Nupe; Kamuku; Tanjijili |
Edati | Nupe, BassaNge |
Gbako | Nupe |
Gurara | Gwandara, Gbagyi |
Katcha | Nupe, Dibo; Kupa |
Kontagora | Acipa, Eastern; Asu; Tsishingini; Tsuvadi |
Lapai | Nupe, Dibo; Gbari; Gupa-Abawa; Kakanda; Kami; |
Magama | Lopa; Tsikimba; Tsishingini; Tsuvadi |
Mariga | Baangi; Bassa-Kontagora; Cicipu; Kamuku; Nupe; Rogo; Shama-Sambuga; Tsikimba; Tsishingini; Tsuvadi |
Mashegu | Asu; Tsikimba; Tsishingini; Nupe-Tako |
Minna | Nupe; Gbari; Gbagyi |
Mokwa | Nupe, Yoruba; Gbari |
Munya | Adara |
Paikoro | Gbari; Kadara |
Rafi | Basa-Gurmana; Bauchi; Cahungwarya; Fungwa; Gbagyi; Gbari; Kamuku; Pangu; Rogo; Shama-Sambuga |
Rijau | Fulani; C'Lela; Tsishingini; Tsuvadi; ut-Hun |
Shiroro | Gbagyi; Gurmana; Bassa |
Suleja | Gbagyi; Gbari; Gwandara; Nupe; Tanjijili |
Wushishi | Hausa; Nupe; Gbari |
Jihohin Najeriya |
Babban birnin tarayyar (Abuja) | Abiya | Adamawa | Akwa Ibom | Anambra | Bauchi | Bayelsa | Benue | Borno | Cross River | Delta | Ebonyi | Edo | Ekiti | Enugu | Gombe | Imo | Jigawa Kaduna | Kano | Katsina | Kebbi | Kogi | Kwara | Lagos | Nasarawa | Neja | Ogun | Ondo | Osun | Oyo | Plateau | Rivers | Sokoto | Taraba | Yobe | Zamfara |
This article uses material from the Wikipedia Hausa / هَوُسَ article Neja, which is released under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 3.0 license ("CC BY-SA 3.0"); additional terms may apply (view authors). An samar da dukkan muƙaloli a ƙarƙashin lasisin Creative Commons Attribution/Share-Alike; tana yiwuwa wasu ƙa'idoji su yi tasiri. Ku duba Ka'idojin Amfani na Gidauniyar Wiki domin ƙarin bayani. Images, videos and audio are available under their respective licenses.
®Wikipedia is a registered trademark of the Wiki Foundation, Inc. Wiki Hausa / هَوُسَ (DUHOCTRUNGQUOC.VN) is an independent company and has no affiliation with Wiki Foundation.