Majalisar dokokin jihar Neja ita ce bangaren da ke tsara dokokin gwamnatin jihar Neja ta Najeriya.
Majalisar dokoki ce mai mambobi guda 27 da aka zaba daga kananan hukumomi guda 25 na jihar.An kayyade kananan hukumomin da ke da yawan mabukata a mazabu biyu don ba da wakilci dai-dai. Wannan ya sanya yawan 'yan majalisar a majalisar dokokin jihar Neja sunkai guda 27.
Majalisar Dokokin Jihar Neja | |
---|---|
unicameral legislature (en) | |
Bayanai | |
Ƙasa | Najeriya |
Applies to jurisdiction (en) | Jihar Neja |
Ayyukan yau da kullun na Majalisar sune ƙirƙirar sabbin dokoki, gyara ko soke dokokin da ke akwai da kuma kula da zartarwa. An zabi membobin majalisar na tsawon shekaru hudu tare da 'yan majalisar tarayya (majalisar dattijai da ta wakilai). Majalisar jihar tana yin taro sau uku a mako (Talata, Laraba da Alhamis) don yin cikakken zama a harabar majalisar a cikin babban birnin jihar, Minna . Ana gudanar da kwamitoci da ayyukan kulawa kamar yadda membobin suka yanke.
Honarabul Abdullahi Wuse da Bako Kassim Alfa a matsayin kakakin majalisa da mataimakin kakakin majalisar. Bako Kasim wanda aka zaba tare da kakakin majalisar a ranar daya ya sauka daga matsayinsa na mataimakin kakakin majalisar tare da wani dalili da ba a bayyana ba, sannan an zabi Jibrin Baba na mazabar Lavun a matsayin mataimakin kakakin majalisar.
This article uses material from the Wikipedia Hausa / هَوُسَ article Majalisar Dokokin Jihar Neja, which is released under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 3.0 license ("CC BY-SA 3.0"); additional terms may apply (view authors). An samar da dukkan muƙaloli a ƙarƙashin lasisin Creative Commons Attribution/Share-Alike; tana yiwuwa wasu ƙa'idoji su yi tasiri. Ku duba Ka'idojin Amfani na Gidauniyar Wiki domin ƙarin bayani. Images, videos and audio are available under their respective licenses.
®Wikipedia is a registered trademark of the Wiki Foundation, Inc. Wiki Hausa / هَوُسَ (DUHOCTRUNGQUOC.VN) is an independent company and has no affiliation with Wiki Foundation.