An haifi Bala Mohammed ne a farkon Watan Oktoban shekarar ta alif dari tara da hamsin da takwas, 1958) Miladiyya.(A.c) Bala Mohammed yayi karatu ne a gida har ya samu Digiri a harshen Turanci a Jami’ar Maiduguri a shekarar 1982, Bala Mohammed ya soma aiki ne a matsayin mai kawowa gidan jaridar nan ta The Democrat rahoto a shekarar 1983 Bio bayan ya kammala karatu.
Daga nan kuma Mohammed ya koma aikin gwamnati har zuwa shekarar 2000, Bala Mohammed yayi aiki a ma’aikatu daban-daban wanda su ka hada da Ma’aikatar ma’adanai da ta harkokin cikin gida, da Ma’aikatar harkokin jirgin sama. A ƙarshe dai yayi ritaya a matsayin Darekta a Nigerian Meteorological Agency. Bala Mohammed ya shiga siyasa ne bayan yayi ritaya inda yayi takara, ya kuma ci kujerar Sanatan Bauchi ta Kudu a shekarar 2007. Sanatan na ANPP ya samu matsala da tsohon Mai gidan sa watau Gwamna Isa Yuguda wanda ya koma PDP a mulkin Yar'adua. Labarai LABARAI Takaitaccen tarihin Mai Girma Gwamnan Jihar Bauchi mai jiran-gado Talata, Maris 26, 2019 at 7:04 Safiya by Muhammad Malumfashi A jiya ne hukumar zabe na INEC ta sanar da cewa Sanata Bala Mohammed ne ya lashe zaben gwamna da aka yi a jihar Bauchi inda ya doke gwamna mai-ci. Mun kawo kadan daga tarihin Kauran Bauchi News.
Bala Mohammed | |||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
29 Mayu 2019 - ← Mohammed Abdullahi Abubakar
11 ga Yuli, 2011 - 29 Mayu 2015 - Mohammed Musa Bello → District: Bauchi South
8 ga Afirilu, 2010 - 11 ga Yuli, 2011 ← Adamu Aliero
8 ga Afirilu, 2007 - 8 ga Afirilu, 2010 | |||||||||
Rayuwa | |||||||||
Cikakken suna | Bala Mohammed | ||||||||
Haihuwa | Alkaleri, 5 Oktoba 1958 (65 shekaru) | ||||||||
ƙasa | Najeriya | ||||||||
Ƙabila | Hausawa | ||||||||
Harshen uwa | Hausa | ||||||||
Karatu | |||||||||
Makaranta | Jami'ar Maiduguri | ||||||||
Harsuna | Turanci Hausa Pidgin na Najeriya | ||||||||
Sana'a | |||||||||
Sana'a | ɗan siyasa | ||||||||
Mahalarcin | |||||||||
Imani | |||||||||
Jam'iyar siyasa | Peoples Democratic Party |
Nijeriya .
This article uses material from the Wikipedia Hausa / هَوُسَ article Bala Mohammed, which is released under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 3.0 license ("CC BY-SA 3.0"); additional terms may apply (view authors). An samar da dukkan muƙaloli a ƙarƙashin lasisin Creative Commons Attribution/Share-Alike; tana yiwuwa wasu ƙa'idoji su yi tasiri. Ku duba Ka'idojin Amfani na Gidauniyar Wiki domin ƙarin bayani. Images, videos and audio are available under their respective licenses.
®Wikipedia is a registered trademark of the Wiki Foundation, Inc. Wiki Hausa / هَوُسَ (DUHOCTRUNGQUOC.VN) is an independent company and has no affiliation with Wiki Foundation.