An haifi Jika Dauda Halliru a shekara ta alif ɗari tara da saba'in da shida 1976 a jihar Bauchi, Nigeria.
Dan kasuwa ne kuma dan siyasa. Ya taba zama kakakin majalisar dokokin jihar Bauchi kuma a yanzu haka dan majalisar dattawa ne mai wakiltar Bauchi ta tsakiya. An fi saninsa da Dokagi.
Jika Dauda Halliru | |||||
---|---|---|---|---|---|
11 ga Yuni, 2019 - District: Bauchi Central
9 ga Yuni, 2015 - 9 ga Yuni, 2019 District: Bauchi Central | |||||
Rayuwa | |||||
Cikakken suna | Jika Dauda Haliru | ||||
Haihuwa | 1976 (47/48 shekaru) | ||||
ƙasa | Najeriya | ||||
Karatu | |||||
Makaranta | Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Kaduna | ||||
Harsuna | Turanci Pidgin na Najeriya | ||||
Sana'a | |||||
Sana'a | ɗan siyasa | ||||
Imani | |||||
Jam'iyar siyasa | All Progressives Congress |
Ya tafi Kwalejin Tunawa da Sardauna da ke Kaduna, Jihar Kaduna ya kammala a shekara ta alif ɗari tara da casa'in da tara 1999. Daga nan ya koma Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Kaduna domin yin karatun Injiniya, kuma ya kammala a shekara ta 2003.
An zabi Jika a matsayin wakilin mazabar Darazo da Ganjuwa a majalisar wakilai ta tarayya kuma ya yi zango biyu a matsayin wakili, na farko tsakanin shekara ta 2007 da shekara ta 2011 da kuma na biyu tsakanin shekara ta 2011 da shekara ta 2015. Sannan a zaben shekara ta 2019 an zabe shi sanata bauchi ta tsakiya karkashin tutar APC.
Jika musulmi ne. Yayi aure da yara.
This article uses material from the Wikipedia Hausa / هَوُسَ article Jika Dauda Halliru, which is released under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 3.0 license ("CC BY-SA 3.0"); additional terms may apply (view authors). An samar da dukkan muƙaloli a ƙarƙashin lasisin Creative Commons Attribution/Share-Alike; tana yiwuwa wasu ƙa'idoji su yi tasiri. Ku duba Ka'idojin Amfani na Gidauniyar Wiki domin ƙarin bayani. Images, videos and audio are available under their respective licenses.
®Wikipedia is a registered trademark of the Wiki Foundation, Inc. Wiki Hausa / هَوُسَ (DUHOCTRUNGQUOC.VN) is an independent company and has no affiliation with Wiki Foundation.