Peoples Democratic Party: Jamiyyar siyasa a Nigeria

Peoples Democratic Party PDP jam'iyyar siyasa ce dake ƙasar Najeriya.

PDP Itace babbar jam'iyyar adawa a Najeriya wadda ta mulki ƙasar na tsawon shekaru goma sha shida tun daga shekara ta dubu ɗaya da Ɗari Tara da casa'in da Tara 1999 zuwa shekara ta dubu biyu da Sha biyar 2015.

Peoples Democratic Party: Jamiyyar siyasa a NigeriaPeoples Democratic Party
Bayanai
Gajeren suna PDP
Iri jam'iyyar siyasa
Ƙasa Najeriya
Ideology (en) Fassara economic liberalism (en) Fassara da social conservatism (en) Fassara
Political alignment (en) Fassara centre-right (en) Fassara
Mulki
Shugaba Uche Secondus (en) Fassara
Hedkwata Abuja
Tarihi
Ƙirƙira 1998

peoplesdemocraticparty.net


Peoples Democratic Party: Jamiyyar siyasa a Nigeria
Peoples Democratic Party: Jamiyyar siyasa a Nigeria
Magoya bayan Jam'iyyar PDP

Tarihi

A shekara ta dubu ɗaya da Ɗari Tara da casa'in da takwas(1998), jam'iyyar PDP ta gudanar da zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa na farko da aka gudanar a Jos, jihar Filato, yankin Arewa ta Tsakiyar Najeriya. Sun tsayar da tsohon shugaban mulkin soja, Olusegun Obasanjo wanda aka saki daga tsare shi a matsayin fursunan siyasa a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen watan Fabrairu shekarata dubu daya da Dari Tara da casa'in da Tara (1999). Atiku Abubakar (Zaɓaɓɓen gwamnan Jihar Adamawa kuma tsohon jigo a jam’iyyar Social Democratic Party) shi ne aka saka a matsayin abokin takarar. Sun ci zaɓen shugaban ƙasa kuma an ƙaddamar da su a ranar 29 ga watan Mayu shekarata 1999.

Obasanjo da Atiku sun sake lashe zaɓen shugaban ƙasa a karo na biyu a shekarata dubu biyu da uku (2003) a ƙarƙashin Jam'iyar ta PDP.

Bayan kammala zangon su a shekarata dubu biyu da bakwai (2007), Umaru Musa Yar'adua ya sake lashe zaɓen shugaban ƙasar Najeriya a ƙarƙashin jam'iyar PDP shi da mataimakin sa Goodluck Jonathan.

Haka nan kuma jam'iyyar ta PDP ta sake yin nasara a zaɓen da aka gudanar a shekarata dubu biyu da Sha daya 2011 inda shugaba Goodluck Jonathan ya samu nasara tare da mataimakin sa Namadi Sambo.

Jam'iyyar PDP ta rasa shugabancin Najeriya ne a lokacin da tayi rashin nasara a zaɓen shekarata dubu biyu da Sha biyar (2015) hannun jam'iyyar All Progressive Congress wadda shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi ma takara da mataimakin sa Yemi Osinbajo. Lamarin da ya kawo ƙarshen mulkin jam'iyyar PDP na tsawon shekaru goma Sha shida a Najeriya.

Manazarta

Tags:

Najeriya

🔥 Trending searches on Wiki Hausa / هَوُسَ:

AbujaHausa–FulaniBobriskyMaitatsineSanskritNational Orthopaedic Hospital, EnuguAminu S BonoKulawar haihuwaJamusMomee Gombe2006TwitterTarayyar SobiyetIbrahim MandawariAfirkaBidiyoTarihin DauraMuhammadu BelloCiwon Daji na Kai da WuyaWikibooksBeninYaren KyrgyzstanBenue (jiha)Al-Nasa'iAbubakar ImamOdumejeAstanaCententennialRanan SallaAntatikaKafancanAdam A ZangoTsibirin BamudaHafsat GandujeNajeriyaBirtaniyaAsturaliyaJegoAkuSaray KhumaloAlakszandiraGaiwaBilkisu AbdullahiMaleshiyaAdaora OnyechereIbrahim NiassHarsunan NajeriyaJerin shugabannin ƙasar NijeriyaMalam MadoriUmmu SalamaFati NijarTarihiBauchi (jiha)Maryam Jibrin GidadoPriyanka ChopraIndonesiyaFaransaBoum AlexisShin ko ka san Al'aduTarihin Ƙasar JapanYolaKhadija MainumfashiSokoto (birni)Musulunci AlkahiraJordanSir Yahaya Memorial HospitalMustapha MustyIsyaka Rabi'uHamisu BreakerTalo-taloFatima Ibrahim ShemaBalbelaChina Radio International🡆 More