Ibrahim Ahmad Maqari: Limamin Masallacin Abuja

Ibrahim Ahmad Maqari an haifeshi a ranar 15 ga watan Satumba, shekarar 1976, a birnin Zariya, da ke jihar Kaduna, Najeriya.

Farfesa Maqari malamin Addinin Musulunci ne a Najeriya dama wajen Najeriya kuma masanin lugah (larabci) yana kuma tafsirin Alqur'ani mai girma a watan Ramadan kuma limamin Masallacin ƙasa na Abuja a Najeriya.

Ibrahim Ahmad Maqari: Rayuwar Farko, Ilimi, Limanci Ibrahim Ahmad Maqari
Rayuwa
Haihuwa 15 Satumba 1976 (47 shekaru)
Sana'a

Rayuwar Farko

An haifi Farfesa Ibrahim Maqari a Zariya, mahaifinsa ma'aikacin gwamnati ne kuma malami. Kakansa dan asalin jihar Borno ne yazo garin Zariya ne don neman Ilimi bayan ya sami abinda ya samu na ilimin addinin Musulunci da Fiqh, sai ya yanke shawarar komawa gida don ci gaba da koyarwa a garinsu Borno, sai dai Sarkin Zazzau na wancan ƙarnin yaƙi yarda ya bar garin Zariya, har Sarkin yake cewa "Malamai basa zuwa garin shi su bar garin" sai sarki ya ba shi gida ya zauna a kusa da Masarautar Zazzau.

Ilimi

Farfesa Ibrahim Maqari ya fara karatun firamare ne a Jihar Katsina a shekarar 1987. Sheikh Ibrahim Maqari ya haddace Alqur'ani mai girma yana ɗan shekara 13-14 a Madarasatul Faidatul Islamiyya ta gidan Sheikh Yahuza Zariya. Daga nan sai ya tafi Kwalejin Nazarin Larabci ta Jama’atu da ke Zariya, Kaduna don yin karatun sakandire. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Al-Azhar da ke birnin Alkahira a shekarar 1999. Ya kuma yi digiri na biyu a Jami'ar Ahmadu Bello a shekarar 2005. Daga nan kuma ya tafi Jami'ar Bayero Kano don samun digirin digirgir a shekarar 2009, inda ya samu digiri na biyu a cikin shekaru biyu. A shekarar 1999, ya fara koyarwa a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya. Ya zama babban malami a Jami'ar Jihar Kaduna a shekarar 2010. Bayan ya shafe kusan shekara ɗaya yana koyarwa, Farfesa Ibrahim Maqari ya koma Jami’ar Bayero Kano inda yayi karatun Farfesanci a sashen Larabci da Harsuna, inda ya yi ritaya da kansa a shekarar 2020. Malam ya yi karatu gwargwado a gidan shahararren malami a garin Katsina Sheikh Abba Abu. Sheikh Ibrahim Maqari ya ɗauki karatu daga malamai da dama a cikin garin Zariya, a cikinsu akwai malam Tanimu Kusfa, shahararren malamin fiqihu da sauran fannonin ilimi. Sannan akwai Malam Bala Kusfa wanda ƙanin Mahaifinsa yake ɗaukan sa suna zuwa tare. Sheikh Ibrahim Ahmad Maqari yayi karatu a ƙasar Masar inda a Chan ne ya haɗu da Sheik Muhammadu Amin Abdullahi mutumin Okene.

Littattafan da ya rubuta

Malam Ibrahim Maqari ya rubuta littafai da dama wanda adadinsu ya kai kusan 40 ga kaɗan daga cikin su:

  • New Generation 3
  • Azzahirat Alsalafiyyat
  • Shi'iri Hubbul Ilaahy
  • A'alamus shi'eril muusahah
  • Alhawaa wabina'is Suratu shi'ri Yahya Annufaahki
  • Attanaasu Bai Al Limtisasi wal'Intisasi.

Limanci

Farfesa Ibrahim Ahmad Maqari Shine Limamin Masallacin Ƙasa da ƙasa dake Abuja babban birnin tarayyar Najeriya.

Manazarta

Tags:

Ibrahim Ahmad Maqari Rayuwar FarkoIbrahim Ahmad Maqari IlimiIbrahim Ahmad Maqari LimanciIbrahim Ahmad Maqari ManazartaIbrahim Ahmad MaqariAddinin MusulunciAlqur'ani mai girmaJihar KadunaMasallacin tarayyar NajeriyaNajeriyaRamadanZariya

🔥 Trending searches on Wiki Hausa / هَوُسَ:

Gaɓoɓin FuruciDokar NajeriyaTasheBabagana Umara ZulumIbrahim Ahmad MaqariShehu Musa Yar'AduaNasir Yusuf GawunaGandun DajiHamisu Breaker2024Jerin gidajen rediyo a NajeriyaGobirMaryam BabangidaTurkiyyaJerin AddinaiSokoto (birni)ZariyaYaƙin gwalaloKanjamauSallar NafilaBola TinubuAdo GwanjaLilin BabaVladimir PutinFika EmirateWikipidiyaKhadija MainumfashiAbdourahmane Ndiaye (mai wasan ƙwallon ƙafa)Annabi IsahIbrahim NiassAmfanin Man HabbatussaudaYakin HunaynKatsinaBabban Birnin Tarayya, NajeriyaMurtala MohammedMaiduguriMasallacin AnnabiLeyti N'DiayeMalam MadoriIslamiyat YusufPidgin na NajeriyaMadagaskarTekuDawaBalaraba MuhammadIsaBarkwanciMacijiKatsina (jiha)TatsuniyaPorsche TaycanSahabbai MataBajogaLittafiJerusalemFarillai, Sunnoni da Mustahabban AlwallaMansura IsahAnnabawa a MusulunciFariAminu Waziri TambuwalSanusi Lamido SanusiBushiyaShehu ShagariUsman NdongMasarautar KanoBilkisu ShemaAishwarya RaiTarayyar TuraiFassaraBahar RumKanunfariTsarin DarasiNepal🡆 More