Garba Ja Abdulqadir

Garba Ja Abdulqadir (An haife shi a shekarar 1933) a Katsina, Najeriya, ya riƙe muhimman mukamai da dama wanda suka hada da babban commisionan zabe na arewa.

Minista Sakatare na noma a watan Augustan shekarar 1993. Gwmanatin Tarayya ta bashi lambar yabo na Sarkin Sudan, sannan ya samu digir na digirgir daga jami’ar Usman Danfodiyo, kuma shine shugaban Jami’ar Lagos. Shi ne chiyaman na kamfanin John Holt Group da kuma sauran kamfanoni guda shida.Akwai unguwa mai zaman kanta (Garba Ja Abdulkadir Crescent) da aka sanya sunan a maimakonsa.

Kuruciya da Ilimi

An haife Garba a 1933 kuma ya fara karatunsa daga 1944 zuwa 1947, daga bisani kuma a Govenrment College da ke Kaduna a tsakanin 1947-1950,sai kuma jami’ar Ibadan daga 1956 zuwa 1959 inda ya kammala karatunsa a fannin tarihi watau (BA History).

Aiki

Garba ya fara aiki a matsayin malami sannan daga baya ya koma Gwamnatin Yankin Arewacin Najeriya a matsayin mai gudanarwa. Ya zamo jami’in yanki (Divisional Officer) a Hadeja daga 1959 zuwa 1960, daga 1959 zuwa 1962 yana aiki da firimiya na Arewacin Najeriya a kaduna, sannan daga baya anyi mai canjin aiki zuwa ofishin Gwamna a matsayin sakatare na kusa a tsakanin 1961 zuwa 1962. Garba ya zamo mai gudanarwa na yankin babban birnin Kaduna 1965, sannan kuma ya zamo sakataren gundumar Plateau daga 1967 zuwa 1975.

A lokacin da aka kafa jihohi a Najeriya, Garba ya zamo sakatare na farko na gwamnatin mulkin soja na gwamnatin arewa ta tsakiya, daga bisani kuma yankin gundumar Kasuna, Zaria da Katsina (jihohin Katsina da Kaduna a yau) inda yayi aiki daga 1967 zuwa 1975 sannan ya ajiye aiki bayan shekaru takwas. Ya rike matsayin shugaban jami’oi kamar haka;

  • Jami'ar Lagos
  • Jami'ar Maiduguri
  • Jami'ar Usman Danfodiyo

Garba yayi aiki a majalisar kasa a tsakanin 1979 zuwa 1999, sannan ya rike matsayin chiyaman a wadannan wurare kamar haka;

  • National freight company
  • Nigerian Railway corporation
  • John holt Plc
  • Granges company
  • Hikima trading company
  • Kado farms

An naɗa shi cikin kwamitin amintattu na gidauniyar jihar Katsina, ya rike matsayin Minista Sakatare na noma a watan Augustan 1993. Gwmanatin Tarayya ta bashi lambar yabo na Sarkin Sudan, sannan ya samu digir na digirgir daga jami’ar Usman Danfodiyo da kuma jami’ar Lagos.

Manazarta

Tags:

KatsinaNajeriyaNoma

🔥 Trending searches on Wiki Hausa / هَوُسَ:

Amurka ta ArewaHadarin Jirgin sama na KanoSinArise PointSanskritJodanNneka EgbujiobiTibiWhatsAppRamsey NouahKanoUsman Musa ShugabaPriyanka ChopraGaskiya Ta Fi KwaboJerin shugabannin ƙasar NijeriyaAlamomin Ciwon DajiKoriya ta Arewa2006Mohammad Reza PahlaviDamaturuHausa–FulaniAliyu Mai-BornuTekun BalticIsra'ilaAuren HausawaSadiya Umar FarouqAtiku AbubakarShu'aibu Lawal KumurciAbincin HausawaGabas ta TsakiyaKwaryaKa'idojin rubutun hausaMikiyaMa'anar AureAl'aurar NamijiTambarin NajeriyaFarillai, Sunnoni da Mustahabban AlwallaAdamawaDahiru Usman BauchiZariyaBukayo SakaBarkwanciAfirka ta YammaJerin Ƙauyuka a Jihar KatsinaIzalaHadiza AliyuMasallacin ƘudusBilkisuAskiAdolf HitlerWaƙaAfirka ta KuduGhanaSani Musa DanjaMasarautar KanoZamfaraAdaora OnyechereWikipediaKazaAhmad Ali nuhuBalbelaBirtaniyaTsuntsuLarabciNitish GulyaniAsiyaRagoTarihin Ƙasar JapanAlqur'ani mai girmaNajeriya🡆 More