Archimedes ko Arkimidus (lafazi: /arkimedes/ ko /arkimidus/) ya kasance masanin lissafi daga kasar Girkawa, masanin kimiyyar physics, injiniya, masanin ilimin taurari da sararin samaniya, kuma mai kirkire-kirkire daga tsohuwar birnin Syracuse, da kuma garin Sicily.
Duk da cewa akwai abubuwan da ba'a gama sani ba game da rayuwars, ana daukarsa a matsayin daya daga cikin jigogin masana kimiyya na zamunan baya - classical antiquity. Ana daukarsa a matsayin daya daga cikin masana lissafi na musamman na tarihin iyaye da kakanni, kuma daya daga cikin wanda suka samu daukaka na kowanne lokaci, Arkimidus ya fasa lissafin calculus na zamani da kuma analysis ta hanyar amfani da salon infinitely small da kuma salon exhaustion don gano da kuma tabbatar da jerin liassafin geometrical theorems.
Arkimidus | |
---|---|
Rayuwa | |
Cikakken suna | Ἀρχιμήδης |
Haihuwa | ancient Syracuse (en) , 287 "BCE" |
ƙasa | ancient Syracuse (en) |
Mazauni | Syracuse (en) |
Mutuwa | ancient Syracuse (en) , 212 "BCE" |
Yanayin mutuwa | kisan kai |
Ƴan uwa | |
Mahaifi | Fidias |
Karatu | |
Harsuna | Ancient Greek (en) |
Sana'a | |
Sana'a | masanin lissafi, physicist (en) , Ilimin Taurari, inventor (en) , military engineer (en) , mai falsafa da injiniya |
Muhimman ayyuka | Archimedes' principle (en) Archimedes' screw (en) Archimedes Palimpsest (en) Archimedes number (en) claw of Archimedes (en) Trammel of Archimedes (en) Archimedean spiral (en) Archimedes' cattle problem (en) Archimedean property (en) Archimedes' Heptagon (en) On the Sphere and Cylinder (en) |
Sauran nasarorin da Arkimidus ya samu a fannin lissafi sun hada da approximation - pi, Archimedean spiral, exponentiation. Kuma yana daya daga cikin mutane na farko-farko da sukayi amfani da lissafi a harkokin rayuwa ta yau da kullum, ta hanyar amfani da kididdiga. Daga cikin nasarorinsa anan shine tabbatar da "law of the lever", wanzuwar amfani da hikimar Law of Gravity, da dai sauransu. Har wayau, ana jinjina masa wajen kirkirar iinjinan saukaka rayuwa irinsu screw pump, injinan daukan kaya masu nauyi, da kuma injina don kare garinsu daga mahara.
Arkimidus ya mutu a harin da aka kai wa Syracuse, yayinda wani sojan Roma ya kashashe shi duk da cewa an bada umurnin kada a taba shi. Cicero ya bayyana yayin ziyartar kabarin da Arkimidus ya bukaci a birneshi, mai alamu wanda ke nuna nasarorinsa a fannin lissafi,
This article uses material from the Wikipedia Hausa / هَوُسَ article Arkimidus, which is released under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 3.0 license ("CC BY-SA 3.0"); additional terms may apply (view authors). An samar da dukkan muƙaloli a ƙarƙashin lasisin Creative Commons Attribution/Share-Alike; tana yiwuwa wasu ƙa'idoji su yi tasiri. Ku duba Ka'idojin Amfani na Gidauniyar Wiki domin ƙarin bayani. Images, videos and audio are available under their respective licenses.
®Wikipedia is a registered trademark of the Wiki Foundation, Inc. Wiki Hausa / هَوُسَ (DUHOCTRUNGQUOC.VN) is an independent company and has no affiliation with Wiki Foundation.