Twitter, a halin yanzu an sake masa tambari zuwa X, na daya daga cikin manyan kafofin sada zumunta na yanar gizo wanda kamfanin Amurka X Corp.
ke kula da ita, bayan Twitter, Inc. Masu amfani da Twitter za su iya yin rubutu, da saka hotuna da bidiyo a kafar. Masu amfani da ita za su wallafa sako (tweet), nuna son shi, sake wallafar (ko retweet), yin sharhi, da kuma aikawa da saƙon kai tsaye ga sauran masu amfani da ita. Masu amfani suna hulɗar da Twitter ta hanyar burauza ko mahaja ta wayar hannu
Ka duba wannan shafin domin sanin yanda zaka gyara wannan mukalar Koyon rubuta mukala Akwai yuwar admin ya goge wannan shafin matukar ba'a inganta ta ba. |
Jack Dorsey, Nuhu Glass, Biz Stone, da Evan Williams ne suka kirkiro Twitter a cikin Maris din Shekarar 2006. An Kuma kaddamar da ita a watan Yuli na wannan shekarar. Tsohon kamfanin, Twitter, Inc., ya kasance a San Francisco, California kuma yana da fiye da ofisoshin 25 a duniya. A shekara ta 2012, masu amfani da twitter fiye da miliyan 100 sun samar da tweets miliyan 340 a rana,
A cikin Oktoba 2022, hamshakin dan kasuwa Elon Musk ya sayi Twitter akan dalar Amurka biliyan 44, wanda haka ya ba shi iko akan mallakarta kuma ya zama Shugaba.
This article uses material from the Wikipedia Hausa / هَوُسَ article Twitter, which is released under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 3.0 license ("CC BY-SA 3.0"); additional terms may apply (view authors). An samar da dukkan muƙaloli a ƙarƙashin lasisin Creative Commons Attribution/Share-Alike; tana yiwuwa wasu ƙa'idoji su yi tasiri. Ku duba Ka'idojin Amfani na Gidauniyar Wiki domin ƙarin bayani. Images, videos and audio are available under their respective licenses.
®Wikipedia is a registered trademark of the Wiki Foundation, Inc. Wiki Hausa / هَوُسَ (DUHOCTRUNGQUOC.VN) is an independent company and has no affiliation with Wiki Foundation.