Abiya: Jiha ce a Najeriya

Jihar Abiya Jiha ce dake yankin Kudu maso Gabashin Najeriya, wacce ta hada iyaka daga arewa da kuma arewa maso kudu da jihohin Enugu da Ebonyi; sai kuma daga yamma da Jihar Imo, Jihar Cross River daga gabas, Akwa Ibom daga kudu maso gabas, sai kuma Jihar Rivers daga kudu.

Jihar ta samo asalin sunanta ne daga yankunan da suka fi kowanne yawan jama'a a garin: Aba, Bende, Isuikwuato, da kuma Arochukwu. Babban birnin jihar itace Umuahia, a yayin da Aba ta kasance mafi girma kuma cibiyar kasuwancin garin.

Abiya: Labarin kasa, Tarihi da yawan jamaa, Tattalin arziki da ababen more rayuwaAbiya
Abia (en)
Abiya: Labarin kasa, Tarihi da yawan jamaa, Tattalin arziki da ababen more rayuwa
Abiya: Labarin kasa, Tarihi da yawan jamaa, Tattalin arziki da ababen more rayuwa

Wuri
Abiya: Labarin kasa, Tarihi da yawan jamaa, Tattalin arziki da ababen more rayuwa
 5°N 8°E / 5°N 8°E / 5; 8
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya

Babban birni Umuahia
Yawan mutane
Faɗi 3,727,347 (2016)
• Yawan mutane 589.77 mazaunan/km²
Harshen gwamnati Turanci
Labarin ƙasa
Yawan fili 6,320 km²
Sun raba iyaka da
Bayanan tarihi
Mabiyi Imo
Ƙirƙira 27 ga Augusta, 1991
Tsarin Siyasa
Majalisar zartarwa Executive Council of Abia State (en) Fassara
Gangar majalisa Abia State House of Assembly (en) Fassara
Bayanan Tuntuɓa
Lambar aika saƙo 440001
Kasancewa a yanki na lokaci
Lamba ta ISO 3166-2 NG-AB
Wasu abun

Yanar gizo abiastate.gov.ng
Abiya: Labarin kasa, Tarihi da yawan jamaa, Tattalin arziki da ababen more rayuwa
Jami'ar jihar abia.
Abiya: Labarin kasa, Tarihi da yawan jamaa, Tattalin arziki da ababen more rayuwa
mutanen abia a bukukuwan al'ada.
Abiya: Labarin kasa, Tarihi da yawan jamaa, Tattalin arziki da ababen more rayuwa
Majalissar dokokin jihar abia
Abiya: Labarin kasa, Tarihi da yawan jamaa, Tattalin arziki da ababen more rayuwa
Tambarin jihar abia
Abiya: Labarin kasa, Tarihi da yawan jamaa, Tattalin arziki da ababen more rayuwa
Abia
Abiya: Labarin kasa, Tarihi da yawan jamaa, Tattalin arziki da ababen more rayuwa
sarakunan gargajiya
Abiya: Labarin kasa, Tarihi da yawan jamaa, Tattalin arziki da ababen more rayuwa
Al'adu
Abiya: Labarin kasa, Tarihi da yawan jamaa, Tattalin arziki da ababen more rayuwa
kasuwanni a wani karni
Abiya: Labarin kasa, Tarihi da yawan jamaa, Tattalin arziki da ababen more rayuwa
Abia_State_coat_of_arms

Acikin jihohi 36 na Najeriya, Abia itace ta 32 a fadin kasa kuma na 27 a yawan jama'a da kiyasin mutane akalla 3,720,000 a bisa kidayar shekara ta 2016. Dangane da yanayin kasa, jihar ta kasu zuwa kashi biyu, Niger Delta swamp forests daga karshen kudancin garin, da kuma busasshen yanayi na Cross–Niger transition forests da yanayi savanna a sauran sassan garin. Sauran muhimman yankunan garin sun hada da Rafukan Imo and Aba wadanda ke kwarara ta yammaci da kudancin iyakar Abiya.

Akwai yaruka da dama da suke zaune a Jihar Abiya a yau, musamman Inyamurai. A lokacin mulkin turawa, yankin Jihar Abiya ta yau na daga cikin yankin mutanen Arochukwu na Daular Aro kafin a turawa su ci su da yaki a Yakin Yakin Anglo-Aro a farkon karni na 1900. Turawa sun mamaye yankin bayan yakin, kuma suka sanya ta cikin Yankin Kudancin Najeriya karkashin kariyar Turawa, wacce daga baya aka hadeta cikin yankin Najeriya ta Mulkin Burtaniya; bayan an hade ta, Jihar Abiya ta zamo cibiyar adawa ga mulkin mallaka turawa wanda ya janyo yakin mata da aka fara a Oloko.

Bayan samun 'yanci a 1960, Jihar Abiya ta yau na daga cikin Yankin Kudancin Najeriya , har zuwa 1967 lokacin da aka rarraba yankin zuwa yankin Jihar Gabas ta Tsakiya. Kasa da watanni biyu bayan faruwar hakan, tsohuwar yankin na Gashin Najeriya ta jawo yakin basasa na tsawon shekaru uku a Najeriya, tare da Abiya na daga cikin garuruwan tawaye na Biyafara. Bayan yakin ya kare kuma an sake hade yankunan a Najeriya, an mayar da Jihar Gabas ta Tsakiya har zuwa 1976 lokacin da Murtala Mohammed ya samar da sabuwar Jihar Imo (wacce ta hada da JIhar Abiya a cikin ta). Bayan shekaru sha biyar, an sake raba Jihar Imo inda aka cire gabashin Imo don samar da Jihar Abiya; amma a shekarar 1996, an sake raba jihar Abiya inda aka samar da Jihar Ebonyi ta yau.

Ta fuskar tattalin arziki, Jihar Abiya ta ta'allaka a samar da man-fetur da natural gas dadi da noma, musamman na doya, masara, taro, man-ja da rogo. Akwai kamfanoni sarrafe-sarrafe musamman a yankin Aba. Dangane da saurin habakar ta a fuskar yawan jama'a da masanaantu, Abiya ta shiga na 8 daga cikin jerin cigaban al'umma a Najeriya.

Tana da yawan fili kimani na kilomita arabba’i 6,320 da yawan jama’a milyan biyu da dubu dari takwas da talatin da uku da dari tara da tisa'in da tara (ƙidayar yawan jama'a shekara 2006). Babban birnin tarayyar jahar ita ce Umuahia. Okezie Ikpeazu shi ne gwamnan jihar tun zaben shekara ta 2015 har zuwa yau. Mataimakin gwamnan shi ne Ude Okochukwu. Dattijan jihar su ne: Eyinnaya Abaribe, Theodore A. Orji da Mao Ohuabunwa.

Labarin kasa

Jihar Abiya wacce ta mamaye fadin kasa kimanin 6,320sqkm, ta hada iyaka daga kudu da kudu maso gabas da jihohin Enugu da Ebonyi. Jihar Imo daga yamma, Jihar Cross River daga gabas da kuma Jihar Akwa Ibom daga kudu maso gabas, sai kuma Jihar Rivers daga kudu. Sashin kudancin garin na fuskantar ruwan sama mai karfi na kimanin 2,400 millimetres (94 in) a duk shekara, kuma yafi karfi a tsakanin watannin Aprelu zuwa Octoba. Rafuka mafi muhimmanci a jihar sune; Imo da Kogin Aba wanda ke kwarara acikin tekun Atlantic ta jihar Akwa Ibom.

Tarihi da yawan jama'a

Abiya na daga cikin jihohi 36 na Najeriya kuma tana da kananan hukumomi guda 17. An kafa jihar Abiya a ranar 27 ga watan Augustan shekara ta 1991, a lokacin mulkin General Ibrahim Babangida. Jihar na zaune a yankin kudu maso gabashin Najeriya. An samar da jihar Abiya daga cikin jihar Imo kuma jihohin biyu sun hada iyaka. Jihar Abiya na daga cikin garuruwan Niger Delta. Babba birnin jihar itace Abiya, sannan ana mata lakabi da GOD’s OWN STATE. Jihar Abiya ta samo asalin sunanta ne daga yankunan ta hudu da sukafi ko ina yawa wato: Aba, Bende, Isuikwuato, da Afikpo.

Jihar Abiya jiha ce ta Inyamurai kuma da yaren Igbonci ake magana a garin. Inyamurai ne suka cike kusan kaso 95% na yawan mutanen garin. Sannan haka zalika ana amfani da harshen turanci a garin, kuma shine matsayin yaren gwamnati da kuma cinikayya. A jihar Abiya, fiye da mutum miliyan 7 kiristoci ne.

Tattalin arziki da ababen more rayuwa

Samar da man-fetur da gas sune muhimman tattalin arzikin Jihar Abiya, wanda yake wakiltan kaso 39% na kudaden shiga (GDP) na Jihar. Amma duk da haka kwararan kamfanonin gida na jihar dangane da shirin Marginal Fields Programme (MFP)- na samun karancin kudade da zai basu damar hakan mai a rijiyoyi kusan 50 dake jihar.

Masana'antun kere-kere na wakiltar kudaden shiga kashi 2% kacal. Cibiyar masana'antun Jihar Abia na nan a birnin Aba, wanda suka hada da kamfanonin sarrafa magunguna, sabulai, robobi, siminti, takalma da kuma kayan kwalliya. Bugu da kari, Jihar Abiya ta samar da wurin taro na kasa da kasa mai daukan mutum akalla 9000 a babban birnin Umuahia. Gwamna T.A Orji ya gina wannan katafaren wuri don bunkasa tattalin arziki ta hanyar tarar baki a tarukan kasa da kasa ko kuma na gida Najeriya da kuma masu yawan bude idanu a Jihar.

Noma na wakiltar kaso 27% na kudaden shiga na Jihar (GDP), kuma ta samar da aiki ga kaso 70% na mutanen garin. Dangane da ruwan sama mai yawa a Jihar, Abiya na da kasar noma mai kyau kuma suna noman doya, masara, dankali shinkafa, kashuw, plantain, taro da kuma rogo. Kwakwan manja ya kasance muhimmin kayan masarufi na siyarwa a Jihar.

Hako Man-fetur da Gas

Akwai akalla rijiyoyin mai guda 100 da kuma masarrafu guda uku a jihar Abiya. Akwai kuma masarrafar gas na "Abia/NNPC gas plant". Yi zuwa shekara ta 2012, cibiyar boundary Commission ta sanar da cewa ta maido da rijiyoyin mai 42 daga Jihar Rivers zuwa Abiya. Hakan na nufin cewa, Jihar Abiya ta zamo na hudu a samar da man fetur a Najeriya. Mashahuriyar kamfanin man fetur wato Shell, ke da mallakin mafiya yawan rijiyoyin man da ke Jihar, kuma ta ware kusan guda 50 wanda ake dauka a matsayin mafi muhimmanci.

Jihar tana samar da 36,000 barrels na man-fetur a duk rana; "Imoturu na samar da barrel 23,000 a duk rana; a yayin da ita kuma tashar man-fetur na Isimili ke samar da fiye da barrel 8,000 a duk rana. Akwai rijiyoyin mai guda 4 a yankin mabubbugan Izaku zuwa Obigo. Akalla rijiyoyin mai guda 30 suna kwarara zuwa Umuri sannan kuma akalla rijiyoyin mai guda 8 suna kwarara daga Umurie zuwa Afam" kamar yadda Samuel Okezie Nwogu, Chairman na Abia State Oil Producing Development Area Commission (ASOPADEC). Amma duk da haka, jihar na kukan rashin isasshen kudi daga kudaden da ake samu na man fetur daga Gwamnatin Tarayya.

Matsalolin Muhalli

Bola

Kungiyar kula da muhalli wato Municipal solid waste management (MSWM), ke da alhakin kwashe shara da tattara ta, da zubar da ita don tabbatar da cewa bata cutar da mutane ba. Akwai matsaloli da dama da suke jawo tara shara a yankuna birane, wanda suka hada da yanayin samun kudi, yanayin sararin samaniya, birane da kuma habakar tattalin arziki. Ma'aikatar MSW a jihar Abiya ta kasu kashi uku;

  1. Sharar gida (shara daga gidaje, wuraren cin abinci, kasuwanni da sauran wuraren cinikayya)
  2. Sharar Masana'antu (wanda suka hada da abubuwa masu cutarwa wanda ke bukatar kulawa ta musamman)
  3. Sharar Ma'aikatu (wannan sun hada da shara daga ma'aikatun gwamnati, makarantu, asibitoci da wuraren shakatawa)

Ma'adanan Jihar Abiya

  • Zinare
  • Lead/Zinc
  • Limestone
  • Oil/gas
  • Salt
  • Kaolin
  • Limestone

Jami'oi da Kwalejoji

Akwai jami'oi shida a jihar, akwai na gwamnatin tarayya wato Michael Okpara University of Agriculture a Umudike, Abia State University a Uturu, akwai kuma ta 'yan kasuwa Gregory University dake Uturu, Rhema University a Abia, Spiritan University a Umu Nneochi da kuma Clifford University da ke Owerrinta.

Akwai kuma kwalejin Ilimi na Abiya dake Arochukwu, akwai kuma kwalejin Kiwon Lafiya dake Aba. Temple Gate Polytechnic dake a Aba, da kuma Abia State Polytechnic.

Sufuri

Tashar jirgin sama mafi kusa a Jihar Abiya itace tashar Sam Mbakwe Cargo Airport (Tashar Jirgin sama na Owerri), tafiyar sa'a daya na iya kai mutum i zuwa Umuahia, Aba kuma tafiyar sa'a biyu ne zuwa Tashar jirgin saman Port Harcourt International Airport. Za'a iya ziyartar tashar jirgin sama na Akwa Ibom Airport (dake Akwa Ibom). Akwai nisan kimanin kilomita 73.28 (45.53 mi) a tsakanin Birnin Uyo (Akwa Ibom) da Birnin Umuahia (Abia).

Har wayau, akwai kuma tashar jirgin kasa wacce ake zirga-zirga ta hanyoyinta, amma ana kan gyaranta a yanzu. Aba ta hade da jihar Porthacourt ta titin jirgin kasa. Birnin Umuahia ta hade da Aba da Enugu ta titin jirgin kasa. Ana iya zirga zirga ta yankunan ruwayen garin akan jirgin ruwa ko kwale-kwale.

Yaruka

A kasa akwai jerin harsuna da ake amfani dasu a Jihar Abiya dangane da kananan hukumominsu:

LGA Languages
Arochukwu Inyamuranci
Ini Inyamuranci
Obi Ngwa Inyamuranci
Umuahia South Inyamuranci
Umuahia North Inyamuranci
Ikwuano Inyamuranci
Isiukwato Inyamuranci
Ukwa West Inyamuranci
Aba South Inyamuranci
Aba North Inyamuranci
Isiala Ngwa North Inyamuranci
Isiala Ngwa South Inyamuranci
Obingwa Inyamuranci
Umunneochi Inyamuranci
Ugwunagbo Inyamuranci
Ukwa East Inyamuranci

Siyasa

Gwamnan jihar shi ke gudanar da harkokin siyasa a jihar tare da taimakon mukarrabansa na majalisar dokokin jihar. Babban birnin Jihar itace Umuahia. Akwai kananan hukumomi 17 a jihar.

A lokacin da ta zamo jiha a 1991, shugaban kasa Ibrahim Babangida ya nada jagoran yankin wato Frank Ajobena kafin a zabi Ogbonnaya Onu a matsayin gwamna a Tarayyar Najeriya ta uku. Shekaru biyu bayan haka, shugabankasa Sani Abacha ya kawo karshen Tarayyar Najeriya ta Uku (Third Republic) kuma ya tilasta mulkin soja a ko ina. A zamanin mulkin Abacha, an sake nada mutane uku (Chinyere Ike Nwosu, Temi Ejoor, da kuma Moses Fasanya) har zuwa lokacin da Abacha ya mutu shi kuma Abdulsalami Abubakar ya cigaba da mulki. Abubakar ya sake nada mai gudanarwa soja Anthony Obi, kafin a fara aiki da dimukradiyya a shekarar 1998.

A 1999, Najeriya ta cigaba da bin tsarin dimukradiyya kuma an zabi Orji Uzor Kalu a matsayin gwamna a karkashin jam'iyyar PDP. An rantsar dashi a ranar 29 ga watan Mayun 1999. A sabon zabe a shekara ta 2003, Kalu ya sake fitowa takarar gwamna kuma an sake zabar sa har zuwa shekara ta 2007 inda wa'adinsa na wa'adi biyu suka zo karshe. Theodore Orji (PPA) yayi nasarar kayar da Onyema Ugochukwu (PDP) a zaben gwmanan jihar Abiya a 2007. A zaben shekara ta 2011, Theodore Orji ya fice daga jam'iyyar PPA zuwa jam'iyyar PDP bayan nan a sake zaben shi don komawa wa'adi na biyu a matsayin gwamna.

A zaben shekara ta 2015, an zabi Okezie Ikpeazu (PDP) a matsayin gwamnan jihar Abiya na tara. Ya sake yin nasara a zaben shekara ta 2015, inda ya kayar da Uche Ogah na jam'iyyar APC da Alex Otti na jam'iyyar APGA kuma an rantsar dashi a ranar 29 ga watan Mayun 2019.

Kananan Hukumomi

Jihar Abia nada Kananan Hukumomi guda goma sha bakwai (17), Sune:

  1. Aba ta Arewa
  2. Aba ta Kudu
  3. Arochukwu
  4. Bende
  5. Ikwuano
  6. Isiala Ngwa ta Arewa
  7. Isiala Ngwa ta Kudu
  8. Isuikwuato
  9. Obi Ngwa
  10. Ohafia
  11. Osisioma Ngwa
  12. Ugwunagbo
  13. Ukwa ta Gabas
  14. Ukwa ta Yamma
  15. Umuahia ta Arewa
  16. Umuahia ta Kudu
  17. Umu Nneochi

Sarakunan Jihar

Mukami Ethnic Group Suna Class Karamar Hukuma Fada
Enyi (Eze) na Aba Igbo / Eziama Aba Eze Issac Ikonne 1 Aba ta Arewa Osusu Aba
Ochiudo 1 na Aba Ukwu Igbo / Aba Jonathan U. oguejiofor (JP): Alkalin Zaman Lafiya na Tarayyar Nijeriya, Jihar Abia
Osimiri III na Aba Igbo / Aba Eze (Barrister) Sunday Emejiaka 1 Aba ta Kudu Aba
Eze Aro Igbo / Arochukwu Mazi Ogbonnaya Vincent Okoro (Eze Aro III) 1 Arochukwu Oro Arochukwu
Ugwumba 1 na Ndida Ozaar Igbo / Asa Eze Samuel Chukwuemeka Agu Ukwa ta Yamma Umuebulungwu, Ndida Ozaar
Ike 1 na Ikeisu Igbo / Isu Augustine O. Igwe (Ike I) ? Arochukwu Ikeisu (Utugiyi)
Ezeala III na Aro Ngwa Igbo / Aro Ngwa Eze Edward Enwereji ? Osisioma Ngwa
Ugo Oha (Eze) na Etiti Mgboko Umuanunu Igbo / Etiti Ngozi Ibekwe 1 Obi ngwa
Eze 1 na ovukwu abam onyerubi Igbo / Ndi oji Abam Oriji Ojembe 1 Isuikwuato ?
Eze Ukwu 1 of Ngwa-Ukwu Igbo / Ngwa Benard Enweremadu 1 Isiala Ngwa Ngwa Ukwu Kingdom. The ancestral home of Ngwa Land.
Nya 1 of Nunya Igbo / Oguduasaa M.E. Ihevume ? Isuikwuato Nunya Autonomous Community
Ossah-Ibeku (Eze) of Umuahia Igbo / Osaa HRH Nze Hope Onuigbo X X Umuahia Amibo, Nsukwe
Eze of Uturu Igbo / Uturu A.E. Ude ? Isuikwuato Uturu
Igbojiakuru (Eze) of Alayi Igbo / Alayi Ukeje Philip ? Bende Ndi Elendu, Amaeke Alayi
Awu (Eze)of Isuamawu Igbo / Isuikwuato Surveyor Chris E Aboh,FNIS ? Isuikwuato Eluama Isuama
Enachioken Of Abiriba Igbo / Abiriba Kalu Kalu Ogbu 1 Ohafia Abiriba
Ohanyere I Of Ohiya Igbo / Umuahia Eze Abel E. Uhuegbue ? Umuahia South Abia
Eze Ohanyere I Of Ahiaba Ubi Igbo / Isiala Ngwa Eze D.O. Ogbuisi ? Isiala Ngwa North Abia
EZE TOWE 1 of umutowe. Igbo / Ohiya Eze G. C Onwuka ? Umuahia South Abia
Ome Udo II Of Umueze, Ohiya Igbo / Ohiya Uche Nwamarah ? Umuahia South Abia
Okaa Omee I of Amaikwu, Abia Igbo / Ohiya Uche Nwamarah ? Umuahia South Abia
"Ehi II" of Ehi na Uguru Auto. Comm, Umuguru Igbo / Umuguru Eze E. E. Eluwa 1 Isiala Ngwa South
"Ochi 1" of Ochi na Isuochi. Comm, Umunneochi Igbo / Umu Nneochi HRM EZEKWESIRI 1 Umu Nneochi Abia

Al'adu da wuraren bude idanu

  • Arochukwu wacce ke da alaka da cinikayyar bayi
  • Azumini Blue River waterside
  • The Amakama wooden cave; wani rami a jikin bishiya dake iya daukan mutum 20
  • Kogo da ke arewa, sun hada da Umu – Neochi zuwa Arochukwu.
  • Rawar al'ada da gargajiya
  • National War Museum, Umuahia da Ojukwu Bunker a Umuahia
  • Wurin tarihin mulkin mallakan turawa na ABiya
  • Akwete” wuri saqa kaya a karamar hukumar Ukwu ta gabas
  • Masu rawar yakin Ohafia
  • Bikin tunawa da AmaforIsingwu biannual Iza aha
  • Bikin Akpe Festival a Umuahia

Sanannun mutane

  • Abai Ikwechegh - Jurist
  • Acho Nwakanma - Former Deputy Governor of Abia State
  • Adaobi Tricia Nwaubani – novelist and essayist
  • Adolphus Wabara - Former Senate President of Nigeria.
  • Akwaeke Emezi – novelist
  • Alex Mascot Ikwechegh, politician, businessman and philanthropist
  • Alexx Ekubo, Nollywood actor and Top Model
  • Alex Otti - Former Group Managing Director of Diamond Bank PLC.
  • Alvan Ikoku, OBE educationist (1900–1971)
  • Anthony Eze Enwereuzor - Former member of the Abia State House of Assembly
  • Anya Oko Anya, technocrat and academic
  • Ashley Nwosu - Former Nigerian Actor
  • Arunma Oteh – Former World Bank Vice President and Treasurer.
  • Azubuike Ihejirika – Lt. General and former Chief of Army Staff
  • Azubuko Udah - Former Deputy-Inspector General of the Nigerian Police Force
  • Basketmouth – comedian
  • Benjamin Kalu – politician and member of the House of Representatives
  • Blessing Nwagba - Female Politician
  • Bob Nwannunu - Politician
  • Bright Chimezie – Highlife Musician
  • Buchi Atuonwu - Gospel Artiste
  • Chelsea Eze – award-winning Nollywood actress
  • Chidi Imoh - Athlete
  • Chijioke Nwakodo - Politician
  • Chika Chukwumerije – Olympic Taekwondo Medalist (Beijing 2008); 3-time Olympian; first Black African Olympic Medalist in the Martial Arts.
  • Chika Okeke-Agulu - Art historian.
  • Chinedu Ikedieze – award-winning Nollywood actor
  • Chinedum Enyinnaya Orji - Speaker of the Abia State House of Assembly
  • Chinweizu Ibekwe - Renowned essayist, poet, and journalist.
  • Chinyere Almona – business executive
  • Chinyere Kalu – Nigeria's first female pilot.
  • Chioma Agomo - Professor of Law
  • Chioma Onyekwere – Nigeria's Discus Champion.
  • Chioma Toplis - Nollywood Actress.
  • Chisom Chikatara - Professional Footballer
  • Christy Ucheibe - Female Nigerian Professional Footballer
  • Chuku Wachuku – Statesman and former Director-General of Nigeria's NDE: National Directorate of Employment
  • Christopher Kanu - Former Nigerian Professional Footballer.
  • Christopher Osondu - Former Navy Captain and Military Administrator of Cross River State
  • Chukwuemeka Ngozichineke Wogu - Former Minister of Labour and Productivity
  • Clifford Ohiagu - Politician
  • Daniel Kanu - Nigerian-American Politician.
  • Dike Chukwumerije – Award-winning Novelist, Poet, Public Speaker and Spoken-word artiste. Listed on 100 most influential Africans.
  • Ebitu Ukiwe – former Military Vice President; Former Governor of Niger and Lagos States.
  • Ejike Asiegbu- Nollywood Veteran actor
  • Ejikeme Ikwunze - Sports Journalist
  • Emma Ugolee - Media Personality and Author
  • Emmanuel Acho - Former American Football Player; Analyst at Fox Sports 1
  • Emeka Ananaba - Former Deputy Governor of Abia State
  • Eni Njoku – pioneer Vice Chancellor, University of Lagos and first black Vice Chancellor, University of Nigeria Nsukka.
  • Enyinnaya Abaribe – Senator and former Deputy Governor
  • Eucharia Oluchi Nwaichi - Environmental biochemist, Soil Scientist, and Toxicologist
  • Ezinne Kalu, Female Basketballer
  • Eziuche Ubani - Female Politician
  • Felix Nmecha - Professional Football Player
  • Fortunatus Nwachukwu - Catholic Prelate
  • Francis Ezeh - Professional Football Player
  • Godswill Obioma - Former National Examination Council Registrar
  • Ifu Ennada - Actress, Fashion Designer, and Former Big Brother Naija Housemate.
  • Iheanacho Obioma - Politician
  • IK Ogbonna, Nollywood Actor and Top Model
  • Ike Ibeabuchi, Professional Boxer.
  • Ike Nwachukwu, military officer, former state governor, diplomat, former senator and former chairman of the governing board of Nigerian Institute of International Affairs.
  • Ikechi Uko- Renowned travel consultant
  • Ikechukwu Uche - Former Nigerian Professional Footballer
  • Ikeogu Oke - Author, Journalist, and Award-winning Poet
  • Isaac Nwaobia - Anglican Bishop
  • Ivy Uche Okoronkwo - First Female Deputy Inspector General of Police
  • J. Martins, Afro-pop artiste
  • Jaja Wachuku – First Minister of Foreign Affairs in Nigeria, First indigenous Speaker of the House of Representatives of Nigeria and first Nigerian Permanent representative to the UN.
  • Joe Irukwu - Nigeria's First Professor of Insurance.
  • Joel Kachi Benson, documentary film maker.
  • John Godson – Polish lawmaker and philanthropist.
  • Johnson Aguiyi-Ironsi – Nigeria's Military Officer and former Head of State.
  • Josaiah Ndubuisi Wachuku - Former Eze of Ngwa land.
  • Joyce Kalu - Nollywood Actress
  • Kalu Uche - Former Nigerian Professional Footballer
  • Kalu Idika Kalu – former Finance Minister and politician
  • Kalu Ikeagwu - Movie Actor and Writer.
  • Kalu Ndukwe Kalu - Political scientist and Distinguished Research Professor of Political Science and National Security Policy at Auburn University
  • Kelechi Emeteole - Former Nigerian Professional Footballer
  • Kenneth Omeruo - Nigerian Professional Footballer
  • Larry Gaaga - Renowned Songwriter and Music Producer
  • Linda Ejiofor - Nollywood Actress
  • Lukas Nmecha - Professional Football Player
  • Mao Ohuabunwa, industrialist and politician
  • Mary Ikoku - Development Consultant
  • Mary Lazarus - Nollywood Actress
  • Martins Azubuike - Former Speaker of Abia State House of Assembly.
  • Michael Okpara – premier of Nigeria's Eastern Region from 1959 to 1966
  • Mr Raw – Igbo rap music pioneer
  • Nathan Kanu - Anglican Bishop
  • Ndubuisi Kanu – Former Governor of Lagos State and old Imo State.
  • Njoku Nnamdi - Former Member of the Abia State House of Assembly
  • Nkechi Blessing Sunday - Nollywood actress
  • Nkechi Justina Nwaogu – Two Time Senator Abia Central Senatorial District and Immediate Past Pro Chancellor University of Calabar.
  • Nkiru Sylvanus - Awarding winning Nollywood actress
  • Nnamdi Kanu – founder of the Indigenous People of Biafra (IPOB), a separatist group.
  • Nnamdi Udoh - Aeronautical Engineer
  • Ndubuisi Ekekwe - Notable Inventor
  • Nnenna Elendu Ukeje - Female Politician
  • Nwabueze Nwokolo - British Lawyer
  • Nwankwo Kanu – Two time African Footballer of the year and Arsenal FC legend.
  • OC Ukeje – Lagos-based Multiple Award Winning Nollywood actor
  • Ogbugo Kalu - Renowned Army Officer.
  • Oji Umozurike, professor of law
  • Ojo Maduekwe - Former Nigerian Politician.
  • Okechukwu Enelamah – former Minister for Trade and Investment (2015–2019)
  • Okezie Ikpeazu – Abia State Governor
  • Olu Oguibe - Professor of art at the University of Connecticut and senior fellow at the Smithsonian Institution in Washington, DC
  • Oluchi Onweagba - International model and first winner of M-Net Face of Africa
  • Onwuka Kalu - Business Mogul and co-founder of Fidelity Union Merchant Bank
  • Onyema Ogbuagu - Medical Researcher
  • Onyema Ugochukwu - First Executive Chairman of the Niger Delta Development Commission(NDDC)
  • Orji Uzor Kalu – chairman, SLOK Group; Former State Governor and one time Founder of Progressive People's Alliance (PPA); Senator of the Federal Republic of Nigeria
  • Pascal Atuma – Canadian-Nigerian actor, screenwriter, film producer, director and CEO/Chairman TABIC Record Label. born in Ikwuano Umuahia, Abia State, Nigeria.
  • Pascal Ojigwe - Nigerian former professional footballer and Abia State Commissioner of Sports.
  • Paul Agbai Ogwuma – former Governor of Nigeria's Central Bank
  • Randy Onuoha, Professional Footballer.
  • Rosemary Inyama - Female Politician
  • Ruggedman, Afro-Rap artiste.
  • 2Shotz, AfroRap Artiste
  • Sam Acho - ESPN Sports Analyst and Veteran American Football Player.
  • Sam Ohuabunwa - Founder of Neimeth Pharmaceutical and Former President of the Pharmaceutical Society of Nigeria
  • Samuel Achilefu – Notable Inventor
  • Samuel Chukwueze – Nigeria National Team football player
  • Samuel Kalu - Nigerian Professional Footballer.
  • Sunday Mba - Nigerian Professional Footballer
  • Theodore Orji – former State Governor and a serving Senator of the Federal Republic of Nigeria.
  • Uche Jombo, award-winning Nollywood actress.
  • Macebuh Chinonyerem - Former member of the Abia State House of Assembly
  • Mike Ezuruonye – Award-winning Nollywood actor.
  • Nwakanwa Chimaobi - Former member of the Abia State House of Assembly
  • Uche Chukwumerije – 3-time Senator of Fed Rep of Nigeria; Former Nigerian Minister of Information and Culture; Former Biafran Minister of Information; Publisher Afriscope Magazine.
  • Uche Elendu - Nollywood actress
  • Uche Okechukwu – former Nigerian Team footballer
  • Uchechukwu N. Maduako - Former Member of the Abia State House of Assembly
  • Uchechukwu Sampson Ogah – Businessman and Politician
  • Uchenna Ikonne – Academic and Public Administrator
  • Uchenna Kanu - Female Nigerian Professional Footballer
  • Ude Oko Chukwu - Deputy Governor of Abia State
  • Uko Nkole - Politician
  • Uma Ukpai – evangelist.
  • Umeh Kalu - Former Commissioner of Justice for Abia State.
  • Uzo Asonye - Partner at Davis Polk & Wardwell
  • Uzodinma Iweala – US-based medical doctor and author of the book Beasts of No Nation.
  • Uzoma Emenike- Nigeria's Ambassador to the United States of America.
  • Victoria Inyama - Nollywood Actress.
  • Vincent Eze Ogbulafor - Former National Chairman of the People's Democratic Party
  • Waconzy - Musician
  • Yagazie Emezi - Award-winning photojournalist
  • Yvonne Okoro - Ghanaian-Nigerian actress

Manazarta


Jihohin Najeriya
Babban birnin tarayyar (Abuja) | Abiya | Adamawa | Akwa Ibom | Anambra | Bauchi | Bayelsa | Benue | Borno | Cross River | Delta | Ebonyi | Edo | Ekiti | Enugu | Gombe | Imo | Jigawa

Kaduna | Kano | Katsina | Kebbi | Kogi | Kwara | Lagos | Nasarawa | Neja | Ogun | Ondo | Osun | Oyo | Plateau | Rivers | Sokoto | Taraba | Yobe | Zamfara

Tags:

Abiya Labarin kasaAbiya Tarihi da yawan jamaaAbiya Tattalin arziki da ababen more rayuwaAbiya Matsalolin MuhalliAbiya Maadanan Jihar Abiya Jamioi da KwalejojiAbiya SufuriAbiya YarukaAbiya SiyasaAbiya Kananan HukumomiAbiya Sarakunan JiharAbiya Aladu da wuraren bude idanuAbiya Sanannun mutaneAbiya ManazartaAbiyaAkwa IbomCross RiverEbonyiEnugu (jiha)ImoJihar RiversNajeriyaUmuahia

🔥 Trending searches on Wiki Hausa / هَوُسَ:

TaimamaCiwon nonoFox Broadcasting CompanyShayarwaCiwon daji na fataAjay DevgnHafsat IdrisJerin AddinaiEmeka EnyiochaCiwon daji na prostateShehu KangiwaZubar da cikiMasarautar GombeKatsina (birni)Bala MohammedTatsuniyaAureYahudawaKimiyyaSirbaloAl Neel SC (Al-Hasahisa)Khulafa'hur-RashidunHausa BakwaiBrazilHawainiyaAtiku AbubakarKadaMasarautar DauraUmar Abdul'aziz fadar begeLaberiyaMaliBayajiddaSani Umar Rijiyar LemoChris RockCirrhosisIsrai da Mi'rajiToyota StarletRundunonin Sojin NajeriyaBBC HausaMusulmiAnas HalouiAl-BurdaHarshen HausaRowan AtkinsonMaryam kkGastroenteritisGado a MusulunciSoAminu Ibrahim DaurawaƘur'aniyyaDankalin turawaMargret HassanTsibirin BamudaUkraniyaKhalid ibn al-WalidZoroasterJerin Sunayen 'yan majalisar wakilan Najeriya, 2019–2023Bassirou Diomaye FayeCiwon hantaKanuriWuhanAfirka ta KuduAaron BoupendzaAfghanistanIsah Ali Ibrahim PantamiUba SaniSwitzerlandDavid CameronAllahYolande Amana GuigoloOndo (jiha)Zauren yan majalisar dokokin Jihar KanoKhadijatul Iman Sani Danja🡆 More