Bbc Hausa

BBC Hausa kafar yaɗa labarai a harshen Hausa ce, Mallakin tashar labarai ta BBC da turanci wato (British Broadcasting Corporation (BBC) World Service wadda take watsa shirye-shiryen ta a harshen Hausa musamman ma labarun da suka shafi ƙasashen Nigeria, Ghana, Niger da kuma sauran masu jin harshen Hausa dake a yankunan Yammacin Afrika.

Bangare ne na harsunan da BBC ke watsa shiryeshiryen ta guda 33 wadanda guda 5 daga cikin su yarukan Afrika ne. Ana watsa shirye shiryen sashen na Hausa kai tsaye daga babbar tashar ta BBC dake birni Landan wato Broadcasting House da kuma tashar ta dake babban birnin taraiyar Najeriya Abuja dakuma shafinta na yanar gizo wanda ake wallafawa duka dai a birnin na Abuja

Bbc HausaBBC Hausa
Bbc Hausa
Bayanai
Iri broadcast network (en) Fassara da Jaridar yanar gizo
Ƙasa Birtaniya
Bbc Hausa
Tambarin BBC HAUSA

Tarihin BBC Hausa

Tashar BBC Hausa itace sashen farko da BBC ta fara gabatar,da shirye shiryen ta daga cikin harsunan dake Afrika kuma daya daga cikin biyar na harsunan Afrika da BBC ke watsa shirye shiryen ta. An kaddamar da tashar ne a ranar 13 ga watan Maris din shekara ta alif 1957 da karfe Tara da rabi 9:30 agogon GMT da shirin minti 15 wanda Aminu Abdullahi Malumfashi ya gabatar. Daga baya kuma Abubakar Tunau yacigaba da kawo labaran fassara a shirin BBC na Labarun yammacin Afrika wato West Africa in the News. Ana gabatar da shirye shiryen sashin Hausa na BBC na farko farko a ranakun Laraba da Juma'a ne kawai, bayan shekara daya kuma akaci gaba da gabatar da labarun kullum kullum.ranar 1 ga watan Yuni shekara ta alif dari tara da Hamsun da takwas 1958.

A watan Mayu na 2017 ne BBC Hausa tayi bikin cika shekara ta sittin 60 da fara watsa shirye shirye. Bikin ya samu halartar daraktar BBC wato BBC World Service Group, Fran Unsworth.

Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya tura sakon murya a yayin bikin inda ya ambaci tashar ta BBC Hausa da tashar jan hankalin masu sauraro kuma wadda ta kwashe shekaru tana gabatar da shirye shirye.

Ofishin Abuja

Anbude Ofishin BBC Hausa a Abuja tun a shekarar 2002.

Watsa, shirye shirye

A yawancin lokuta BBC nada babban edita da masu gabatar da shirye shirye da mataimakan editoci da babban mai gabatar da rahoto. Sannan kuma tafi karfin gabatar da labarunta game da al'amuran da suka shafi biranen Kaduna, Kano, Jos, Enugu, Abuja da Sokoto da kuma kasahen Niger republic, Ghana da kasar Sin.

Tashoshin FM da suke gabatar da shirye shiryen BBC Hausa a Najeriya

Ana sake watsa wasu shirye shiryen na BBC Hausa a kafafan Radiyo da Talabijin dake Najeriya da hadin gwiwar kafar BBC wato BBC World Service. Ga wasu daga cikin su

Shiye shiryen kafar yanar gizo

Bbc Hausa 
Wasu daga cikin kafofin yanar gizo da ake sauraren bbc hausa kenan

Ana gabatar da shirye-shiryen sashen Hausa na BBC a kafar yanar gizo cikin kwarewa kuma da sauki wajen nemowa. Kafar yanar gizon BBC Hausa ta zama kafa ta biyu wadda akafi ziyarta a Najeriya, da masu ziyarta miliyan 68.6 a wata (wasu da wayar hannu wasu kuma da kwamfuta wasu kuma da akwatun Rediyo). Da kuma mabanbantan masu siya miliyan 3.5 a kowanne wata. BBC Hausa nada mabiya masu dimbin yawa a kafafen sada zumunta. Kimanin sama da mutum 840,000 a Facebook, da mabiya sama da 100,000 a Twitter, da mabiya samada 70,000 a Googl+, da mabiya samada 6,600 a Youtube.

Manazarta

Tags:

Bbc Hausa Tarihin BBC HausaBbc Hausa Watsa, shirye shiryeBbc Hausa ManazartaBbc HausaAbujaGhanaHarshen HausaHausaNijar (kasa)Nijeriya

🔥 Trending searches on Wiki Hausa / هَوُسَ:

Aisha NajamuAbubakar ImamMusa DankwairoHawan dabaSoftwarefordBayajiddaSenegalMinnaTarihin HabashaHausa–FulaniJerin kasashenJimlaZakiPakistanAl'adar bikin cika-cikiKashin jiniJide Kene AchufusiJerin ƙauyuka a jihar YobeAmen Edore OyakhireYaƙin Duniya na IISaudiyyaJohn CenaKogon da As'habDahiru Usman BauchiMagaryaKhadija MainumfashiAshiru NagomaMaliBidiyoKatsina (birni)BudurciGaskiya Ta Fi KwaboYadiyaMohammed Umar BagoHamisu BreakerBukar IbrahimJerin Sunayen Gwamnonin Jihar BornoWikiA'Darius PeguesGariAskiDutsen ZumaIsaiah Oghenevwegba OgedegbeKalmar TheBrisbaneChukwuma Kaduna NzeogwuAbujaSani DauraShamsiyyah SadiKufaHawan jiniAminu DantataƘanzuwaWakilin sunaWiktionaryRashaRahama SadauGrand PHusufin rana na Afrilu 8, 2024Yaƙin UhuduKambodiyaUmaru Musa Yar'aduaDaular UsmaniyyaHarshe (gaɓa)Ahmed MusaKanunfariKanyaIlimin taurari a duniyar Islama ta tsakiyar zamaniHukumar Hisba ta Jihar KanoRubutaccen adabiJyoti ChettyMalmo🡆 More