Helen Adams Keller marubuciya ce kuma mai jawabi yar kasar Amurika.
An haifeta a Tuscumbia, ta jihar Alabama a 1880. Mahaifinta shine Arthur H. Keller mahaifiyarta kuma Kate Adams Keller. Tana yar watanni goma sha tara ne ta kamu da larurar da tayi sanadiyyar da ta rasa ji da ganin ta. Tana da matukar biyayya kuma gata yarinyar kirki. Magana da sauran mutane yanayi mata matukar wahala saboda bata gani kuma bata ji. Tana yin amfani da wata irin ishara ne wajen isar da sako musamman ga ahalin ta. Saidai da farko su ahalin na Helen basa fahimtar isharar tata, hakan kuma n tayar mata da hankali. Lokacin da Helen ke da shekaru bakwai be ahalin ta suka yanke shawarar nema mata malami nata na musamman. Sai suka rubuta wasika zuwa ga wani Michael Anagnos, wanda shine darakta na makarantar makafi ta Perkins Institute and Asylum for Blind. Sun rokeshi da ya taimaka masu wajen samun malamin. Sai ya dawo masu da salon cewa akwai wata matashiyar malama sunan ta Anne Sullivan. Dafarko itama makauniya ce amma bayan wata tiyata daga baya kuma sai ganinta ya dawo. Anne ta tafi zuwa Alabama inda ta zauna tare da ahalin Keller domin ta koyar da Helen a Maris 1887
Helen Keller | |
---|---|
Rayuwa | |
Cikakken suna | Helen Adams Keller |
Haihuwa | Tuscumbia (en) , 27 ga Yuni, 1880 |
ƙasa | Tarayyar Amurka |
Mazauni | Coolidge Hill Road (en) Dana Street (en) |
Mutuwa | Easton (en) , 1 ga Yuni, 1968 |
Makwanci | Washington National Cathedral (en) |
Yanayin mutuwa | Sababi na ainihi (cuta) |
Ƴan uwa | |
Mahaifi | Arthur Henley Keller |
Mahaifiya | Catherine Adams |
Abokiyar zama | Not married |
Ƴan uwa | view
|
Karatu | |
Makaranta | Radcliffe College (en) The Cambridge School of Weston (en) Jami'ar Harvard Perkins School for the Blind (en) |
Matakin karatu | Bachelor of Arts (en) |
Harsuna | Turanci |
Malamai | Anne Sullivan (en) |
Sana'a | |
Sana'a | marubuci, orator (en) , essayist (en) , political activist (en) , trade unionist (en) , peace activist (en) , suffragette (en) , linguist (en) da autobiographer (en) |
Mahalarcin | |
Muhimman ayyuka | The Story of My Life (en) The Frost King (en) |
Kyaututtuka | gani
|
Ayyanawa daga | gani
|
Mamba | Industrial Workers of the World (en) American Academy of Arts and Letters (en) National Woman's Party (en) |
Imani | |
Addini | The New Church (en) |
Jam'iyar siyasa | Socialist Party of America (en) |
IMDb | nm0445656 |
Anne ta taimakama Helen wajen koya mata yadda zata runka isar da sakonni ga jama'a. Ta koya mata sunayen abubuwa ta hanyar rubuta mata sunayensu a hannun ta. Da farko Helen bata iya gane sunayen abubuwa. Kalmar farko da ta fara koya itace WATER Ruwa kenan da Hausa. Tafara da koyon kalmar ne daga lokacin da Anne ta dora hannun Helen kan ruwa inda ta rubuta mata haruffan W, A, T, E, R a hannun ta. A shekarar 1890 me ahalin Helen suka turata makarantar Perkins domin ta koyi magana. Lokacin da shekarun Helen suka kai 19 ne ta tafi kwalejin Redcliffe a Massachusetts. Ta kammala a 1904. Itace kurma-makauniya ta farko data taba samun digiri. A shekarar 1903 Helen ta rubuta littafi dangane da rayuwar ta. Sunan littafin The Story of my life ma'ana Tarihin rayuwa ta. a 1964 aka shirya wani wasan kwaikwayo maisuna The Miracle Worker dangane da rayuwar ta. Ta kuma rubuta littafi dangane da malamarta maisuna Teacher. Ta kuma rubuta wasu litattafan goma sha biyu. Helen ta tallafi masu karamin karfi da makafi lokacin rayuwarta. Tayi tafiye tafiye zuwa sama da kashe 39.
Helen Keller taso tayi aure inda ta fada soyaiya da sakataren ta, saidai mahaifiyarta bata barta ta aure shi ba saboda a lokacin masu bukata ta musamman ba'a barinsu suyi aure. Hellen Keller ta rasu a 1 ga Yuni 1968
This article uses material from the Wikipedia Hausa / هَوُسَ article Helen Keller, which is released under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 3.0 license ("CC BY-SA 3.0"); additional terms may apply (view authors). An samar da dukkan muƙaloli a ƙarƙashin lasisin Creative Commons Attribution/Share-Alike; tana yiwuwa wasu ƙa'idoji su yi tasiri. Ku duba Ka'idojin Amfani na Gidauniyar Wiki domin ƙarin bayani. Images, videos and audio are available under their respective licenses.
®Wikipedia is a registered trademark of the Wiki Foundation, Inc. Wiki Hausa / هَوُسَ (DUHOCTRUNGQUOC.VN) is an independent company and has no affiliation with Wiki Foundation.