Abū Ḥanīfa al-Nuʿmān b.
Thābit b. Zūṭā b. Marzubān (larabci|أبو حنيفة نعمان بن ثابت بن زوطا بن مرزبان; Yarayu daga shekara ta c. 699 zuwa shekara 767 CE), An haife shi a shekara ta 699 (80 Hijri)
garin Kufa, Umayyad Caliphate, ya kuma dasu a shekara ta 767 (150 Hijri)
a birnin Baghdad, Abbasiyya, Dan asalin Parisa ne shi Shi Dan garin Kufa ne
Imam Abu Hanifa | |
---|---|
Rayuwa | |
Cikakken suna | النُّعْمَانِ بْنِ ثَابِتٍ بْنِ مَرْزُبَان الكُوفِيّ التَّيْمِيّ بِالْوَلَاء |
Haihuwa | Kufa, 5 Satumba 699 (Gregorian) |
Mutuwa | Bagdaza, 18 ga Yuni, 767 (Gregorian) |
Makwanci | Bagdaza |
Karatu | |
Harsuna | Larabci |
Malamai | Hammad ibn Abi Suleyman (en) Ata ibn Abi Rabah (en) Zayd ibn Ali (en) Jafar ibn Muhammad Anas bn Malik Amir al-Sha'bi (en) Tawus ibn Kaysan (en) Jabalah ibn Suhaim (en) Abd al-Rahman ibn Húrmuz (en) Amr ibn Dinar (en) Talha ibn Nafi (en) Nafi Mawla ibn Umar (en) Muharib ibn Diththar (en) Alqamah ibn Marthad (en) Abd-al-Aziz ibn Rafí (en) Samak ibn Harb (en) Abdul Malik bin Omair (en) Al-Baqir Ibn Shihab al-Zuhri (en) Muhammad ibn Munkadir (en) Ata ibn al-Saib (en) Hisham ibn Urwah (en) |
Ɗalibai | view
|
Sana'a | |
Sana'a | Ulama'u, Ɗan kasuwa da Islamic jurist (en) |
Muhimman ayyuka | Musnad Abu Hanifa Al-Fiqh al-Akbar (en) |
Imani | |
Addini | Musulunci |
Ya shahara a karantar da fahimtar sa akan Istihsan, ya wallafa shahararren littafin nan wato Al-Fiqh al-Akbar. Malamansa sune; Hammad bin Abi Sulayman, Ata' ibn abi rabah, Zayd ibn Ali, Ja'far al-Sadiq, da sauran manyan tabi'in, yakarantar da dalibansa kamar su; Imam Malik Ibn Anas, Imam Al-Shafi'i, Muhammad al-Shaybani, Abu Yusuf, al-Tahawi, Ahmad Sirhindi, Shah Waliullah da sauransu.
Anfi saninsa da Abū Ḥanīfa ko kuma Imam Abū Ḥanīfa musamman a wurin mabiya Sunnah, Yakasance dan karni na 8th ne, mabiyin Sunnah, Malamin Tauhidi kuma Alkali wanda asalinsa ba Parise ne. shine yasamar da makarantar Hanafiyya ko Hanafi Mazhab, wanda har wayau itace Mazhabar dake da mafi yawan mabiya ahlus-sunnah a duniya. Ana kiransa da al-Imām al-aʿẓam ("The Great Imam") and Sirāj al-aʾimma ("The Lamp of the Imams") a wurin mabiya ahlus-sunnah.
An haife shi daga cikin Gidan musulunci a garin Kufa, Abu Hanifa yatafi zuwa yankin Hejaz dake kasashen larabawa a waccan lokacin yayinda yake matashi, a nan ne yayi karatu a wuraren manyan malaman garin Makkah da Madina. A matsayin sa na Malamin akida kuma mai hukunci Abu Hanifa yayi suna akan yardarsa da amfani da hankali wurin yin hukunci da ma akida (faqīh dhū raʾy). makarantar Abu Hanifa itace ta zama zuwa makarantar Maturidi school of orthodox Sunni theology.
Al'umman Zaydi Shi'a suma dai baa barsu abaya ba, Dan suna matukar girmama Imam Abu hanifa a matsayin wani babban Malamin addinin musulunci.
This article uses material from the Wikipedia Hausa / هَوُسَ article Imam Abu Hanifa, which is released under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 3.0 license ("CC BY-SA 3.0"); additional terms may apply (view authors). An samar da dukkan muƙaloli a ƙarƙashin lasisin Creative Commons Attribution/Share-Alike; tana yiwuwa wasu ƙa'idoji su yi tasiri. Ku duba Ka'idojin Amfani na Gidauniyar Wiki domin ƙarin bayani. Images, videos and audio are available under their respective licenses.
®Wikipedia is a registered trademark of the Wiki Foundation, Inc. Wiki Hausa / هَوُسَ (DUHOCTRUNGQUOC.VN) is an independent company and has no affiliation with Wiki Foundation.