Swahili, Anfi saninsa da Kiswahili wanda ke nufin (Harshen Mutanen Swahili), tana daga cikin Harshen Bantu kuma itace harshen farko na Mutanen Swahili.
Itace harshen magana wato lingua franca a yankin African Great Lakes da wasu yankunan gabashi da kudu maso gabashin Africa, dasuka hada da Tanzania, Kenya, Uganda, Rwanda, Burundi, Mozambique, da the Democratic Republic of the Congo (DRC). harshen Comorian, da ake amfani dashi a Comoros Islands shima wani nau'in harshen Swahilin ne, dukda wasu na ganinsa a matsayin wani harshe ne daban.
Harshen Swahili | |
---|---|
Kiswahili — كِسْوَحِيلِ | |
'Yan asalin magana | 15,437,390 (2012) |
| |
Baƙaƙen rubutu | Baƙaƙen boko da Swahili Ajami (en) |
Lamban rijistar harshe | |
ISO 639-1 | sw |
ISO 639-2 | swa |
ISO 639-3 | swa |
Glottolog | swah1254 |
Ba a san ainihin adadin masu jin Swahili ba, walau na asali ne ko kuma na yare na biyu, kuma batu ne na muhawara. An gabatar da ƙididdiga daban-daban kuma sun bambanta sosai, daga miliyan 50 zuwa sama da miliyan 100.[4] Swahili yana aiki azaman yaren ƙasa na ƙasashe huɗu: Tanzaniya, Kenya, Uganda, da JDK. Shikomor, harshen hukuma a Komoro kuma ana magana da shi a cikin Mayotte (Shimaore), yana da alaƙa da Swahili.[5] Har ila yau Swahili ɗaya ne daga cikin harsunan aiki na Ƙungiyar Tarayyar Afirka kuma an amince da ita a matsayin harshen yare na Ƙungiyar Gabashin Afirka.[6] kasar Afirka Kudu ta yarda da koyar da Swahili a cikin kasar a cikin batutuwan ganin dama, za a fara a 2020.[7]
Yawancin kalmomin Swahili ansame sune daga harshen Larabci, misali Kalmar littafi a Swahili shine "kitabu", yayi daidai da Kalmar a larabci "كتاب". Dukda cewar jam'in kalmar littafi a Swahili shine "vitabu", haka daga tsarin harshen Bantu na "ki-" a matsayin Kalmar shigarwa kafi suna, wanda jam'insa shine "vi-".
This article uses material from the Wikipedia Hausa / هَوُسَ article Harshen Swahili, which is released under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 3.0 license ("CC BY-SA 3.0"); additional terms may apply (view authors). An samar da dukkan muƙaloli a ƙarƙashin lasisin Creative Commons Attribution/Share-Alike; tana yiwuwa wasu ƙa'idoji su yi tasiri. Ku duba Ka'idojin Amfani na Gidauniyar Wiki domin ƙarin bayani. Images, videos and audio are available under their respective licenses.
®Wikipedia is a registered trademark of the Wiki Foundation, Inc. Wiki Hausa / هَوُسَ (DUHOCTRUNGQUOC.VN) is an independent company and has no affiliation with Wiki Foundation.