manufofi Biyar

An gina Wikipedia akan muhimman manufofi guda biyar:
Wiki:
manufofi Biyar
Wiki insakulofidiya ce, (Kundin Ilimi)
Wiki insakulofidiya ce da ta tattaro ilimin bangarori da dama wanda ya shafi dukkan ilimin dan adam. Ba manufar Wikipedia bane tallata wata haja ta wata akidar siyasa ko rayuwa, ba kuma hadafinta bane tallacen tallacen ra'ayoyi da kuma kayan kasuwanci ba. Wikipedia ta bambanta da jarida ko mujalla, domin ba hadafinta bane bada labaran yau da kullum ba, ba kuma kamus bace, domin ba manufar ta bane bada bayanin ma'anonin kalmomi ba.
manufofi Biyar
Wiki ana rubuta ta daga mahangar da ba son rai
Wiki:
Editocin Wikipedia suna kokarin yin bayanin al'amurra daga mahangar da ba son rai a cikinta, da kuma baiwa kowane al'amari hakkinsa. Wannan yana nufin dukkan muƙaloli dake a cikin Wikipedia ya zama tilas a rubuta su daga mahangar adalci, mahangar da ba son rai ko kuma fifita wani al'amari saboda wani dalili. In kana rubuta muƙala, ka rubuta iya sahihan bayanai da aka riga aka rubuta a ingantattun littatfai ko jaridu da makamantansu, sanna kuma ka bada inda ka samo wannan bayanan daga karshen muƙalar.
manufofi Biyar
Wiki ta kowace, da kowa zai iya gyarawa kuma yayi amfani da abubuwan da ke cikinta
Wiki:
Dukkan abun da aka rubuta a Wikipedia yana da madogara, akuma karkashin lasisin CC BY-SA 3.0 wanda yake ba kowa damar iya amfani da rubutun, saboda haka babu wani edita daya da yake da hakkin mallakar wata mukala ko wani shafi akan Wikipedia; ko da shi kadai ya rubuta shi duka.
manufofi Biyar
Masu gyara Wikipedia (Editoci) dole suyi mu'amala da juna cikin girmamawa
Wiki:
Domin samun damar yin aiki cikin jin dadi da zaman lafiya, dole ne kowane editan Wikipedia ya girmama dan uwanshi, kuma ya maida ansa ko martani ta hanyar amfani da tattausan lafuzza a yayin da ake muhawara. Babu maganar cin zarafin juna, kuma ko da yaushe ka kyautata zato akan dan uwanka edita.
manufofi Biyar
Matsayin dokoki a Wikipedia
Wiki:
Wiki tana da wata babbar manufa ta tattaro dukkanin ilimin dan adam tare da wallafa shi domin amfanin al'umma ta hanya mai sauki. Kasancewar wannan manufa tana gaba da komai, yana da kyau duk inda kaga wani gyara ko abinda ba daidai bane a cikin wata mukala, kawai ka gyara shi. Kar ka ji tsoro, kuma kar kayi taraddudi akan hakan.
*Manufofi Biyar *Shawarwari akan gyaran Wiki *Yadda ake rubuta muƙala *Rubutu a mahangar da ba son rai *Ingancin tushen bayanai

🔥 Trending searches on Wiki Hausa / هَوُسَ:

Sunayen RanakuPatricia KlesserJabir Sani Mai-hulaEvani Soares da SilvaKolmaniNahawuGajimareSani Umar Rijiyar LemoJerin shugabannin ƙasar NijeriyaStacy LackayShari'aSana'ar NomaIzalaZariyaDaular SokotoTarihin Kasar SinMansura IsahBello Muhammad BelloJerin kasashenDaular UsmaniyyaAbincin HausawaSunnahJerin Sunayen Gwamnonin Jihar BornoBet9jaRaisibe NtozakheHaruffaMuhammadu Abdullahi WaseAbdul Rahman Al-SudaisLaberiyaNajeriyaAa rufaiMikiyaJerin Sunayen Gwanonin Jihar SokotoTukur Yusuf BurataiGambo SawabaFezbukJami'ar BayeroWhatsAppJerin ƙauyuka a jihar YobeOlusegun ObasanjoCadiKazaAngo AbdullahiSule LamidoKalmaMan shanuJerin ƙauyuka a jihar BauchiRoger De SáYaƙin Duniya na IBayanauAbba el mustaphaAisha TsamiyaOga AmosMaryam MalikaSunmisola AgbebiBirtaniyaGrand PMafarki2009TuranciFaggeJinin HaidaAliyu Magatakarda WamakkoAyislanJean-Luc HabyarimanaBudurciIbrahim Hassan DankwamboHadi SirikaZanzibarZaboFalasdinawa🡆 More