Harin Jirgin Ƙasar Abuja-Kaduna: Harin Jirgin kasa a Jihar Kaduna, Najeriya

A ranar 28 ga Maris, 2022, an kai hari kan wani jirgin ƙasa daga Abuja zuwa Kaduna a Katari, jihar Kaduna, Najeriya.

A martanin da ta mayar, hukumar kula da layin dogo ta Najeriya (NRC) ta dakatar da ayyukan hanyar na ɗan takaitaccen lokaci.

Infotaula d'esdevenimentHarin jirgin ƙasar Abuja-Kaduna
Iri aukuwa
mass shooting (en) Fassara
Garkuwa da Mutane
Kwanan watan 28 ga Maris, 2022
Wuri Jihar Kaduna
Nufi Nigerian Railway Corporation
Adadin waɗanda suka rasu 60
Perpetrator (en) Fassara Ƴan ƙungiyar fashi a Najeriya
Makami improvised explosive device (en) Fassara
Bindiga

Lamarin

Da misalin ƙarfe 7:45 na dare, an yi garkuwa da ɗaruruwan fasinjojin da ke tafiya arewa kan hanyarsu ta zuwa yankin arewa maso yammacin Najeriya a Katari, jihar Kaduna, yayin da wasu ‘yan bindiga suka kai hari kan jirgin Abuja zuwa Kaduna, suka kashe tare da jikkata wasu.

Kimanin fasinjoji 970 ne ke cikin jirgin, kuma mai yiwuwa ƴan fashin sun yi awon gaba da wasu da dama cikin daji da wasu 'yan fashi da suka iso kan babura riƙe da bindigogi da wasu muggan makamai, a cewar wani fasinja da ya tsere daga harin.

Jirgin ya taso daga tashar Idu da ke Abuja da karfe 6 na yamma kuma an shirya ya isa tashar jirgin Rigasa ta Kaduna da ƙarfe 8 na dare Kamar yadda shaidun gani da ido suka tabbatar, an kai wa jirgin ruwan bama-bamai sau biyu kafin ƴan bindigar ɗauke da makamai su buɗe wuta kan fasinjojin dake cikin jirgin. Duk da cewa an ba da sanarwar ɓacewar fasinjoji 26 a hukumance, ya zuwa ranar 4 ga Afrilu, sama da fasinjoji 150, ba a san inda suke ba.

Kashe-kashe

Sama da mutane sittin (60) ne, aka kashe da suka haɗa da: Amin Mahmoud, shugaban matasa na jam'iyyar All Progressives Congress, APC, Chinelo Megafu Chinelo, likita, Tibile Mosugu, lauya mai tasowa kuma dan babban lauyan Najeriya, Barista Musa Lawal- Ozigi, sakatare-janar, Trade Union Congress, TUC.

Wata likita mai suna Megafu Chinelo ta rasu ne sa’o’i bayan ta bayyana a shafinta na Twitter cewa an harbe ta ne a cikin jirgin ƙasa da ke kan hanyarsa ta zuwa Kaduna. A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar 28 ga Maris, 2022, ƙungiyar likitocin Najeriya (NMA) ta tabbatar da hakan. Chinelo ya wallafa a shafinsa na Twitter jim kaɗan bayan harin da ƴan ta’adda suka kai wa jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna inda ya ce: “Ina cikin jirgin, an harbe ni. Don Allah a yi mini addu’a.”

Hare-hare na baya-bayan nan

Lamarin ya faru ne a cikin rikicin ‘yan bindigan Najeriya kwanaki biyu bayan wani farmaki da ƴan bindiga suka kai a filin jirgin sama na Kaduna, inda aka kashe jami’an hukumar kula da sararin samaniyar Najeriya (NAMA) biyu tare da yin garkuwa da wasu ma’aikata da dama. A cikin Oktoba 2021, NRC ta dakatar da ayyukan kan hanyar a karon farko saboda wannan dalili.

Bayan haka

Bayan harin, sojojin saman Najeriya sun kai samame a dajin da ke kan iyakar jihar Neja da jihar Kaduna, inda suka kashe ‘yan ta’adda ƙasa da su 34, kamar yadda jaridar The Guardian ta ruwaito.

Manazarta

Tags:

Harin Jirgin Ƙasar Abuja-Kaduna LamarinHarin Jirgin Ƙasar Abuja-Kaduna Kashe-kasheHarin Jirgin Ƙasar Abuja-Kaduna Hare-hare na baya-bayan nanHarin Jirgin Ƙasar Abuja-Kaduna Bayan hakaHarin Jirgin Ƙasar Abuja-Kaduna ManazartaHarin Jirgin Ƙasar Abuja-KadunaAbujaKaduna (birni)Kaduna (jiha)NajeriyaNigerian Railway Corporation

🔥 Trending searches on Wiki Hausa / هَوُسَ:

Sankaran NonoHarsunan NajeriyaDuniyaAnnabi SulaimanMa'anar AureAbdulsalami AbubakarPrabhasBangladeshAfirkaBeninYakubu MuhammadMaud DightamAl Kur'aniAhmadu BelloFuntuaZamantakewaTarihin DauraLiberalismAjingiJa'afar Mahmud AdamBobriskyAyilan (ƙasa)IndonesiyaHadiza MuhammadJahar TarabaLibyaSunayen RanakuSadiq Sani SadiqArmeniyaBien HoaAmaryaKano (jiha)MoroccoNafisat AbdullahiJigawaTarayyar AmurkaKabewaMaguzanciYarbanciKarin maganaAbubakar Shehu-AbubakarItaliyaRamy BensebainiCristiano RonaldoGudanar da Sharar gida a IndiaRema (musician)GwargwamiGoron tulaKainuwaBotswanaJerin Sunayen Gwanonin Jihar SokotoRashanciTarihin Hausawa2014Kwara (jiha)FalsafaZuruTumfafiyaMuhammadu BelloMagaryaAhmad S NuhuJennifer UchenduAmica HallenndorffUmmi RahabCiwon sanyiKashin jiniSam DarwishYaƙin BadarZazzabin RawayaAski🡆 More