Rahab Salim wacce aka fi sani da Ummi Rahab ko Ummi Takwara (an haifeta a ranar 7 ga watan Afrilu, shekara ta 2004) a garin Kaduna.
Ƴar wasan kwaikwayo ce a masana'antar fim ta Kannywood 'yar rawa kuma 'yar talla wacce ta auri Jarumi, Furodusa kuma mawakin Hausa, Lilin Baba.
Ummi Rahab | |
---|---|
Rayuwa | |
Cikakken suna | Rahab Salim |
Haihuwa | Kaduna, 7 ga Afirilu, 2004 (19 shekaru) |
ƙasa | Najeriya |
Ƴan uwa | |
Abokiyar zama | Lilin Baba |
Sana'a | |
Sana'a | Jarumi |
An haifi Ummi Rahab a ranar 7 ga watan Afrilu, shekara ta 2004 a cikin garin Kaduna dake arewa maso yammacin Najeriya.
Ummi rahab tayi karatun firamare da sakandire a jihar Kaduna, kafin daga baya ta koma garin Kano domin ci gaba da rayuwar ta.
Ummi Rahab na daga cikin jaruman Kannywood da suka fara taka rawa a wasan kwaikwayo tun suna ƙanana. Ummi Rahab ta fara fitowa a fim tun lokacin tana makarantar firmare, acikin fim din da tayi fice da shi wato "Takwara Ummi". A lokacin tana da shekaru goma a duniya inda ta fito a matsayin diyar Adam A Zango. Ummi Rahab tayi fice a masana'antar fim na Kannywood kuma ta fito a bidiyon waƙoƙin Hausa da dama da suka hada da: Meleri - WUFF Dake.
Ranar 18 ga watan yuni, 2022 Ummi Rahab ta auri Lilin Baba.
This article uses material from the Wikipedia Hausa / هَوُسَ article Ummi Rahab, which is released under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 3.0 license ("CC BY-SA 3.0"); additional terms may apply (view authors). An samar da dukkan muƙaloli a ƙarƙashin lasisin Creative Commons Attribution/Share-Alike; tana yiwuwa wasu ƙa'idoji su yi tasiri. Ku duba Ka'idojin Amfani na Gidauniyar Wiki domin ƙarin bayani. Images, videos and audio are available under their respective licenses.
®Wikipedia is a registered trademark of the Wiki Foundation, Inc. Wiki Hausa / هَوُسَ (DUHOCTRUNGQUOC.VN) is an independent company and has no affiliation with Wiki Foundation.