Bauchi

Bauchi jaha ce dake yankin Arewacin Najeriya tana yankin Arewacin gabashin Najeriya an kirkiri jihar Bauchi ne a watan Fabrairun shekarar ta 1976 daga tsohuwar jihar Arewa maso Gabas ta gwamnatin Janar Murtala Mohammed.

Asali ta hadane da yankin Gombe, wadda ta zama jiha ta daban a shekarar 1996. Tana da kananan hukumomi Ashirin 20. Babban birninta shi ne Bauchi. Jihar Bauchi tana yankin Arewa maso Gabashin Najeriya, tana da fadin murabba'in kilomita 45,837. Jihar Bauchi tana iyaka da Kano da Jigawa daga arewa sai Yobe da Gombe daga gabas sai jihar Kaduna ta yamma da Filato da Taraba a kudu. Gaba daya yankunan yammacin jihar da arewacin kasar suna da tsaunuka, da duwatsu. Hakan ya faru ne sakamakon kusancin jihar da tsaunukan Jos ta jihar Plateau da kasar Cameroun. Jihar Bauchi na daya daga cikin jahohin Arewacin Najeriya da suka mamaye yankunan ciyayi guda biyu, wato Sudan Savannah da Sahel Savannah. Manyan koguna guda biyu ne suka ratsa jihar, kogin Gongola da Hadejia. Yanayin yanayin jihar Bauchi yana da zafi sosai a watannin Afrilu da Mayu, yayin da Disamba da Janairu ne watanni mafi sanyi. Jihar Bauchi na daya daga cikin jahohin Arewacin Najeriya da suka mamaye yankunan ciyayi guda biyu, wato Sudan Savannah da Sahel Savannah. Manyan koguna guda biyu ne suka ratsa jihar, kogin Gongola da Hadejia. Yanayin yanayin jihar Bauchi yana da zafi sosai a watannin Afrilu da Mayu, yayin da Disamba da Janairu ne watanni mafi sanyi. Jihar Bauchi tana da ƙabilu masu yawa, wanda sun kai ƙabilu 55 da suka haɗa da Fulani, Gerawa, Sayawa, Jarawa, Kirfawa, Turawa Bolewa, Karekare, Kanuri, Fa'awa, Butawa, Warjawa, Zulawa, Boyawa MBadawa. Amma Fulani su ne ƙabila mafi Yewa a Jahar,inda suka mamaye kananun hukumomi irinsu Toro, jama'are, giade, darazo, katagum, misau, Alkaleri, dambam, da dai sauran su. Wannan yana nufin cewa suna da asali,da tsarin sana'a, da sauran abubuwa da yawa waɗanda ke cikin kasancewar al'ummar jihar.

BauchiBauchi
Wiki disambiguation page (en) Fassara

ASALIN SUNA

An samo Sunan garin Bauchi ne daga sunan wani Baushe wanda ya kasance jajirtaccen mafarauci a zamaninsa. Baushe shine ya fara zama a Bauchi kafin zuwan Malam Yakubu Sarkin Bauchi na farko. Bauchi a cewar masu fassarar Hausa na farko na nufin “babu wata dabba da ta tsira daga tarko da kibiryar Baushe”. Akwai kamanceceniyar al'adu a tsakanin kabilun jihar, ayyukan sana'a, bukukuwa, sutura da kuma yawan mu'amalar ƙabilanci musamman wajen zaman aure da tattalin arziki. Wasu daga cikin ƙabilun suna da alaƙar barkwanci da ke tsakanin su, misali; Fulani da Kanuri, Jarawa da Sayawa, da sauransu.

TATTALIN ARZIKI

Jihar Bauchi jihar noma ce. Sunada Faɗin ƙasa mai albarka hakan yasa yana ƙara fa'ida ga kayan amfanin gonar da suke samarwa, waɗanda suka haɗa da masara, shinkafa, gero, gyada. Ana yin noma da tallafawa ta hanyar amfani da madatsun ruwa kamar dam na Balanga da sauransu. Haka nan ana kiwon shanu da sauran dabbobi a jihar. Haka kuma jihar tana da masana’antun da suke samar da kayayyakin Amfanin Al'umma na yau da kullum.

YAWAN BUDE IDO

Jihar Bauchi na da albarkar wuraren yawon bude ido da dama. Jihar Bauchi tana da wurin ajiyar Dabbobi na Yankari (mafi girman kiwo a Afirka ta Yamma), Premier Game Reserve, Rock Paintings a Goji da Shira, Gidan Tarihi na jiha Shehu Azare Park Tunga Dutse Wikki Warm Springs Yankari National Park (Game Reserve).

BUKUKUWAN AL'ADA

Amanya Festival Bikin Fasaha da Al'adu na Jahar Bauchi Idin kaciya na mutanen Gezawa Durbar Festival Kokowa and Dambe Festival Lake Efi Fishing Festival Bikin Al'adun Yankari

Bikin Daba (Durbar) babban abin jan hankali ne na shekara-shekara

KANANAN HUKOMOMI

Birnin Bauchi na cikin ƙananan hukumomi ashirin da ke jihar Bauchi:

Bauchi, Tafawa Balewa, Dass, Toro, Bogoro, Ningi, Warji, Ganjuwa, Kirfi, Alkaleri, Darazo, Misau, Giade, Shira, Jamaare, Katagum, Itas/Gadau, Zaki, Gamawa da Dambam.


Manazarta

Tags:

Bauchi ASALIN SUNABauchi TATTALIN ARZIKIBauchi YAWAN BUDE IDOBauchi BUKUKUWAN ALADABauchi KANANAN HUKOMOMIBauchi ManazartaBauchiFulaniKanuriKarekareNajeriyaSana'a

🔥 Trending searches on Wiki Hausa / هَوُسَ:

ZogaleSaddam HusseinTarihin rikicin Boko HaramDuluoTitanicAnnabi IshaqHijira kalandaDaular Kanem-BornuIbrahim NiassBrazilPatricia OkaforIbrahim MandawariSanusi Lamido SanusiMohammed AruwaCiwon hantaYadda Ake Turaren Wuta Na MusammanIman ElmanIbrahim TalbaAhmad Mai DeribeKhalid Al AmeriKunun AyaUmar Abdul'aziz fadar begeCiwon zuciyaFarfaɗiyaJamusDance (Rawa)Jerin Ƙauyuka a Jihar KatsinaMasarautar GombeHannatu MusawaMurja IbrahimTahajjudMoroccoMusbahuISBNFassaraAbdul Rahman Al-SudaisHanafiyyaAdolf HitlerHassan WayamAnnabi MusaFoluke AkinradewoDawaKanjamauFarillai, Sunnoni da Mustahabban AlwallaIshaaqHafsat IdrisHawainiyaMuhammad dan Zakariya al-RaziBoko HaramCutar zazzaɓin cizon sauroSankaran NonoAljeriyaNomaPape Mar BoyeAbujaJima'in jinsiMamayewar Rasha a Ukraine na 2022JiminaOla AinaAljannahJerin ƙauyuka a jihar KebbiBuhariyyaCadiDokiZaben Gwamnan Jihar Kano 2023Mohammed Danjuma GojeKatsina (jiha)WikisourceIbrahim ShekarauMansura IsahBirnin KuduUmmi Rahab🡆 More