Turaren wuta ana yin sa ne da itace, domin turara ɗaki, da dukkanin jiki da na tsugunno, da kuma na sutura.
Ana zuba shi cikin gaushi (garwashi) ne a kasko. Nan da nan kuwa ka ji ƙamshi ya gauraye ko’ina a cikin gida. Daga cikin Itatuwa da ake turare da su kuwa Sun haɗa da:
Icen Sandal
Icen, Hawi
Icen Gab-Gab
Icen Durot Da dai Sauransu.
Larabawa da kuma mutanen Maiduguri ne suka fi shahara wajen amfani da turaren wuta. Mazansu na taimakawa sosai, su siya wa matansu turare akai-akai. A wajensu tamkar dole ne amfani da turare . Mace ba ta da daraja sai da kasancewa cikin ƙamshi a kodayaushe .
Za a sa icen Hawi a turmi a daddaka shi sama-sama. A sa icen gab-gab shima haka. Sai a juye su cikin mazubi. A dauko ruwan turare Matan Arewa a zuba a kan itatuwa. A juye Soyayyen farce. A zuba Misik. Sai a ɗauko turaruka: Alhaji Abdullahi, da salamalekum, da Sasorabia, da 20 fragrances. Kowanne a buɗe a juye. Sai kuma a dauko madarar turare masu matukar ƙamshi a zuba su. A juya da kyau ko’ina ya samu ya haɗe . A samu mazubi a juye a ciki. Kuma a rufe shi sosai.
This article uses material from the Wikipedia Hausa / هَوُسَ article Yadda Ake Turaren Wuta Na Musamman, which is released under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 3.0 license ("CC BY-SA 3.0"); additional terms may apply (view authors). An samar da dukkan muƙaloli a ƙarƙashin lasisin Creative Commons Attribution/Share-Alike; tana yiwuwa wasu ƙa'idoji su yi tasiri. Ku duba Ka'idojin Amfani na Gidauniyar Wiki domin ƙarin bayani. Images, videos and audio are available under their respective licenses.
®Wikipedia is a registered trademark of the Wiki Foundation, Inc. Wiki Hausa / هَوُسَ (DUHOCTRUNGQUOC.VN) is an independent company and has no affiliation with Wiki Foundation.