Damaturu ƙaramar hukuma ce kuma babban birnin jihar Yobe dake arewa maso gabashin Najeriya.
Nan ne hedikwata inda fadar gwamnatin Jihar Yobe take wadda gwamna Mai Mala Buni ke mulkinta a halin yanzu, sannan kuma cibiyar gudanar da mulki na jahar. Masarautar Damaturu, ita ce masarautar gargajiya daya jal ta sarkin yanka mai daraja ta ɗaya a gabadaya fadin birnin. Kebantacciyar lambar akwatin waya na birnin ita ce 620. Karamar hukumar tana da fadin kasa 2,366 2 da yawan jama'a 88,014 a ƙidayar shekara ta 2006. Garin Damaturu yana kan babbar hanyar A3. A alkaluman ilimin zanen kasa, birnin Damaturu ya gindayu ne akan alkaluman kwa'odineto 12°00′00″N 12°00′00″E / 12.00000°N 12.00000°E.
Damaturu | |||||
---|---|---|---|---|---|
| |||||
Wuri | |||||
| |||||
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya | ||||
Jiha | Jihar Yobe | ||||
Babban birnin | |||||
Yawan mutane | |||||
Faɗi | 88,014 lissafi | ||||
• Yawan mutane | 37.2 mazaunan/km² | ||||
Labarin ƙasa | |||||
Yawan fili | 2,366 km² | ||||
Altitude (en) | 371 m | ||||
Bayanan Tuntuɓa | |||||
Kasancewa a yanki na lokaci |
Damaturu ta kasance a matsayin mallaka a lokacin da turawan Ingila suka sassaka ta daga gundumar Alagarno . Hakan ya haifar da mamaye daular Bornu a shekara ta 1902 da sojojin mulkin mallaka karkashin jagorancin Kanar Thomas Morland suka yi.
Damaturu dai ya sha fuskantar hare-haren mayakan jihadi na Boko Haram a yakin da suke yi na kafa daular halifanci a yankin arewa maso gabas.
11°44′40″N 11°57′40″E / 11.74444°N 11.96111°EPage Module:Coordinates/styles.css has no content.11°44′40″N 11°57′40″E / 11.74444°N 11.96111°ETemplate:Yobe State
This article uses material from the Wikipedia Hausa / هَوُسَ article Damaturu, which is released under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 3.0 license ("CC BY-SA 3.0"); additional terms may apply (view authors). An samar da dukkan muƙaloli a ƙarƙashin lasisin Creative Commons Attribution/Share-Alike; tana yiwuwa wasu ƙa'idoji su yi tasiri. Ku duba Ka'idojin Amfani na Gidauniyar Wiki domin ƙarin bayani. Images, videos and audio are available under their respective licenses.
®Wikipedia is a registered trademark of the Wiki Foundation, Inc. Wiki Hausa / هَوُسَ (DUHOCTRUNGQUOC.VN) is an independent company and has no affiliation with Wiki Foundation.