Luka Bulus Madaki; wanda aka fi sani da BOC Madaki (An haifeshi ranar 22 ga watan Satumban shekarar 1993) ɗan Najeriya ne, Marubucin Waƙa, Kuma mawaƙi.
BOC Madaki | |
---|---|
Rayuwa | |
Cikakken suna | Luka Bulus |
Haihuwa | Jihar Bauchi, 22 Satumba 1993 (30 shekaru) |
ƙasa | Najeriya |
Sana'a | |
Sana'a | mai rubuta waka, Masu kirkira da rapper (en) |
Imani | |
Addini | Kiristanci |
An haifi shine ranar 22 ga watan Satumban shekarar 1989 a ƙaramar hukumar Bogoro da ke Jihar Bauchi a matsayin ɗan fari ga iyayensa.
BOC yayi karatunsa na firamare a makarantar gandun daji da Jibril Aminu kafin ya zarce zuwa makarantar sakandaren kwana ta Shadawanka inda ya samu shedar SSCE.
Bayan ya kammala makarantar sakandare, ya kuma cigaba zuwa makarantar kimiyya da fasaha ta Abubakar Tatari Ali inda ya sami difloma ta ƙasa a fannin nazarin muhalli da kula da gidaje.
Ayyukan sa na waƙa ya fara ne daga Coci tare da ƙaramin rukuni na mawaƙa, bayan shafe shekaru yana gwagwarmaya a cikin waƙa, ƙarshe BOC Madaki ya ci gaba a shekarar 2013.
BOC ya zama shahararren mawaƙi a lokacin da ƙungiyar Toss A Popular Music ta sa hannu a wancan lokacin.
Tunda ya shiga harkar waka, BOC ya fitar da wakoki sama da 100 wanda ya gabatar da manyan mawaka na hausa kamar Classiq, DJ AB, Kheengz, Morell da Bash ne pha.
Madaki ƙwararren mai waƙoƙin waƙa ne da kiɗa mai ban sha'awa, waƙoƙin sa suna mai da hankali ga canza rayuwar matasa.
Wasu daga cikin wakokin sa da sukayi fice shine Zafi, Dabarbaru, da dai sauransu kuma yafitar da Album da dama kamar wane album dinshe No English, Sorry Please thanks da dai
This article uses material from the Wikipedia Hausa / هَوُسَ article BOC Madaki, which is released under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 3.0 license ("CC BY-SA 3.0"); additional terms may apply (view authors). An samar da dukkan muƙaloli a ƙarƙashin lasisin Creative Commons Attribution/Share-Alike; tana yiwuwa wasu ƙa'idoji su yi tasiri. Ku duba Ka'idojin Amfani na Gidauniyar Wiki domin ƙarin bayani. Images, videos and audio are available under their respective licenses.
®Wikipedia is a registered trademark of the Wiki Foundation, Inc. Wiki Hausa / هَوُسَ (DUHOCTRUNGQUOC.VN) is an independent company and has no affiliation with Wiki Foundation.