Daular Kanem–Bornu ta kasance daula ce data taɓa kasancewa a inda ayau itace kasar Cadi da Nijeriya.
Masanan ƙasashe larabawa suna kiran daular da Kanem Empire daga ƙarni na 9th har zuwa sanda takasance daular musulunci Bornu (Daular Bornu) a Shekarar 1900. Kanem Empire CE tun daga shekara ta (c. 700 zuwa 1380) takasance ne ƙasashen Chad, Nigeria da Libya. A matuƙar girmar daular ta tattara ƙasashe ba kawai ɗaukacin ƙasar Chad ba, takai har zuwa kudancin ƙasar Libya (Fezzan) da gabashin Nijar, arewa maso gabas din Nigeria da arewacin kamerun. A yayin da Daular Bornu take a shekara ta (1380s zuwa 1893) takasance a inda ake kira ayau arewa maso gabashin Nigeria, wanda tacigaba da girma fiye da daular Kanem, ta tattari kasashen da ayau sune ko kuma suke daga cikin kasashe kamar Chad, Nijar, Sudan, da Cameroon; an samar da’ita daga shekara ta 1380s zuwa shekarar 1893. Farkon tarihin daular an santa ne da jerin masu sarautar ko Girgam matafiyin bincike dan kasar jamus wato Heinrich Barth wanda aka gano a shekarar 1851.
Daular Kanem-Bornu | |||||
---|---|---|---|---|---|
| |||||
Wuri | |||||
| |||||
Babban birni | Njimi | ||||
Yawan mutane | |||||
Harshen gwamnati | harsunan sahara | ||||
Bayanan tarihi | |||||
Mabiyi | Kanem Empire (en) | ||||
Ƙirƙira | 11 century | ||||
Rushewa | 22 ga Afirilu, 1900 |
Kanem takasance a kudancin dake yankin kasuwanci da ake kira wato trans-Saharan trade dake tsakanin garin Tripoli da kuma yankin tabkin Cadi. Baccin mutanen biranen kasar kawai ta tattari harda wasu kungiyoyin al'ummu makiyaya masu amfani da harsuna kamar harshen Teda–harshen Daza (Toubou).
Yadda aka Samu Kanem nada rudani. Wasu tsoffin tarihai sun danganta samuwar Kanem-Bornu da kifewar daular Assyrian Empire c. 600 BC har zuwa arewa maso gabashin tabkin Cadi. amma sai dai nazarcen zamani na goyon bayan cewar samuwar yankin yafi kusanci da shigowar yanciranin.
Daga wani nazarin daya karbu, ansamu cewar masarautar tafara kafuwa ne a shekara ta 700 AD a karkashin makiyayan masu amfani da harshen Tebu-Kanembu. Ance mutanen Kanembu an tursasa sune sukabar yankunansu har zuwa kasar noma dake yankin kudu maso yammacin tabkin Chadi daga matsin siyasa da desiccation a tsohuwar mazauninsu, yankin nada yancin kanta tun asali, walled city-states belonging to the Sao culture. A karkashin mulkin Duguwa dynasty, Kanembu sun mamaye Sao, bawai bayan sun dauki aladun matanen ba. ancigaba da gwabza yaki tsakanin su har zuwa karshen karni na goma sha shida (16th).
Wani nazarin ya nuna cewar batacciyar kasar Agisymba wanda (Ptolemy ya ambata tun a tsakiyar karni na biyu (2nd) AD) itama mafiriyar daular Kanem din ce.
This article uses material from the Wikipedia Hausa / هَوُسَ article Daular Kanem-Bornu, which is released under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 3.0 license ("CC BY-SA 3.0"); additional terms may apply (view authors). An samar da dukkan muƙaloli a ƙarƙashin lasisin Creative Commons Attribution/Share-Alike; tana yiwuwa wasu ƙa'idoji su yi tasiri. Ku duba Ka'idojin Amfani na Gidauniyar Wiki domin ƙarin bayani. Images, videos and audio are available under their respective licenses.
®Wikipedia is a registered trademark of the Wiki Foundation, Inc. Wiki Hausa / هَوُسَ (DUHOCTRUNGQUOC.VN) is an independent company and has no affiliation with Wiki Foundation.