Najeriya Asaba

Asaba Birni ce, a cikin jihar Delta, a cikin Najeriya.

Tana nan daga yammacin gabar rafin Niger, ta karamar hukumar Oshimili South. Asaba na da yawan jama'a kimanin mutum 149,603 a kiadayar shekara ta 2006, da yawan mutane a birnin kimanin mutum dubu dari biyar.

Najeriya AsabaAsaba
Najeriya Asaba

Wuri
Najeriya Asaba
 6°11′00″N 6°45′00″E / 6.1833°N 6.75°E / 6.1833; 6.75
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya
JihaDelta
Babban birnin
Yawan mutane
Faɗi 149,603
• Yawan mutane 558.22 mazaunan/km²
Labarin ƙasa
Yawan fili 268 km²
Altitude (en) Fassara 180 ft
Bayanan tarihi
Ƙirƙira 1884
Bayanan Tuntuɓa
Lambar aika saƙo 320241
Kasancewa a yanki na lokaci
Tsarin lamba ta kiran tarho 056
Wasu abun

Yanar gizo asaba.com
Najeriya Asaba
Wurin Asaba a cikin Najeriya
Najeriya Asaba
Asaba.
Najeriya Asaba
Asaba roundabout delta state

An san birnin Asaba da mu'ala iri-iri musamman a dalilin wuraren shakatawa da otel-otel dake garin, gidajen rawa, swuraren kallo na sinima, da wuraren shahulgula iri-iri. Akwai biki da ake gabatarwa duk shekara a garin wanda ake kira Delta Yaddah, ana tara mawaka a taron bikin. Ta'addanci yayi yawa a birnin saboda yawan jama'arta. Ta'addanci sun hada da yankan aljihu, kwace da sauransu. Akwai tsadar rayuwa a garin saboda mutane daga kasashen waje dake shigowa birnin. Gadar Onitsha itace iyaka tsakanin jihar Delta da Anambra, gadar ita ta raba Asaba da Onitsha.

Asalin Kalma

Kalmar Asaba ta samo asali ne daga kalmar Ahabam ma'ana "Na zaba da kyau" ko kuma "I have chosen well" da turanci, kalmar da aka hakayo daga Nnebisi, wanda shine asalin wanda ya samar da Asaba. Mafi akasarin mutanen Asaba inyamurai ne.

Tarihi

Birnin Asaba ta kasance a da babban birnin yankunan mulkin Turawa na kudanci Najeriya wato Southern Nigeria Protectorate. An samar da birnin a shekara ta 1884. A tsakanin 1886 da 1900, ita ke dauke da kamfanin Royal Niger Company, wanda turawa suka kafa don habaka kasuwanci da fitar da kaya zuwa kasashen turai. Wannan kamfanin a yau shi ake kira da UAC Nigeria PLC. Matafiyin neman ilimi dan Faransa William B. Balkie, lokacin da yake waken yarjejeniyar kasuwanci da shugaban inyamurai Ezebogo a Asaba a ranar August 30, 1885, "Bayan gaisuwar mu, ina magana akan abota, ta kasuwanci, da ilimi, da kuma mafi muhimmanci akan sharrin yaki, da amfanin zaman lafiya, wanda duka anyi maraba da su".

Dangane da fitaccen tarihin Asaba da kuma labarin kasar ta, da kuma tasirinta a Najeriya ta fuskar siyasa da kuma kasuwanci, Ana yi wa Asaba lakabi da cibiyar yankin Anioma.

Labarin Kasa

Asaba na kan wani bisa kwarin rafin Niger, daura da Rafin Anambara. A bayan wadannan rafuka akwai kurgunmin daji mai tarin itace. A tarihance wannan rafin Niger River ya kasance cibiyar sufuri tsakanin kasashen Afurka har zuwa tekun Atlantic Ocean. Asaba ta hada mahada tsakanin yammaci, gabaci da arewacin Najeriya hanyar rafin River Niger daga arewa da kuma gadar Rafin Niger, wanda yake gabas-maso-yammacin yankin kuma babban tambari ne na Najeriya.

Asaba na nan daga degree6 daga arewacin equator, sannan tana da nisan iri daya daga meridian sannan tana da nisan kusan kilomita 160km (mil 100) daga arecin inda ruwan rafin Niger ke gangarawa cikin tekun Atlantic Ocean. Asaba ta mamaye fili mai fadin 300kmsq. Tana da zafi na kimanin 32c a lokaci na rani, sannan da matsakaicin adadin ruwan sama na kimanin millimitoci 2,700m (106 in) a lokacin damuna.

Babban birnin Asaba ya hada sauran makwabtan garuruwa kamar as Igbuzo, Okpanam, Oko, Okwe and Ugbolu wanda ke yankin yammacin River Niger.

Ala'adu

Al'adun Asaba sun ta'allaka kwarau da gaske da soyayyar su ga "Asagba of Asaba", wanda shuwagabanninsu (da ake kira da "Diokpa”) na duka kauyukan garin guda biyar ke kai wa kukansu game da abun da ya shafi mutanen garin. Iyasele na Asaba [Iyase] ke taimakawa wa Asagba wanda shine matsayin prime minista na gargaijya kuma shugaban dattijai [Kamar [Olinzele, Otu Ihaza, Oloto, da dai sauransu.]

Jama'a

Inyamuarai suka kwashe kaso 63% na mutanen garin, kuma mafi akasarin su haifaffun birnin Asaba ne. Asaba ta habaka ta fannin yawan mutane da kusan rabin miliyan (500,000) tun daga lokacin da ta zamo babban birnin Delta. A yanzu ta tara mutane iri-iri wanda ba 'yan asalin birnin bane. Wasu daga cikin yarukan da ke zama a birnin sun hada da Urhobo, Isoko, Ijaw, Hausa, Itsekiri da kuma Yabawa.

Tattalin arziki

Asaba cibiyar gudanarwa ce kuma mazaunin gwamnati wanda aka samar da ita a lokacin kamfanin Royal Niger Company a yanzu (UACN), kuma itace babban birnin gudanarwa na jihar Delta. A dalilin hakan mafi akasarin mutanen birnin ma'aikatan gwamnati ne. Gwamnatin Najeriya a karkashin mulkin gwamnatin Samuel Ogbemudia suka samar da kamfanin Asaba Textile Mills da kuma kamfanin wutar Lantarki na Asaba. A birnin Asaba akwai kamfanoni dake sarrafa magunguna sannan akwai kamfanin sarrafa karafuna. Akwai masu zuwa yawan bude idanu da yawa cikin garin, wannan ya jawo habakar kasuwancin wuraren shakatawa da otel-otel.

Kasuwanni

Akwai manya-manyan kasuwanni guda uka a Asaba wanda suka hada da: kasuwar Ogbe-Ogonogo, kasuwar Cable Point, da kuma kasuwar Infant Jesus.

Wasanni

Filin wasan kwallon kafa na Stephen Keshi Stadium na Asaba, wacce ke da budadden gaba saboda masu kallo daga gari ya dauki nauyin wasanni kwallon kafa da dama tun lokacin da aka gyara ta a karkashin mulkin Senator Dr. Ifeanyi Arthur Okowa, tare da amincewar tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo. Filin shine matsayin filin wasanni na gida na kungiyar kwallon kafa na Delta Force FC.

Sufuri

Jirgin sama

Za'a iya ziyarta birnin Asaba da sauran biranen kewaye ta hanyar filin jirgin sama na Asaba international Airport.

Titin Mota

Babban titin Asaba zuwa Benin titi ne mai matukar muhimmanci saboda shi ya hada garuruwan yammaci da gabacin Najeriya. Sanna har wa yau akwai titin da ya hada Asaba da Ughelli, sannan titin Asaba-Ebu ya hada Asaba da arewacin Najeriya.

Ruwa

Ana iya zirga-zirga ta ruwa a birnin Asaba ta rafin River Niger, wacce ta zagaye yawancin garuruwan Afurka.

Sanannun Mutane

Hotuna

Kara dubawa


Hanyoyin hadin waje

Template:Igbo topics Template:Cities in Nigeria


Manazarta

Tags:

Najeriya Asaba Asalin KalmaNajeriya Asaba TarihiNajeriya Asaba Labarin KasaNajeriya Asaba AlaaduNajeriya Asaba JamaaNajeriya Asaba Tattalin arzikiNajeriya Asaba WasanniNajeriya Asaba SufuriNajeriya Asaba Sanannun MutaneNajeriya Asaba HotunaNajeriya Asaba Kara dubawaNajeriya Asaba Hanyoyin hadin wajeNajeriya Asaba ManazartaNajeriya AsabaDelta (jiha)Najeriya

🔥 Trending searches on Wiki Hausa / هَوُسَ:

RFI HausaUmar Abdul'aziz fadar begeEniola AjaoƊan wasaAbubakar AuduMotsa jikiJerin ƙauyuka a jihar JigawaGoogleSadiya Umar FarouqAlhaji Muhammad Adamu DankaboSafiya MusaDaular SokotoMaleshiyaNatalie FultonHadarin Jirgin sama na KanoJanabaTarihin Annabawa da SarakunaHabbatus SaudaDiana Hamilton (makaɗiya)Mala`ikuAlhusain ɗan AliKareHauwa WarakaBayajiddaZumunciSarakunan Saudi ArabiaTogoHussain Abdul-HussainWudilSadarwaSheikh Ahmad Abulfathi AlyarwaweeMasarautar Sarkin Musulmi, SokotoRuwaRimiYaƙiSulluɓawaAmfanin Man HabbatussaudaHolandDodon kodiSani Musa DanjaAisha NajamuMuhammadJamusJerin kasashenAbdullahi Umar GandujeMikiyaSallar Matafiyi (Qasaru)RashaBet9jaAminu KanoTumatirYankin Arewacin NajeriyaDawakin TofaMutanen NgizimLittattafan HausaTanya SeymourTarihin AmurkaCiwon hantaJamhuriyar Najeriya ta farkoFati MuhammadƘarama antaTanzaniyaBayanauMarta (mai wasan ƙwallon ƙafa)Garba Ja AbdulqadirTinsel (TV series)NgazargamuMalmoSaudiyyaBorisAfirka ta YammaSalman KhanGumelUwar Gulma (littafi)🡆 More