Wankan Janaba ((الغسل الجنابة)) A Musulunci shi dai wankan Janaba ba kamar wankan da muke yi ba ne na yau da kullun ba, shi yana da kuma ka'idoji da yadda ake yin shi kamar yadda ya zo a littafan addinin Musulunci, kamar su Fiqhu da dai sauran su.
Janaba | |
---|---|
Islamic term (en) da Sufi terminology (en) |
awa ne tun daga sanda ka dauki ruwanka mai Tsarki.
tsarki, idan abin da ruwan ya ke a ciki mai budadden baki ne sai a ajiye shi a bangaren hannun dama, idan kuma mai rufaffen baki ne sai a sashi a hannun hagu (kamar buta).
wato BISMILLAH (amma a zuci, saboda ba a ambaton sunan Allah a yayin da ake cikin bandaki). Sannan a wanke hannu kafin a fara komai sau uku (3)
yin niyya ace "Nayi niyyar yin wankan janaba, Farilla, domin na gusar da babbar dauda(نويت غسل الجنابة فرض رفع الحدث أكبر)." (ita ma niyyar a zuci. Idan ma ba a fada ba, ba laifi, don niyya tana farawa tun daga sanda aka dauki abin wankan, buta ko bokiti da sauransu).
wankewar gaba da kuma kewayensa). Bayan wannan sai ayi alwala shudi dai-dai, idan an gama ana iya jinkirta wankin kafafu sai a karshen wanka.(amma malamai sun ce an hana barin sunnah a cikin yin wanka, barin sunnah makaruhi ne, an qishi, ana so musulmi ya yi wanka cikakke tare da farillan wanka da kuma sunnonshi). Kun ga kenan alwalar mu zamu yi ta ne cikakkiya kamar zamu yi Sallah.
uku, za a shigar har da wuya a wankin kai, da wankin kunnuwa ciki da waje, mace kuma zata zuba ruwa a cikin gashinta ta bubbuga sai ruwan ya shiga ciki sosai. Amma idan tana da larura to anso ta shafa kanta sau ukun ko ina da ina.
na dama tun daga kafada har zuwa kafa, sannan a wanke tsagin jiki na hagu shima tun daga kafada har kafa. a cuccuda sosai da sosai.
Ana so ko ina ya shafi ruwa kamar su matsematsin cinyoyi,da kuma kwarin cibiya duk a tabbatar an cudasu da kyau.Sannan a kula kada a shafi Al'aura don kada alwalar ta karye, (idan ana nufin yin amfani da ita). Domin za'a iyayin Sallah da wannan Alwalar da aka yi wanka da ita, sallah ta inganta.Amma idan bayan wankan aka taba al'aura to sai an sake alwala. Domin shafar farji ko gaba na warware alwalar wanka.
A yi kokari a kiyaye da barin lam'a wato shi ne wani dan karamin wuri a jiki wanda zai zama ruwa bai shafe shi ba, sai a kiyaye. Wankan Janaba ya kammala.
Allah shi ne mafi sani
Kuma Mai tausayin bayinsa
This article uses material from the Wikipedia Hausa / هَوُسَ article Janaba, which is released under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 3.0 license ("CC BY-SA 3.0"); additional terms may apply (view authors). An samar da dukkan muƙaloli a ƙarƙashin lasisin Creative Commons Attribution/Share-Alike; tana yiwuwa wasu ƙa'idoji su yi tasiri. Ku duba Ka'idojin Amfani na Gidauniyar Wiki domin ƙarin bayani. Images, videos and audio are available under their respective licenses.
®Wikipedia is a registered trademark of the Wiki Foundation, Inc. Wiki Hausa / هَوُسَ (DUHOCTRUNGQUOC.VN) is an independent company and has no affiliation with Wiki Foundation.