Mohammed Aamir Hussain Khan (an haifeshi a ranar 14 ga watan Maris shekarar 1965), jarumi ne a masana'antar finafinai ta kasar Indiya, kuma darakta, maishirya fim kuma sananne a gabatar da shirin talabijin.
Ya kwashe sama da shekaru talatin a masana'antar Bollywood, Khan ya ayyana kansa a matsayin fitacce kuma babban jagora a masana'antar ta Bollywood. Yana da masoya masu yawan gaske musamman ma a Indiya da Sin, kuma jaridar Newsweek ta aiyanashi da babban tauraro, a duniya. Amir Khan ya samu kyaututtuka da lambobin yabo masu dimbin yawa, daga ciki akwai Filmfare Awards, hudu, National Film Awards da AACTA Awards, harma ma ta Academy Award. Gwamnatin Indiya ta girmama shi da kyautar Padma Shri a shekarar 2003 da kuma Padma Bhushan a shekarar 2010, sannan ya samu lambar girmamawa daga gwamnatin kasar Sin a shekarar 2017.
Amir Khan | |||
---|---|---|---|
| |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Mumbai, 14 ga Maris, 1965 (59 shekaru) | ||
ƙasa | Indiya | ||
Ƴan uwa | |||
Mahaifi | Tahir Hussain | ||
Abokiyar zama | Reena Dutta (en) (18 ga Afirilu, 1986 - Disamba 2002) Kiran Rao (en) (28 Disamba 2005 - 2 ga Yuli, 2021) | ||
Yara | |||
Ahali | Faisal Khan (en) , Nikhat Khan (en) da Farhat Datta (en) | ||
Karatu | |||
Makaranta | Bombay Scottish School (en) St. Anne's High School, Bandra (en) Narsee Monjee College of Commerce and Economics (en) | ||
Harsuna | Harshen Hindu Urdu Turanci | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan wasan kwaikwayo, darakta, mai tsara fim, marubin wasannin kwaykwayo, mai gabatarwa a talabijin da producer (en) | ||
Kyaututtuka | gani
| ||
Wanda ya ja hankalinsa | B. R. Ambedkar | ||
Imani | |||
Addini | Musulunci | ||
IMDb | nm0451148 |
Farko Amir Khan ya fara baiyana fuskar sa akwatin talabijin yana dan shekara takwas a cikin fim din kawun sa Nasir Hussain mai suna Yaadon Ki Baaraat a shekarar (1973). Fim din sa na farko bayan girmansa shine Holi a shekarar (1984), sannan ya fara fita a matsayin cikakken jarumi a fim din soyayya na Qayamat Se Qayamat Tak a shekarar (1988). Kwazon da ya nuna a fim din Raakh a shekarata (1989) ya saka shi ya samu kyautar National Film Award. Bayan karin samun karbuwar fina finan sa da kuma samun nasarorin da yayi a shekarun a shekarar 1990, sai Amir Khan ya aiyana kansa da daya daga cikin na gaba gaba na masana'antar finafinai ta Indiya. Hakan yafarune bayan samun karbuwar fina finan sa kamar DilWanda akayi a shekarar (1990) da Raja Hindustani shekarar (1996) da kuma Sarfarosh a shekarar (1999).
This article uses material from the Wikipedia Hausa / هَوُسَ article Amir Khan, which is released under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 3.0 license ("CC BY-SA 3.0"); additional terms may apply (view authors). An samar da dukkan muƙaloli a ƙarƙashin lasisin Creative Commons Attribution/Share-Alike; tana yiwuwa wasu ƙa'idoji su yi tasiri. Ku duba Ka'idojin Amfani na Gidauniyar Wiki domin ƙarin bayani. Images, videos and audio are available under their respective licenses.
®Wikipedia is a registered trademark of the Wiki Foundation, Inc. Wiki Hausa / هَوُسَ (DUHOCTRUNGQUOC.VN) is an independent company and has no affiliation with Wiki Foundation.