Ahmed Usman

Ahmed Usman (An haifeshi a shekara ta 1951 - 14 ga watan Afrilu, 2019).

Ya kasance tsohon gwamnan jihar Ondo ne.

Farkon Rayuwa da Aiki

An haifi Ahmed Usman a shekarar 1951 kuma ya girma a Okura-Lafia, ƙaramar hukumar Dekina, Jihar Kogi. Bayan shiga aikin soja, muƙamai sun hada da Bataliya ta biyu, Bataliya ta 192, Abak da Bataliya ta 141, Kano (1983-1985), Rundunar Majalisar Ɗinkin Duniya a Lebanon (1985-1986) da Bataliya Kwamanda G Amphibious, Elele Port Hartcourt (1990-1991).

Gwamnan jihar ondo

An naɗa Usman, gwamnan jihar Ondo a watan Satumba 1994. Yayin da gwamnan jihar Ondo, Usman ya ɗora Oba Adeleye Orisagbemi a matsayin Attah na Ayede Ekiti. Yayin da ake nuna damuwa game da ayyukan kungiyar asiri a jihar, a ranar 17 ga watan Yunin 1996, Usman ya yi barazanar korar duk wani alkalin jihar Ondo da ya bayar da belin wadanda ake zargi da kungiyar asiri. A shekarar 1998, Adeoluwa Oyerinde, tsohon Manajan Darakta na wani reshen Kamfanin Inbestment na Odu’a, ya yi zargin cewa ya bayar da cin hanci ga Usman da wasu gwamnonin soji a lokacin da Usman ke riƙe da mulki a Jihar Ondo.

Gwamnan jihar Oyo

Watan Agustan 1996 ne aka tura Usman jihar Oyo domin ya zama gwamna a daidai lokacin da ake ƙara nuna rashin jin dadi game da mulkin soja ƙarƙashin jagorancin Sani Abacha. A ranar 12 ga Mayun 1997, wani bam da ya tashi a babban birnin jihar Ibadan ya raunata sojoji biyu da dan sanda guda. Usman yace waɗanda suka aikata wannan aika aika matsorata ne. An kashe mutane biyu tare da raunata kusan 20 a filin wasa na Salami da ke Ibadan a watan Afrilun 1998, lokacin da magoya bayan ƙungiyar United Action for Democracy (UAD) suka tarwatsa taron magoya bayan Abacha da Kanar Usman ya yi jawabi a baya.An kashe mutane bakwai a ranar Mayun 1998 a arangama tsakanin 'yan sanda da masu zanga-zangar neman dimokaraɗiyya. Usman ya zargi "makiya kasashen waje" da goyon bayan tashin hankalin. A cikin wannan watan ne Usman ya ce an sanya jami’an tsaro jajircewa domin dakile duk wata zanga-zanga a babban birnin jihar Ibadan. Bayan ‘yan kwanaki, an kama ‘yan Nijeriya 37, aka tuhume su da laifin yin zagon ƙasa, ciki har da malami kuma shugaban jam’iyyar Democratic Coalition na Jihar Oyo, Lam Adesina, wanda daga baya ya zama Gwamnan Jihar a shekarar 1999. Usman ya ce za a ɗauke su a matsayin fursunonin yaki. An tuhumi wasu mutane uku, daya fitaccen editan jarida ne da laifin yin zagon kasa. Sani Abacha ya rasu a watan Yunin 1998, sannan Usman ya sauke shi daga muƙamin gwamna a watan Agustan 1998.

Bayan mulkin soja

Dawowar mulkin dimokaraɗiyya a 1999 Usman ya shiga kasuwanci na zaman kansa kuma bai shiga harkar siyasa ba har sai a watan Agustan 2008, inda ya bayyana cewa yana da niyyar tsayawa takarar gwamnan jihar Kogi a 2011. Da yake takara a ƙarƙashin jam’iyyar PDP, ya sha kaye a zaɓen fidda gwani na jam’iyyar. Daga baya ya nuna sha’awarsa ta tsayawa takara a zaɓen gwamnan jihar Kogi a 2019 shi ma, a jam’iyyar All Progressives Congress, amma a ƙarshe bai shiga takara ba.

Rasuwa

Usman ya rasu ne a ranar 14 ga Afrilu, 2021 yana da shekaru 69 a Jos, Jihar Filato, sakamakon rashin lafiya. An dawo da gawarsa garinsu na Okura-Lafia a jihar Kogi domin yin jana'izar Musulunci. Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ya mika ta'aziyyar rasuwar Usman.

Manazarta

Tags:

Ahmed Usman Farkon Rayuwa da AikiAhmed Usman Gwamnan jihar ondoAhmed Usman Gwamnan jihar OyoAhmed Usman Bayan mulkin sojaAhmed Usman RasuwaAhmed Usman ManazartaAhmed Usman

🔥 Trending searches on Wiki Hausa / هَوُسَ:

Yusuf Baban CineduJerin ƙauyuka a jihar KadunaIsah Ali Ibrahim PantamiIlimiBOC MadakiShuwa ArabTarihin falasdinawaEnku EkutaBilkisuCadiAhmed Muhammad DakuWilliams UchembaKunun AyaMasaraJahar TarabaMaliHadisiRashaPrabhasTafasaMuhammadu DikkoOla AinaTumfafiyaAlamomin Ciwon DajiRabi'a ta BasraMalawiAsturaliyaNumidia LezoulAgnès TchuintéCelene IbrahimSojaIndustrial RevolutionIbn TaymiyyahSaddam HusseinZaben Gwamnan Jihar Kano 2023FulaniRabi'u RikadawaAbdullahi Bala LauIstiharaBuhariyyaAsabe MadakiSana'oin ƙasar HausaHassan WayamMaitatsineHassana MuhammadGmailMutuwaShehu ShagariKarin maganaBiologyChioma OnyekwereDDG (rapper)KenyaMesopotamiaJinin HaidaAmarachi UchechukwuPotiskumYusuf (surah)NapoleonƘur'aniyyaAfirkaWikipidiyaObi MadubogwuIlimin halin dan AdamAishwarya RaiKitsoMusaAnnabi SulaimanWahayiYehya BundhunMasarautar NajeriyaYewande Omotoso🡆 More