Adarawa (kuma Eda da Kadara ), ƙabilu ne a yankin Tsakiyar Najeriya da ke magana da yaren Adara, harshen Arewacin Filato na Najeriya.Mr.
Dio Awemi Maisamari shine shugaban kungiyar mutanen adara watau Adara Development Association (ADA) tare da kuma mataimakin sakatare Luke Waziri.
Yankuna masu yawan jama'a | |
---|---|
Najeriya |
Wasu kimantawa suna sanya yawan mutanen Adara a kusan 381,000.
Kimanin kashi 55% na Adara Kiristoci ne yayin da wasu kuma suke bin addinin Islama.
Ana iya sumun mutanen Adara a yankunan kusa da sahara na Afurka amma a Najeriya kadai ake iya samun asalin su. Ana iya samunsu kuma a Jihar Benue da wasu sassan jihar Kaduna kamar kananan hukumomin Kajuru da Kachia dake jihar Kaduna.Unguwanninsu kuma sun hada da suMagunguna, Idazo, Ungwan Galadima, Ungwan Guza, Etissi, Ungwan Ma’aji, Ungwan Dantata, Ungwan Araha 1 & 2, Ungwan Goshi, Ungwan Shaban, Ungwan Jibo, Ungwan Maijama’a, Ungwan Sako, Ungwan Maidoki and Ungwan Masaba.
Al’umar Adara sun wahala daga rikice-rikicen kabilanci da ke faruwa a Nijeriya, musamman rikice-rikicen makiyaya da manoma a Najeriya, ciki har da na Jihar Kaduna .
This article uses material from the Wikipedia Hausa / هَوُسَ article Adarawa, which is released under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 3.0 license ("CC BY-SA 3.0"); additional terms may apply (view authors). An samar da dukkan muƙaloli a ƙarƙashin lasisin Creative Commons Attribution/Share-Alike; tana yiwuwa wasu ƙa'idoji su yi tasiri. Ku duba Ka'idojin Amfani na Gidauniyar Wiki domin ƙarin bayani. Images, videos and audio are available under their respective licenses.
®Wikipedia is a registered trademark of the Wiki Foundation, Inc. Wiki Hausa / هَوُسَ (DUHOCTRUNGQUOC.VN) is an independent company and has no affiliation with Wiki Foundation.