Mujiya tana daga cikin jinsin tsuntsuyewadda take da matsakaicin girma, tana da manyan idanuwa.
Ƴan'uwanta tsuntsaye, da suke cin nama sune kamar shaho, Angulu da dai sauran su. Sai dai duk da girman idanunta bata gani da rana, shiyasa ma bata yawo sai da dare, saboda idan ta fito da rana tsuntsaye da sauran dabbobi zasu kashe ta, don kuwa basa shiri ko misƙala zarratin. Itama mujiya bata barin su (tsuntsaye) da sauran ƙananan dabbobi irin su Ƙadangare saboda tana farautar su da dare tana cinye su. Akwai wani kalan kuka da mujiya take yi da dare, to idan har tayi kalan kukan dole ko wane tsuntsu ya nemi mafaka. Haka masana sun bayyana cewar ita mujiya tana Kuma da gira har guda uku (3) ta farko tana amfani da ita wajen goge ido, haka akwai wadda take ƙyafta ido, sai kuma girar da mujiya take bacci da ita, shi ya haɗa gira uku kenan. Wasu kuma suna asiri da mujiya kamar ƴan indiya. Haka kuma a ƙasar Hausa a na yin wani karin magana wai "Reshe ya juye da mujiya" .
Mujiya | |
---|---|
Scientific classification | |
Kingdom | Animalia |
Subkingdom | Eumetazoa (en) |
Phylum | Chordata |
Class | Aves |
Superorder | Neoaves (en) |
order (en) | Strigiformes Wagler, 1830 |
Geographic distribution | |
General information | |
Babban tsaton samun abinci | European rabbit (en) |
This article uses material from the Wikipedia Hausa / هَوُسَ article Mujiya, which is released under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 3.0 license ("CC BY-SA 3.0"); additional terms may apply (view authors). An samar da dukkan muƙaloli a ƙarƙashin lasisin Creative Commons Attribution/Share-Alike; tana yiwuwa wasu ƙa'idoji su yi tasiri. Ku duba Ka'idojin Amfani na Gidauniyar Wiki domin ƙarin bayani. Images, videos and audio are available under their respective licenses.
®Wikipedia is a registered trademark of the Wiki Foundation, Inc. Wiki Hausa / هَوُسَ (DUHOCTRUNGQUOC.VN) is an independent company and has no affiliation with Wiki Foundation.