Babban Masallacin Makkah (da larabci; ٱلْـمَـسْـجِـد ٱلْـحَـرَام a furucci; al-Masjid al-Ḥarām a ilimance; Masallaci mai Tsarki, da turanci; The Sacred Mosque)) shine masallacin daya zagaye Kaaba dake birnin Mecca, Saudiya.
Wuri ne na ziyara domin aikin hajji, wanda kowane Musulmi dole ya aikata shi, karanci sau daya a rayuwarsa idan yana da ikon zuwa, wanda aikin yahada da kewaye dakin Kaaba dake a cikin masallacin. Kuma nan muhimmin wurin yin ‘Umrah, karamin aikin hajji da akeyi a kowane lokaci a cikin shekara. Babban masallacin yahada da wasu mahimman wurare, wadanda suka hada da, Baƙin Dutse, Rijiyar ZamZam, wurin tsayuwar annabi Ibrahim, da duwatsun Safa da Marwa. A bude Masallacin yake, akowane lokaci da yanayi.
Masjid al-Haram | |
---|---|
المسجد الحرام | |
Wuri | |
Ƴantacciyar ƙasa | Saudi Arebiya |
Province of Saudi Arabia (en) | yankin Makka |
Tourist attraction (en) | Makkah |
Coordinates | 21°25′21″N 39°49′34″E / 21.4225°N 39.8261°E |
History and use | |
Grand Mosque Seizure | |
| |
Aikin Hajji | |
| |
Umrah | |
| |
Start of manufacturing | 630 |
Addini | Musulunci |
Maximum capacity (en) | 820,000 |
Karatun Gine-gine | |
Style (en) | Islamic architecture (en) |
Tsawo | 137.5 m |
Parts | Hasumiya: 9 |
Offical website | |
|
Babban Masallacin harami shine masallaci mafi girma a duniya, kuma anmasa gyararraki da faɗaɗa shi a lokuta daban-daban a shekaru. Ta wuce lokuta da dama ƙarƙashin kulawar Halifofi daban-daban, sultans da sarakuna, kuma ayanzu babban masallacin na ƙarƙashin kulawar Sarkin Saudi Arabia wanda shine Custodian of the Two Holy Mosques. Tana nan ne a gaban Abraj Al Bait, mafi tsayin ginin agogo a duniya, aikin gininsa dake cike da cece-kuce akan rushe wuraren tarihi na farkon musulunci da gwamnatin Saudiya tayi.
This article uses material from the Wikipedia Hausa / هَوُسَ article Masjid al-Haram, which is released under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 3.0 license ("CC BY-SA 3.0"); additional terms may apply (view authors). An samar da dukkan muƙaloli a ƙarƙashin lasisin Creative Commons Attribution/Share-Alike; tana yiwuwa wasu ƙa'idoji su yi tasiri. Ku duba Ka'idojin Amfani na Gidauniyar Wiki domin ƙarin bayani. Images, videos and audio are available under their respective licenses.
®Wikipedia is a registered trademark of the Wiki Foundation, Inc. Wiki Hausa / هَوُسَ (DUHOCTRUNGQUOC.VN) is an independent company and has no affiliation with Wiki Foundation.