Hadiza Aliyu: 'Yar fim

Hadiza Aliyu wacce akafi sani da Hadiza Gabon (An haife ta ranar ɗaya 1 ga watan Yuni, 1989) a ƙasar Gabon, Hadiza Aliyu ta Kasance Shahararriyar 'yar wasan kwaikwayo ce a Hausa film a Najeriya, a ƙarƙashin masana'antar film ta Hausa kannydwood.

Hadiza Aliyu: Farkon Rayuwa, Ilimi, Shahara
Hadiza Aliyu: Farkon Rayuwa, Ilimi, Shahara Mukala mai kyau

Hadiza Aliyu: Farkon Rayuwa, Ilimi, Shahara Hadiza Aliyu
Hadiza Aliyu: Farkon Rayuwa, Ilimi, Shahara
Rayuwa
Cikakken suna Hadiza Aliyu
Haihuwa Libreville, 1 ga Yuni, 1989 (34 shekaru)
ƙasa Najeriya
Mazauni Kaduna
Harshen uwa Hausa
Fillanci
Karatu
Harsuna Turanci
Hausa
Larabci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a Jarumi
Imani
Addini Musulunci
IMDb nm8040689
hadizaaliyu.com
Hadiza Aliyu: Farkon Rayuwa, Ilimi, Shahara

Farkon Rayuwa

An haifi Hadiza Aliyu Gabon ne a ƙasar Libreville da ke ƙasar Gabon, ta dawo kasar mahaifiyar ta Najeriya daga bisani domin wasu dalilai, inda tayo karatu, sannan ta fara harkan fim, Haifaffiyar garin Libreville, Jamhuriyar Gabon, Hadiza Aliyu ‘yar gidan Malam Aliyu ne wanda dattijo ne. A ɓangaren mahaifinta, Hadiza 'yar asalin ƙasar Gabon ce, kuma a bangaren mahaifiyarta, asalin ta Fulani ce daga jihar Adamawa, Najeriya.

Ilimi

Hadiza Aliyu ta halarci makarantun firamare da sakandiri a ƙasar haihuwarta inda ta rubuta jarabawarta ta A-Level tare da burin zama lauya sannan daga baya ta zabi Lauya a matsayin kwas din da ta fi so. Ta fara karatun jami'a a matsayinta na daliba, amma dole ta daina zuwa makaranta saboda wasu matsaloli da suka dabaibaye karatun nata . Karatun nata ya tsaya a lokacin kuma hakan ya ba ta damar halartar shirin difloma a cikin Harshen Faransanci kuma daga baya ta zama malama mai koyar da Faransanci a wata makarantar sirri.

Shahara

Tana daya daga cikin manyan jarumai mata a masana'antar fim ta kannywood, dake arewacin nigeria. Tana da masoya da dama , tayi fina finai shaharrru a masana'antar. Ta fito a fim mai dogon zango na tashar Arewa 24 mai suna GIDAN BADAMASI, ta kuma fito a shahararren fim mai dogon zango MANYAN MATA. A halin yanzu ta bude wani filin tattaunawa da manyan mutane Sannan nu mai suna GABONS ROOM TALK.

Fim

Hadiza Aliyu ta shiga Kannywood ba da dadewa ba bayan ta shigo daga Gabon zuwa jihar Adamawa, Najeriya . Ta tashi daga Adamawa zuwa Kaduna yayin da take sha'awar shiga masana'antar fim ta kannywood tare da dan uwan ta. Ta samu damar ganawa da Ali Nuhu kuma ta nemi taimakonsa don kaddamar da ita a matsayin 'yar fim. Hadiza ta fara fitowa ne a shekara ta 2009, inda aka sanya ta a Artabu, ta samu shiga masana'antar fim ta kannywood a matsayin daya daga cikin manyan jarumai mata tare da taimakon Ali Nuhu da kuma jagorancin Aminu Shariff . Ta kasance shahararriyar 'yar wasan Hausa ce. Mutane da dama na gani da daukan ta a matsayin jarumar 'yar wasan Kannywood kuma abar koyi musamman yadda take fitowa cikin sutura na al'ada da kyau, tana fitowa a wasannin barkwanci na ban dariya. Hadiza ta kasance ita ce jakadiyar da ta daga cikin kamfanin sadarwa na Najeriya MTN Nigeria da kuma kamfanin abincin Indomie, ta karbi kyautar Best Actress Jury Award a 2nd Kannywood Award wanda kamfanin MTN Najeriya suka dauki nauyin bayarwa. Ita ce wacce ta kafa gidauniyar HAG Foundation.

Hadiza ta yanke shawarar shiga Nollywood a shekara ta 2017, biyo bayan Ali Nuhu, Sani Musa Danja, Yakubu Muhammed, Maryam Booth da Rahama Sadau . An saka ta a fim dinta na farko na Nollywood kusa da Mike Ezuruonye, Mike Angel da Emmanuella a fim mai taken Lagos Real Fake Life .

Jakadanci

A watan Disambar shekara ta 2018 ne, kamfanin NASCON Allied Plc, wanda ke reshen rukunin kamfanonin Dangote , ya bayyana Hadiza Aliyu a matsayin jakadiyar jakadancin Dangote Classic Seasoning a yayin kaddamar da kayan hada kayan a Kano.

Taimako

A shekara ta 2016, Hadiza ta kafa ƙungiyar agaji mai suna HAG Foundation Da nufin inganta rayuwar talakawa ta hanyar samar da taimako a bangarorin ilimi da kiwon lafiya gami da wadatar abinci, Ta zama daya daga cikin ‘yan wasa mata na farko a tarihin Kannywood da ta gabatar da irin wannan taimakon jin kai.

A watan Maris na shekara ta 2016, ta ziyarci sansanonin ‘yan gudun hijirar da ke cikin jihar Kano inda ta ba da gudummawar kayayyakin abinci, kayan masaka da sauran kayan masarufi da mazauna sansanin suke bukata saboda rikicin arewacin Najeriya.

Lamban girma

Hadiza Aliyu ta samu kyaututtuka da girmamawa da dama wadanda suka hada da shekara ta 2013 Best of Nollywood Awards da 2nd Kannywood / MTN Awards a 2014. Saboda karramawar da ta yi a matsayin 'yar fim, Hadiza ta karrama a shekarar 2013 daga tsohon Gwamnan Jihar Kano, Dakta Rabi'u Musa Kwankwaso . An kuma ba ta lambar yabo ta Hollywood ta Afirka a matsayin Jarumar Jarumai mata .

Awad

Lamban girman da Hadiza Aliyu Gabon ta samu

Year Lamban girma Rukuni Fim Sakamako
2013 Kwankwasiyya Award Recognition Award Kwankwasiyya Award Lashewa
2013 2013 Best of Nollywood Awards Best Actress (Hausa) Babban Zaure Lashewa
2014 City People Entertainment Awards Best Actress (Hausa) Babban Zaure Ayyanawa
2014 2nd Kannywood/MTN Awards Best Actress of the Year(Jury Choice) Daga Ni Sai Ke Lashewa
2015 Kannywood AWA 24 Film & Merit Award Best Supporting Actress Ali Yaga Ali Lashewa
2016 African Hollywood Awards Best Actress African Films in Hausa Language Lashewa
2017 Arewa Night Award Recognition Award Lashewa
2017 2017 Best of Kannywood Award Best Actress (Hausa) Ayyanawa

Kyaututuka

Jadawalin kyaututtukan martabawa da Hadiza Aliyu Gabon ta samu

Year Girmamawa Rukuni Bangare
2016 Kano State Senior Secondary Schools Management Board Certificate of Appreciation Educational Support
2016 Statup Kano Certificate of Appreciation Empowerment Support
2016 Billycares Charity Foundation Recognition Award Philanthropy
2019 Hausa Students Association of Nigeria (BUK) Recognition Award Educational Support

Fina finai

Fina finan ta
Shekara Sunan Fim Matsayin Nau'i
Daina Kuka Jaruma Fim
Farar Saka Jaruma Fim
Fataken Dare Jaruma Fim
Kolo Jaruma Fim
Mukaddari Jaruma Fim
Sakayya Jaruma Fim
Umarnin Uwa Jaruma Fim
Ziyadat Jaruma Fim
2009 Artabu Jaruma Fim
2010 Wasila Jaruma Fim
2010 Umarnin Uwa Jaruma Fim
2012 Aisha Humaira Jaruma Fim
2012 'Yar Maye Jaruma Fim
2012 Badi Ba Rai Jaruma Fim
2012 Akirizzaman Jaruma Fim
2012 Dare Daya Jaruma Fim
2012 Wata Tafi Wata Jaruma Fim
2013 Da Kai Zan Gana Jaruma Fim
2013 Haske Jaruma Fim
2013 Ban Sani Ba Jaruma Fim
2014 Mai Dalilin Aure Jaruma Fim
2014 Daga Ni Sai Ke Jaruma Fim
2014 Ali Yaga Ali Jaruma Fim
2014 Basaja Jaruma Fim
2014 Uba Da 'Da Jaruma Fim
2014 Indon Kauye Jaruma Comedy/Fim
2014 Ba'asi Jaruma Fim
2014 Jarumta Jaruma Fim
2017 Gida da waje Jaruma Fim
2017 Ciki Da Raino Jaruma Comedy/Fim
2019 Hawwa Kulu Jaruma Fim
2019 Wakili Jaruma Fim
2019 Dan Birnin Jaruma Fim
2019 Gidan Badamasi Jaruma Comedy/Fim

Hotuna

Duba nan

Manazarta

Tags:

Hadiza Aliyu Farkon RayuwaHadiza Aliyu IlimiHadiza Aliyu ShaharaHadiza Aliyu JakadanciHadiza Aliyu TaimakoHadiza Aliyu Lamban girmaHadiza Aliyu HotunaHadiza Aliyu Duba nanHadiza Aliyu ManazartaHadiza AliyuGabonHausaNajeriya

🔥 Trending searches on Wiki Hausa / هَوُسَ:

Aliyu Muhammad GusauLilin BabaƘananan hukumomin NajeriyaZauren yan majalisar dokokin Jihar KanoBasma HassanTarihin HabashaJean Alassane MendyHamza al-MustaphaAyabaSofiyaFati WashaMikiyaAttahiru BafarawaSanusi Lamido SanusiRomawa na DaKalabaFadila MuhammadAnas BasbousiLibyaSadiya GyaleMarcia FalkFaggeNura M InuwaMansa MusaAsiyaAbdourahmane Ndiaye (mai wasan ƙwallon ƙafa)TasheMagaryaKoriya ta KuduKamala HarrisDuniyaJami'aAmina A ShehuGabashin TuraiFalalar Azumi Da HukuncinsaAladuIsra'ilaGhanaAbba Kabir YusufMaryam MalikaDelta (jiha)New HampshireBet9jaSallah TarawihiKaruwanci a NajeriyaSahabbai MataAmfanin Man HabbatussaudaKajal AggarwalAl'adun Najeriya na gargajiyaTibiYammacin AsiyaIbrahim ShekarauRashanciAliyu Sani Madakin GiniMr442Cold WarShugaban kasar GhanaDagmawit Girmay BerhaneLaberiyaTarihin Jamhuriyar NijarJinin HaidaAminu KanoTauraron dan adamBauchi (jiha)Aikin HajjiMusulunciSinYakolo IndimiShehu IdrisYahudawaMisraWilliams Uchemba🡆 More