Ranar sallah rana ce ta farin ciki ga musulmain duniya bakidaya wacce take gudana sau biyu a kowace shekara.
Sallah ta kasu kashi biyu, akwai babbar sallah da karamar sallah.
Ita karamar sallah ana hidimarta ne bayan kammala azumin watan Ramadan, Sannan kuma musulmi na yanka kaji domin murnanta bayan ziyarce-ziyarce ga junansu.
Babbar sallah ana hidimarta ne bayan kwananki saba'in daga kammala azumin watan Ramadan, wanda hakan yayi dai-dai kwana goma ga watan sha biyu (zul-hijja).
Ita karamar sallah ana yin ta ne bayan an gama azumin watan Ramadana, idan an ga wata a daren 29 ko 30, to, washe gari za a yi sallar azumi. Ita kuma babbar sallah ana yinta ne bayan azumi da wata biyu da kwana goma. Wato goma ga watan zul-hajji, washegarin Arafa. Ana yanka rago, tunkiya, akuya, taure, saniya, ko rakumi.
Ranar karama sallah wato sallar azumi. Da safe bayan an karya kowa zai yi wanka ya sanya sababbin kaya, a je masallaci domin gudanar da sallar idi. Su kuma iyaye mata za su yi girki na musamman da za a ci a gida da kuma rabawa 'yan' uwa da abokan arziki. Ranar sallah kowa yana samun abin da zai ci. Rana ce ta musamman ga al’ummar musulmai gabaki daya.
Ranar babbar sallah/sallar layya. Ranar sallah da safe kowa zai sa kayansa mai kyau, amma an fi son fararen kaya ga wanda Allah ya hore ma wa, amma kuma za ka iya sa kalar da kake so ba laifi ba ne, amma idan mutum yana da halin layya, ana so ya kame bakinsa har sai an sauko daga masallaci bayan babban limamin ya yanka ragonsa. Idan an sauko wato an dawo daga masallaci, sai duk wanda yake da abin yanka ya yanka dabbarsa. A kasar Hausa, ranar za a rataye ragon sai washe gari a yi aiki, shi kuma kayan ciki za su sarrafashi a soya kowa ya taba. Washegari za a sauko da dabbar da aka rataye a yayyanka a bai wa yara su rarraba wa makota da 'yan' uwa. Sauran naman za a dafa shi a soya a rarraba wa mutanen gida kowa ya dauki rabonsa. Shi kuma kai da kafafun dabbar za a babbake a ajiye sai bayan yan kwanaki a yi ragadadarsa a ci. Wasu kan ajiye shi sai lokacin takutaha wanda shi ma wata al-ada ce ta Hausawa.
This article uses material from the Wikipedia Hausa / هَوُسَ article Ranan Salla, which is released under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 3.0 license ("CC BY-SA 3.0"); additional terms may apply (view authors). An samar da dukkan muƙaloli a ƙarƙashin lasisin Creative Commons Attribution/Share-Alike; tana yiwuwa wasu ƙa'idoji su yi tasiri. Ku duba Ka'idojin Amfani na Gidauniyar Wiki domin ƙarin bayani. Images, videos and audio are available under their respective licenses.
®Wikipedia is a registered trademark of the Wiki Foundation, Inc. Wiki Hausa / هَوُسَ (DUHOCTRUNGQUOC.VN) is an independent company and has no affiliation with Wiki Foundation.