Hula Wata sutura ce da ake sawa a kai.
A al'adar Malam Bahaushe sa hula na daga cikin cikar kamalar ɗa namiji da suranta girma. Garuruwan da suka shahara a ɗinkin hula su ne kamar haka, Borno da Katsina da Paki. Hula suna ne na "tilo" jam'i kuma "Huluna". Kuma hula tana da mutukar muhimmanci a wajen mutane, musamman ma a Kasar Hausa, kuma tana nuna cikar kamala "cikar ado a wurin Malam Bahaushe sai da hula".
hula | |
---|---|
Bayanai | |
Ƙaramin ɓangare na | headgear (en) |
Fabrication method (en) | Dinkin hula |
Hula dai ta samo asali ne tun a ƙarnin baya, inda mutane musamman ma dattawa suka fi amfani da ita domin sanya ta a kai, hula tana kara nuna mahimmanci ga mutane a wasu ƙabilun inda wasu kuma ke sanya ta domin ado. Hula kala-kala ce kuma a Nijeriya kusan kowane yanki da yadda suke sa hula. Kuma maza su ne aka fi sani da sana'ar ɗinkin hula musamman ƴan Maiduguri.
This article uses material from the Wikipedia Hausa / هَوُسَ article Hula, which is released under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 3.0 license ("CC BY-SA 3.0"); additional terms may apply (view authors). An samar da dukkan muƙaloli a ƙarƙashin lasisin Creative Commons Attribution/Share-Alike; tana yiwuwa wasu ƙa'idoji su yi tasiri. Ku duba Ka'idojin Amfani na Gidauniyar Wiki domin ƙarin bayani. Images, videos and audio are available under their respective licenses.
®Wikipedia is a registered trademark of the Wiki Foundation, Inc. Wiki Hausa / هَوُسَ (DUHOCTRUNGQUOC.VN) is an independent company and has no affiliation with Wiki Foundation.