Harin Bam A Nyanya, Afrilu 2014: Harin ƴan ƙungiyar Boko Haram a Najeriya

A ranar 14 ga watan Afrilu, 2014 da misalin ƙarfe 6:45 na safe, wasu bama-bamai biyu sun tashi a wata tashar mota mai cunkoson jama’a, a garin Nyanya na Jihar Nasarawa, hakan ya jawo mutuwar mutane aƙalla 88 tare da jikkata wasu 200.

Tashar motar na da nisan kilomita 8 ne  daga kudu maso yammacin babban birnin tarayya.

Infotaula d'esdevenimentHarin bam a Nyanya, Afrilu 2014
Harin Bam A Nyanya, Afrilu 2014: Kai hari, Nauyi, Martani
 9°03′N 7°30′E / 9.05°N 7.5°E / 9.05; 7.5
Iri bomb attack (en) Fassara
Kisan Kiyashi
Bangare na Rikicin Boko Haram
Kwanan watan 14 ga Afirilu, 2014
Wuri New Nyanya
Ƙasa Najeriya
Adadin waɗanda suka rasu 75
Adadin waɗanda suka samu raunuka 124

Kungiyar Boko Haram ta ɗauki alhakin kai harin kwanaki shida bayan faruwar lamarin. Hakan ya faru ne sa'o'i kaɗan kafin a sace ƴan matan Chibok.

Kai hari

Harin Bam A Nyanya, Afrilu 2014: Kai hari, Nauyi, Martani 
Wani mutum yana hutawa a asibiti biyo bayan mutuwar mutane 71 yayin da aƙalla 124 har dashi suka jikkata, sakamakon harin a wata tashar mota da ke wajen birnin Abuja, 15 ga Afrilu, 2014.

Wasu bama-bamai da aka ɓoye a cikin motoci sun tashi da sanyin safiya a wata tashar mota da ke Nyanya a wajen Abuja. Bayan fashewar farko, an sake samun tashin bama-bamai yayin da tankunan mai a cikin motocin da ke kusa da su suka tarwatse.

Abbas Idris, shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa a Abuja, ya tabbatar da mutuwar mutane 71 tare da jikkata wasu 124. Tashar motar na yi wa talakawa da wasu ƙabilu ko mabiya wani addini, hidima. Kakakin Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kasa, Manzo Ezekiel, ya tabbatar da cewa da yawan waɗanda suka jikkata na samun kulawa a asibiti. Ya zuwa ranar 15 ga watan Afrilu, adadin waɗanda suka mutu ya karu zuwa 75, yayin da masu bincike ke ci gaba da zaƙulo tarkacen da aka samu a wurin da fashewar ta afku. Har wayau ya zuwa ranar 18 ga watan Afrilu, adadin waɗanda suka mutun ya ƙaru zuwa 88, yayin da fiye da 200 aka ruwaito sun jikkata.

Nauyi

Kungiyar Boko Haram ta ɗauki alhakin kai harin, kwanaki shida bayan faruwar lamarin—a cikin bidiyon da ya nuna su a lokacin da su ke ɗaukar alhakin kai harin, ya kunshi shugaban kungiyar Abubakar Shekau wanda aka saki a ranar 19 ga watan Afrilu. Hukumar ƴan sandan kasa da kasa ta Interpol ta kama Aminu Sadiq Ogwuche a kasar Sudan a watan Mayun 2014, bisa zargin kasancewar sa a cikin ɗaya daga cikin waɗanda su ka kai harin bam ɗin. Sa'o'i kadan biyo bayan harin, ƴan ƙungiyar Boko Haram sun yi garkuwa da ɗaruruwan ƴan matan makarantar Chibok.

Martani

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya ziyarci wurin da fashewar ta faru, inda ya ce:

Mun yi asarar adadi mai yawa. Muna jajantawa ƙasar mu, maza da mata. Batun Boko Haram wani mummunan tarihi ne a cikin wannan lokaci na ci gabanmu. Gwamnati na yin komai don ganin mun ciyar da ƙasarmu gaba. Amma waɗannan abubuwan da ba dole ba ne ke jawo mana koma baya. Amma za mu kawo karshen hakan.

Harin dai ya zo ne kwana guda bayan ɗan majalisar dattawan Najeriya Ahmed Zanna ya yi ikirarin cewa ƙungiyar ƴan ta'addan, ta hallak fararen hula 135 a arewa maso gabashin Najeriya a wasu jerin hare-hare uku da aka kai, a makon da ya gabata.

Duba kuma

  • Harin bam a Nyanya, Mayu 2014

Manazarta

7°30′00″E / 9.0500°N 7.5000°E / 9.0500; 7.5000

Tags:

Harin Bam A Nyanya, Afrilu 2014 Kai hariHarin Bam A Nyanya, Afrilu 2014 NauyiHarin Bam A Nyanya, Afrilu 2014 MartaniHarin Bam A Nyanya, Afrilu 2014 Duba kumaHarin Bam A Nyanya, Afrilu 2014 ManazartaHarin Bam A Nyanya, Afrilu 2014Babban Birnin Tarayya, NajeriyaNasarawa

🔥 Trending searches on Wiki Hausa / هَوُسَ:

Abdullah ɗan Mas'udZubar da cikiAisha TsamiyaJakiIbrahim MandawariAl Kur'aniMasarautar Sarkin Musulmi, SokotoIndiyaAminu AlaImam Malik Ibn AnasBOC MadakiFaransaKitsoAli Ben SalemBarau I JibrinHanafiyyaShehu KangiwaBotswanaIranMisraCynthia OgunsemiloreHausaTarihin Waliyi dan MarinaKungiyar AsiriTauhidiShuaibu KuluKalaman soyayyaTaimamaNimco AhmedISBNSahurSokoto (jiha)TumfafiyaAbubakar RimiRukiya BizimanaGenghis KhanJoko WidodoAbay SitiNijeriyaAminu Ibrahim DaurawaAzamcin tsaftar muhalliShinkafiCabo VerdeAminu DantataPotiskumKaduna (jiha)Yanar Gizo na DuniyaTunisiyaPakistanTarihin Ƙasar IndiyaJahar TarabaMalam Lawal KalarawiHausa BakwaiKhalid Al AmeriRahama SadauKebbiAmurka ta ArewaMamman ShataYaƙin BadarUmar Tall Ɗan (ƙwallon ƙafa)WikisourceDogo GiɗeDayo AmusaEritreaGmailAli RanaShams al-Ma'arifAbba Kabir YusufRabi'u DausheTarihin AmurkaSwitzerlandAmal UmarDutseShuwa ArabFalasdinawaGoogle🡆 More