Farida Jalal (An haife ta ranar 2 ga watan Nuwamba, shekara ta alif ɗari tara da tamanin da biyar1985) na Miladiyya.
A birnin Katsina. Ƴar wasan fim ce a masana'antar fina-finan Arewacin Najeriya da aka fi sani da Kannywood.
Farida Jalal | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | 2 Nuwamba, 1985 (38 shekaru) |
Sana'a | |
Sana'a | ɗan wasan kwaikwayo |
An haifi Farida Jallal ne a ranar 2 ga watan Nuwamba, 1985 a birnin Katsina, Jihar Katsina. Farida ta taso ne kuma ta yi karatu a jiharta ta Katsina inda daga baya ta koma jihar Kano ta fara sana’ar fim a masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood.
Farida ta shiga harkar fim ne a shekarar 2002 inda ta fito a manyan fina-finan masana’antu na lokacin kamar Yakana, Sansani da Madadi. An dakatar da Jaruma Farida Jallal daga yin fim na wasu lokuta saboda hana wasu jaruman fina-finai da gwamnatin jihar Kano ta yi. A Shekarar 2019, Farida har ta sake fitowa a Kannywood. A lokacin ta bayyana cewa ta dawo harkar fim har ma ta sanar da cewa nan ba da daɗewa ba za ta fitar da fina-finanta. A wata hira da ta yi da BBC Hausa, Farida ta bayyana cewa har yanzu ana cin moriyarta a masana'antar Kannywood. A cikin wata hira da jaruma Farida Jallal ta bayyana cewa a halin yanzu tana mai da hankali kan waƙoƙin Bisharar Musulunci.
Farida Jalal ta zayyano waɗansu finafinai da tayi. Sun haɗa da;
Da sauransu da dama a cewar ta.
Farida tayi aure ta haifi ƴaƴa biyu, amma ɗaya daga cikin ‘ya’yanta ya rasu. Farida bata da aure a halin yanzu.[ana buƙatar hujja]
This article uses material from the Wikipedia Hausa / هَوُسَ article Farida Jalal, which is released under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 3.0 license ("CC BY-SA 3.0"); additional terms may apply (view authors). An samar da dukkan muƙaloli a ƙarƙashin lasisin Creative Commons Attribution/Share-Alike; tana yiwuwa wasu ƙa'idoji su yi tasiri. Ku duba Ka'idojin Amfani na Gidauniyar Wiki domin ƙarin bayani. Images, videos and audio are available under their respective licenses.
®Wikipedia is a registered trademark of the Wiki Foundation, Inc. Wiki Hausa / هَوُسَ (DUHOCTRUNGQUOC.VN) is an independent company and has no affiliation with Wiki Foundation.