Ahmed Makarfi (An haife shi a ranar 8 ga watan Agusta,shekara ta alif dari tara da hamsin da shida 1956) a karamar hukumar Makarfi, jihar Kaduna.
Ya kasance dan siyasa a Nijeriya, kuma tsohon gwamnar jihar Kaduna, da ke Arewa maso tsakiyar Najeriya. Gwamnan jihar Kaduna ne daga shekara ta alif daritara da casa'in da tara ( 1999 ) zuwa shekara ta dubu biyu da bakwai ( 2007 ), bayan Umar Farouk Ahmed - kafin Namadi Sambo. Kuma ya kasance membane na jam'iyyar PDP.
Ahmed Makarfi | |||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|
14 Nuwamba, 2011 - 6 ga Yuni, 2015 - Samaila Suleiman →
5 ga Yuni, 2007 - 6 ga Yuni, 2011 District: Kaduna North
29 Mayu 1999 - 29 Mayu 2007 ← Umar Farouk Ahmed - Namadi Sambo → | |||||||
Rayuwa | |||||||
Haihuwa | Makarfi, 8 ga Augusta, 1956 (67 shekaru) | ||||||
ƙasa | Najeriya | ||||||
Ƙabila | Hausawa | ||||||
Harshen uwa | Hausa | ||||||
Karatu | |||||||
Makaranta | Jami'ar Ahmadu Bello | ||||||
Harsuna | Turanci Hausa Pidgin na Najeriya | ||||||
Sana'a | |||||||
Sana'a | ɗan siyasa | ||||||
Imani | |||||||
Addini | Musulunci | ||||||
Jam'iyar siyasa | Peoples Democratic Party |
An haifi Ahmad Makarfi a ranar 8 ga watan Agustan shekara ta alif, 1956,a karamar hukumar Makarfi dake jihar Kaduna.
Ahmad Makarfi kwararren dan siyasa ne a Najeriya. Kuma cikakken dan jam’iyar PDP ne a Jihar Kaduna.
Matarsa ita ce Hajiya Asma’u Makarfi ta fara karatunta na firamari a shekara ta alif, 1977,a makarantar Kaduna Capital School, Inda ta fara samo ilimi akan harkan zamantakewa da dabi’a ta kula da yara.
A cikin shekara ta (2017), an cire Makarfi a matsayin Shugaban PDP kuma an ayyana Ali Modu Sheriff a matsayin shugaban, amma bayan hukuncin mutum biyar na Kotun Apex, Makarfi ya dawo bakin aikinsa a matsayin Shugaban PDP na kasa.
A watan Yuni a shekara ta (2018), Makarfi ya bayyana cewa yana shiga cikin "gogaggun 'yan jam'iyya maza da mata" a fafatawar neman takarar shugaban kasa na babbar jam'iyyar adawa a zaben shekara ta (2019). Ya ce adalci ne kawai ya shiga takarar bayan tattaunawa mai zurfi tare da jam’iyyarsa maza da mata da sauran masu ruwa da tsaki. Makarfi yana daya daga cikin 'yan takara (12) da sukayi takarar neman PDP a babban taron da akayi a Fatakwal a ranar (6) ga watan Nuwamba a shekara ta (2018). Daga cikin 'yan takara( 12 )da suka nemi tsayawa takarar,' yan takara hudu ciki har da shi kansa Makarfi sun fito ne daga jihohin Arewa maso Yamma. Aminu Tambuwal (Jihar Sakoto), Rabiu Kwankwaso (Jihar Kano), Attahiru Bafarawa (Jihar Sakoto) su ne sauran ‘yan takarar da suka kafa yankin. Manazarta sun yi hasashen cewa dimbin 'yan takara daga yankin zasu raba kuri'un wakilai daga yankin tsakanin masu fafatawa dakebada dama ga fitattun' yan takara daga wasu yankuna akan su. A zaben fidda gwani na PDP, Makarfi ya samu matsayi na (5) mai nisa bayan Atiku Abubakar wanda ya lashe zaben. Sakamakon rashin nasara daga firamare ya kawo karshen takarar shugaban kasa a shekara ta (2019).
This article uses material from the Wikipedia Hausa / هَوُسَ article Ahmed Makarfi, which is released under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 3.0 license ("CC BY-SA 3.0"); additional terms may apply (view authors). An samar da dukkan muƙaloli a ƙarƙashin lasisin Creative Commons Attribution/Share-Alike; tana yiwuwa wasu ƙa'idoji su yi tasiri. Ku duba Ka'idojin Amfani na Gidauniyar Wiki domin ƙarin bayani. Images, videos and audio are available under their respective licenses.
®Wikipedia is a registered trademark of the Wiki Foundation, Inc. Wiki Hausa / هَوُسَ (DUHOCTRUNGQUOC.VN) is an independent company and has no affiliation with Wiki Foundation.